← Book details Gov Wife Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 38

Sashe 17

Gov Wife Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan har saboda mun raba ki da Ubaydullah ne kika yi watsi da aurenki to ki sani abinda kike ba abinda zai haifar miki sai ba
in ciki.

Ban ji da
i ba Asiya.

Shikenan ba zaki saki ranki ki rungumi aurenki a matsayin ibada ba"
"Abba shine bai
aukeni da daraja ba.

He's using me for his campaign"
"Sai me?"
"Abba!"
"Sai me idan yayi amfani dake wajen kamfen
insa, ba mijin ki bane?"
Asiya ta saka hannu ta fara goge hawayenta.

Ita kam akan Gwamna Abba kamar baya sonta.

Sauran nasihar Abba ma dai Asiya ba ji tayi ba, dan rabi kuka rabi sa
e-sa
e ta ke yi a zuciyarta.

A rana ta uku da dawowarta sai ga Mahirah da Junior sun zo gaisheta.

Lokacin da take Asibiti Hajia Umma da wasu 'yan tsiraru cikin 'yan uwan Gwamna sun zo sun gaisheta.

Sai yau ne Asiya ta zauna da Mahirah saboda duk zaman da tayi a gidan Gwamna Mahira tana Kachallah house.

Yarinyar kam ba laifi akwai hankali ba kamar Nana ba.

Maganarta sanyi, kominta a sanyaye.

Ta yi tunanin Bilkisu Kachallah ce ta turosu amma ga mamakinta sai Mahira tace mata Gwamna ne ya ce su zo su gaisheta.

Junior ya sake jiki da su Ali da Gwani suka tafi da shi yawo.

"Ya jikin Nana?" Asiya ta tambaya ganin shirun yayi yawa dan Mahira bata da yawar magana kamar 'yar uwarta.

"Da sau
"Har yanzu ba a dawo da ita gida ba?"
"Sun ce sai ta cika wata shida a wajen"
"Amma kuna zuwa dubata ko?"
"E muna zuwa duk weekend"
Asiya tana
arin updating wayarta saboda lokacin da aka bata wayar kafin a sakota sun share kusan komai na kan wayar.

"Anty Shahidah dan Allah ki kula da Daddy, wallahi bashida lafiya"
Asiya ta kalleta da mamaki.

Kanta a
asa ta cigaba da bayani "tunda aka
auke ki bashida lafiya.

Akwai ranan da ya zo gaishe da Dadda da zai tafi sai kawai gani muka yi ya fa
i.

Ya cewa Dadda kar ta fa
awa kowa, kuma har yanzu ya
i yaje a duba shi.

He was busy, Mommy ma kuma kamfen ne a gabanta yanzu"
"Miyasa kike gaya min wannan?"
"Because...because you are a good person"
Asiya ta kauda kanta kamar bata damu da abinda Mahira ta fa
a ba.

Sai yamma kafin suka tafi, lokacin da aka dawo da Junior yayi futu-futu da shi wai ball ya buga.

Da ke yaron kullum a takure yake, yanzu da ya zaga anguwa yai wasa da sa'anninsa da kuma wanda suka girmeshi sai ya langwa
e jikin Ali yace ba zai tafi ba.

Da
yar Asiya ta lallashe shi akan za a kawo shi gobe.

Bayan tafiyar su Mahira, Asiya ta shiga tattauna maganar da Mahira ta mata, da ma maganar Abba daya tsaya mata a rai tun jiya.

Ta kasa yarda cewa Gwamna ba shi da hannu a saceta da aka yi saboda alamu sun nuna shi munafukine.

Amma yanzu kuma maganar Mahirah ya sa ta fara tantama da abinda ta sawa ranta.

A wani gefe kuma kalaman Gwamna na ranan suna kashe mata jiki, suna tunku
e duk wani haushinsa da take ji.

'Ina son ki Asya' duk lokacin da ta tuno wa
annan kalamomi sai ta dinga ji tsikar jikinta na tashi.

Sannan
walwarta na
arin gano mata a wani siga za ta fayyace kalaman.

