Sashe 94
Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wani abune dai, I will talk to her bari nasa yan aiki su daura abinci awuta, amman ai banma taba ganin fushin Zara ba, ballema masifarta" gyadamata kai Granny tayi takasa tsaye takasa zaune har ranta tanaji something is going on, fitowa Mum tayi ganin Granny, na wajen har lokacin tsaye yasa tace "Granny kina tsaye har yanzu, karki damu muje kiga" binta kawai Granny tayi tawuce suka fitadaga side din sukabar Amna ita kadai zaune afalon tana kallon cartoon. Bude kofa sukayi suka shiga flat din Granny, Zara suka gani zaune kan kujera sai uban zufa tayike ranta amugun bace fuskanta Yaya sosai duk uban AC dakin, ba Granny kadaiba har Mum saida gabansu yafadi, da sauri Granny takarasa kusada ita tace "Zara wai kodai zazzabin ne tun ciwon kan dakikayi jiya wanan zufa dakike yi na lafiya ne iyye jibeki"? Cikin fushi tace "zufan danakeyi ba matsalanki bace" zaro ido Granny tayi tana kallonta, cikeda masifa da ihu tace "kungayamai bani aurenshi kun raba auren dakuka hada"? Wanan karan kasa magana Granny tayi sai salati data fara, Mum ce tace "Zara are you okay kuwa? Tayaya za'a raba aurenki da Tobi dakike s......" wani ihu tayi tace "karki kara hadani da mutumin nan, karki kara kiramin sunanshi akunne na nagaya miki, karki kara, na tsaneshi na tsaneshi nace na tsaneshi" tai maganan tana tashi daga kan kujeran tana ihu sosai tai wajen TV dake kan stand batai wata wataba taja TV sai kasa tana ihu ta tsaneshi, da sauri Mum tadaga Granny tana salati suna kallon yanda Zara ke hauka, dinning tayi tana ihu ta tsaneshi duka kuloli da plate dake kan wajen ta shiga watsosu kasa suna tsalle suna breaking jikake rukuku karan fashewan glass hakan yasa da sauri Mum tabude kofa taja Granny suka fice daidai ana bude gate din gidansu manya manyan motoci suka shigo irin Family car, Dr Imam ke tukin sai babanshi adayan bangaren gaban, Mamanshi da kannenshi na baya, saikuma motar Dady. Fashewa da kuka sosai Granny tayi dayasa duk sukai parking motoci suka fitoda sauri sukai inda suke, Imam kuma yafito karshe yana sanye da shadda, Abba ne yafara cewa "Lafiya Mama" cikeda tashin hankali ta kalli Imam dake karasowa tace "Imam dubamin Zara, wlh jiya da yamma tai complain ciwon kai sosai, nabata paracetamol guda biyu tasha taje ta kwanta gab da magrib tai bacci, shinefa tun safe naga Zara ta tashi ba itaba, sai rashin kunya take tana sai mun raba aurenta da mutumin nan, shine yanzu kuma tanata fashe fashe adakina kaman ta haukace, Muhammadu bikifa saura kwana takwas nan da kwana hudu yan uwan mijinta zasu diro Abuja mun shiga uku" da sauri Abba yasaketa, sanan ya kalli Imam da kaninshi yace "let's go" bude kofan flat din Granny sukayi suka shiga, gabaki dayan kasan dakin glass ne, tagama da dinning tass akitchen suka jita tana fashe fashe tana watsarda abu, duk basu cire takalmi ba sukai kitchen din, Imam yafara shiga kitchen din ta haukata kitchen din tana ihu, zufanma datakeyi shine zaimafi baka tsoro sabida yanda internally take burning da hatred da kunci, kanta babu dan kwali akanta gashin kanta ya barbaje na hauka, tayi wani irin mugun haske tai kyau sosai kirjinta sun kara cika sosai, duk tsayawa sukayi awajen kofa suna kallonta, juyowa tayi ta kallesu tana kokarin daukan pots ta kalli Baban Imam tace "kaine ai katambayeni ko inasonshi ka daura auren ko wlh kuje kuraba