Shin Gwamna yana sonta a matsayin matarsa ne, ko kuma a matsayin wacce ya kamu da soyayyarta?...

Kwananta biyar a gida ta warware kamar ba ita ba.

Ranan ne kuma aka raba musu gadon Umma wanda Abba ko tsinke bai
auka ba, dan cewa yai ya yafe nashi kason.

Washegari Abba yace ta tattara ta koma gidanta.

Tun maganar da Abba ya mata take shakkarsa dan haka da yai maganar ko musu ba ta yi ba ta kira Yaya Bello tace ya zo ya
aukesu bayan sallar magariba.

Abin mamaki gidan Gwamna ta
auka za su wuce sai ta ga yayi hanyar gidan Gwamnati.

"Yaya Bello ka kaini gidansa bana son hayaniyar wanchan gidan"
"Mai girma ne yace nan gidan za a kawoki"
Tayi shiru ba dan ranta ya so ba, sai dan tana
arin bin nasihar Abba.

Shine da ikon sakata a duk inda ya ga dama, tunda sunan matarsa take amsawa.

"Mommy where is Hancha'u?" Junior yayi wa Bilkisu tambayar nan yafi a irga.

Yanzun ma Safiyya ce ke zuba masa abinci shiyasa ya tambaya saboda tunowa da yai da ita.

"Na gayama kar ka sake tambayar Hansa'u a gidan nan.

She's gone"
"Mommy why?"
"Ni kam ko yarinyar nan mayya ce, kullum minti
aya biyu sai ka tambayi Hansa'u.

Eat your food ko kuma na hanaka zuwa Kachallah house gobe"
"gidansu Ali zan je gobe"
"Waye kuma Ali?"
"Alin gidansu Asiya.

Oops Anty Asiya"
Dai dai lokacin Asiya ta shigo dinning room
in da sallama.

"Speaking of the devil" Bilkisu ta fa
a a ranta.
akin da Asiya ta zauna kwanan baya an rufe shi.

Ta tambayi wata mai aiki tace Bilkisu ce ta rufe.

"Ina bu
atar key
akina"
"Wani
aki fa?"
Asiya ta ha
e gira tace "
akin da ya dace da matar Gwamna"
Bilkisu Kachallah ta saka dariya, dariya sosai har da buga table.

Asiya da Junior suka zuba mata ido...

Gwamna yana zaune a falo yana karanta jarida lokaci zuwa lokaci yana
an kur
an tea.

Safiyar Lahdi ne kuma ya yi niyyar babu inda zai je da safe sai yamma idan ya fita duba 'yarsa Nana.

She's improving sosai, ba kamar farkon kaita ba, dan har kaman zarewa ta yi saboda
wayar data dena sha.

Kwanan Asiya
aya kenan da dawowa gidan kuma tun dawowanta bata ha
u da Gwamna ba, sai yanzu da ta zo falonsa.

"Barka da safiya"
Tun da ta bu
ofa yake binta da wutsiyar ido amma ba zaka gane hakan ba saboda gilashin da ke idonsa akwai
an duhu.

Idanunsa da kullum suke a kumbure saboda rashin isashshen barci da hutu ya saka shi sanya gilashi a koda yaushe.

"An tashi lafiya?"
"Lafiya"
Shiru ne ya biyo bayan hakan na wasu mintina da za su iya haura biyu.

"Ranan a Asibiti..." sai tayi shiru saboda nauyin maganan.

Har yanzu ta kasa yarda da maganar Sumayya amma kuma hoton data gani yana yawan yi mata shawagi a idanunta musamman idan ta rufe ido.

Wani lokaci tana duba hoton a wayarta saboda ta
ara fassara hoton da Sumayya ta
auka.

Ta saka Sumayya goge hoton a wayarta, amma kafin nan sai da ta tura hoton zuwa nata wayar ba tareda sanin Sumayya ba.

"Ina jin ki?"
"Ina so ka manta da abinda na fa
a cikin bacci, saboda shirmen bacci ne"
Gwamna ya ajiye jarida akan cinyarsa ya kalleta yace "ni kuma sai nake ganin kamar kin fa
i abinda ke ranki ne, dan abinda ka kwanta da shi da shi kake tashi"
"A'uzubillahi.

Ni wallahi ba abinda zai sa na yi irin wannan tunanin.

Balle na furta munanan kalmomi haka" ta rage muryarta
asa
asa tace "sai kace wata karuwa"
Gwamna bai gane inda ta dosa ba amma yace "shikenan in kince a rufe maganar za a rufeta.

Amma..."
"Allah shirmen bacci ne ba komai ba.

Ka manta da duk abinda na fa
a" ta fa
a da sauri
Sai daya kalleta kamar mai nazari sai yace "shikenan zan manta da komai"
"Ina so na je garinmu.

Mama bata da lafiya"
"Ki yi ha
uri zuwa wani lokaci sai kije amma ba yanzu ba"
Har ga Allah bata ji da
i ba, sai dai kuma yanzu ta yi al
awarin yi masa biyayya gwargwadon iyawarta tun lokacin da Abba ya mata fa
a...

Sati
aya Asiya ta lura Hansa'u bata gidan.

Da ta tambayi masu aiki sai aka ce mata tunda ta tafi
auye bata dawo ba.

Ta ja bakinta tayi shiru, dama saboda ta saba da ita a gidan ne yasa ta tambaya da bata ganta ba.

Asiya bata ta
a ganin Alhaji Abdullahi ba sai a lokacin bikinsu da Gwamna.

Kafin nan kam tana jin sunansa amma ba za ta iya tuna takamaimai kamanninsa ba.

Sai ga hotonsa a wayar Sumayya daga shi sai towel daya
aura a
ugu.

Ga tunbinsa ya fito kaman mai cikin wata takwas.

Abin haushi harda ri
ugu kamar wata mace.

Kanta ya
au zafi saboda hoton da kuma inda ta samu hoton yana nuni da cewa shi ya turo hoton ta whatsapp.

A ina Sumayya ta san Alhaji Abdullahi?

Garin sauri saboda makara yasa Sumayya ta manta wayarta a gida.

Asiya hotunanta na biki da akayi a gidansu take son turawa taci karo da wannan hoton.

Ta san password
in Sumayya dan haka kai tsaye ta bu
e whatsapp
inta ta fara neman tushen wannan hoto.

Sunan da aka yi saving da My Abdul ta shiga, kuma a nan ta tarar da hoton da aka tura, a
asan an rubuta "yanzu na fito daga wanka"
an saman chat
in ka
an ta ga hoton da Sumayya ta tura masa wanda yake dishi-dishi saboda an riga an goge hoton akan wayar.

Hoton
irjinta ne zuwa cikinta wanda babu riga babu komai.

Hannu na rawa ta fara bibiyar chats
in wanda ya tsaya kusan sati biyu baya.

Da alama an goge sauran ne saboda daga inda maganar ta fara ya nuna anyi wani a baya gogewa akayi.

Idan bata manta ba Alhaji Abdullahi cousin
in Gwamna ne kuma abokinsa.

Ba ta da masaniya akan iyalinsa amma ta san yanada mata da 'ya'ya.

Nawa Sumayya take?

Ko shatakwas idan ta cika to kwanan nan ne.

Ta ina ma suka ha
u?

Ta sake tambayar kanta.

Haka ta ri
e wayar tana sintiri a
aki, zuciyarta na ayyano mata abubuwa dayawa.

Kafin ta taho ranan kaman ta ji warin sigari tattare da Habibu amma bata sa hankali ba saboda ba a nitse take ba.

Wace irin 'yaruwa ce ita da tayi watsi da lamarin
annenta haka?

Kullum tana cikin jin haushin Gwamna ta ina zata lura da abubuwan da suke wakana a kusa da ita.

Lokacin da Sumayya ta dawo,
akin Asiya ta fara shiga saboda ta gaisheta kamar yadda ta saba.
Chapter 17 · 0% Book details