shi na tsaneshi nace, na tsaneshi, kuraba auren nan wkh kona wulakanta ku" tawani watso musu pots din da sauri su Abba suka fice Imam yajuya baya pots din suka sameshi, sanan yajuyo yataho kanta, ihu tacigaba dayi tana jefamai duk abinda tasamu harya karaso gabanta ihu take ta tsaneshi, daukanta chak yayi tana ihu tana kokarin kwatan kanta, yakalli Babanshi yace "Dad check my medical bag a car, and get alluran bacci" sanan yawuce dakinta da ita, shikuma Babanshi yayi waje da sauri zuwa car. Shigar da ita dakin yayi tana dambe dashi sosai yana mamakinta, hannayenta yakama yabude tafukan hannunta dasukai zufa sosai ya kalla, sanan yakama fuskanta tana dukanshi sosai, yabude su yakalla daidai anbude kofan, yana rikeda ita yafadama babanshi iya yawan dazai zuko sanan yakarba yace "surikemai ita" riketa sukayi yaje tabayanta yadan dage riganta batareda yabari sun ganiba yamata alluran. Ko minti daya baiyi dayiba sai bacci, sakinta duk sukayi suka tashi akanta, Abba yace "subhanallahi meke damunta haka Imam"? Ahankali yana kallonta yace "I don't know Abba" Dad yace "Mum tace kodai aljanu ne" girgiza kai Imam yayi yana kallonta yace "ba aljanu bane wlh, look at her ita kanta wahala take, bakuga yanda take zufa ba am coming" fita yayi saigashi yashigo da wani dan roba da syringe, jininta yadeba sanan yatashi yace "bari naje lab and run some test a jininta, Dad ku zauna agidan please karku fita, men need to be around karta jima kanta kowasu ciwo, I will be back once nasan meke damunta" "Allah maka Albarka" Abba yafadi ahankali, shikuma yawuce yafita, su Granny na tambayanshi bai amsasuba yawuce abinshi. Hospital wani abokinshi yaje, dakanshi ya shiga testing jininta, gwajin farko yaga tanada cikin sati hudu dayan kwanaki, jimmm yayi saikuma ahankali yacigaba da abubuwan dayakeyi, yayi test sama da 15 duka negative tundaga kan maleria, typhoid, HIV, hepatitis duka negative, hakan yasa wajajen 5 yafito, ya tsaya a pharmacy yasaimata magungunan dayakamata mai ciki tasha, yana mamaki to cikine yasa take fushi haka take hauka dan babu abinda ciki baya sawa, saida ya tsaya yay salla sanan yawuce yatafi, daidai wata mad ride na shiga gidansu, shikuma yana shigowa anguwan yakarasa gate yashiga shima, lokacin daidai bodyguard din Tobi yafito yabudemai kofa, dan tunda yaji muryan Granny da tambayan datamai hankalinshi yaki kwanciya kawai yabi jirgi yazo, yana sanye dawani soft yard paper lace mai bala'in kyau milk yasha guga ga karin guga akayan, kanshi na sanye na hulan yarbawa dayama kwana yay wani kyau, idanunshi sanye da bakaken glasses, kafanshi sanye da palm na Hermes, yay kyau looking damn fresh kana ganinshi kaga ajebota yaro dan gata, black skin nashi nakara shinning kaman daga spa yake. _NAFJAN COLLECTION_ _Nafjan Collection business ne na shahararriyan CEO dinan wato Nafisa, wacce ta kware akan sana'oi kala kala._ _Tana saida kowani kalan kaya dakuka sani, Riga, wando, lace, shadda, atampa, takalma, na maza, na mata, na yara, na manya, sneakers, cambas, sandals, flat shoe duka, handbags, bagpack, akwatuna, dogayen riguna, agoguna, tana shigo da hadaddun kayan daki daga kasan waje, kayanta arahansu zaisa kama rufe baki, dan tuntubarta ko magana da ita directly zaku iya saminta awanan number wayan 08160472711, kowani kalan abu kuke nema kawai ku danna mata kira dan tambayanta kuji kotana dashi kobatada shi_ _Dankuma magana da ita directly a watsapp zaku iya samunta ta hanyar danna wanan link din. https://wa.me/+2348160472711 _danyin Yosarin kaya awajenta da sallan nan, just chat her up_ https://wa.me/+2348160472711 Parking shima Imam yayi yafito rikeda ledan magungunan, da papers na test results dinta, ganin Mota dama yasa Tobi ya tsaya dan yadauka Dad ne yagaisa saisu shiga ciki tare dan babu wanda yasan da zuwanshi ganin Dr Imam yasa ahankali yacire glasses din idanunshi yana kokarin tuno inda yataba ganin this face hakan yasa yakasa motsi, karasowa Imam yayi ahankali yamikamai hannu yace "OluwaTobi" hannu Tobi yamikamai bakinshi na motsi trying to mention Imam name daya shigemai hakan yasa Imam yaydan murmushi yace "Dr Imam, you helped me with my bag back then at Lagos" "OMG!" Tobi yafadi surprisingly, saikuma with a very clean heart kawai ya rungumeshi yanda yaran yan gayu keyi yace "Hi Dr Imam, longest time, how have u been" karan buga abu dasukaji yasa dukansu suka juyo, Zarane take kokarin fasa window tafito sabida hango Tobi datayi, dasauri Tobi yakalleta saima yamanta da Imam yay wajen da sauri yace "Jewel"! Daidainan su Dad suka kamota tana ihu sosai hakan yasa yay hanyar shiga flat din Granny, Imam biyedashi, suna budewa su Rahma yagani da masu gadin gidan na tattare glasses da TV daya fashe yayi akasa, hakan yasa ya tsaya turus, Imam yawuce shi yay corridor, inda Granny ke tsaye tana kuka sosai, Mum na Ammi na lallashinta, dan haukan da Zara keyi yawuce tunani, Imam yawucesu yabude dakin datake ciki yashiga, ahankali yakarasa batare daya shiga corridor ba ya tsaya turus yana kallon Granny dake kuka sosai da kowana wajen, bude kofan da Imam yayi yasa yay ido hudu da Zara dake kallonshi da kwayan idanunta dayaga sun chanza mai tana ihu tana I will kill you Tobi! Yakasa motsi yakasa magana, yama kasa tunanin komi, ganin haka yasa Mum tabar Granny da Ammi tazo wajen Tobi tace "saukan yaushe inlaw" kasa bata amsa yayi, ahankali yace "whats wrong with My wife Mum"? Kafinma Mum tai magana sukaji anbude kofan Zara ne tafito da gudu tai kitchen Allah yasa anshare glasses din wajen da wlh taji ciwo akafa, wuka ta dauko tadawo tafito, tayo kan Tobi dayajuyo yazuba mata idanu, dasauri Mum dakowa sukai ihu zasu tareta Tobi yadaga musu hannu alamun sun barta, har gabanshi tazo tadaga wukan daidai tadaura a chest dinshi Imam yawani irin fizge, juyawa tayi ta kalli Imam saikuma tajuyo ta kalli Tobi ahauce, tace "I hate you Tobi! I hate anything that has to do with you, I am not going to marry you, I swear by Allah I will not leave or stay with you, bazan aureka ba, kuma wlh idan basu raba auren mu ba saina illata kowa nagidan nan, I hate you with passion OluwaTobi" cikin wata irin kalan murya datai rauni sosai yana kallon kwayan idanunta sa hatred din yake gani aciki yace "Jewel stop saying this words to me, it hurts, I love yo..........." bai karasa maganan ba tadaga hannu ta tsinkamai wani irin mahaukacin mari, jikake pau!!!!! Yakauda kanshi gefe, dakin akai tsit kowa mamaki ya cinyeshi, zabura Granny tayi tatashi tazo zatai magana yarike mata hannu yace "please Granny! This is an issue between me and my wife, don't interfere" sanan yajuyo ahankali ya kalli Zara dake zufa tako'ina tana kallonshi tana huci kaman macijiya, cikin muryan so da asalin tausasawa da sanyin murya dakuma lallabawa kaman bashita mara ba