← Book details Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 97

Sashe 26

Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

shima turaren tsoron fesawa tayi balle ta zabanmai hakan yasa kawai ta debi biyar randomly ta ijiye mai da deodorant dakuma body spray din sanan tadau dadduma tafita ahankali tamaida kofan tarufe sanan tabude kofa tafita daga dakin tasauka kasa da gudu dan duka duka bakwai saura minti uku, kitchen dinshi tayi bata tsaya kallon komi ba sabida kar time yakure mata tadau goran ta dauraye sanan tafito taje gaban water dispensa tacika mai goran da ruwa tafito ta ijiye a sama sanan takoma sama da gudu ahankali tabude kofan ta maida tarufe daidai bakwai na safe na clicking daidai kuma yana bude ido, karasowa gaban gadon tayi tai kneeling kanta akasa gabanta nawani irin mugun faduwa tana jira yatashi. Tashi yayi ahankali zaune yana mika, sanan gently ya sauko da kafafunshi kasa batare daya fito da kanshi daga cikin labulen gadon ba, girgiza kafanshi for the first time bata luraba dan kanta nakasa akaro nabiyune ta lura dan alamun motsi tagani da sauri ta daga idanunta sama ta kallai gani tayi idanunshi lumshe kuma bai yaye labulen ba yana ciki, sake girgixa mata kafan dayayi yasa dawani irin sauri ta dauki bathroom dake wajen tasaka mai a kafafuwanshi dabasuyi kama da wanda aka taba takasu akasa ba sanan takoma inda take kanta nakasa, tashi tsaye yayi ahankali tareda bude idanunshi sanan ahankali yajuya yana tafiyan nan daidai cikeda gajiya kaman zai fadi yabude kofan bathroom ya shiga. Tashi tayi itama tuna abinda yafadi mata ta tattare labulen gadon ta sakalesu inda ake sakawa, ta gyara gadon tsaf tareda shimfida hadaddun lallausan bargunan dake kan gadon da bata taba ganin irinsu, ta gyara decorations dasuke gefen side drawer tass, sanan tafita tadauko vacuum daga inda taga masu aikin jiya sun ajiye sun koya mata yanda ake amfani dashi tun jiyan ta jona ta share dakin da dama babu datti ko daya tass akasan sanan tafitar ta dawo ta sake kneeling a inta take, bude kofa yayi yafito dudda bata juyoba but saida kamshin sabulun wankan shi yacika mata hanci dakenan kaman turare yana kamshi combination na dry wood da citrus, jin yakara bude dakin closet yashiga yasa ta tashi tabude kofar bayin, chak ta tsaya ganin yanda yay messing bayin up kaman yaro karami, bathrobe da boxer daya cirene tagansu akasa, ga brush din dayay amfani dashi a inda tabarshi mirror wajen ya batashi da kumfan makilin kaman akanshi yake fesa kumfan, hadaddun rags dake shimfida akasan bayin ya jikasu da ruwa, toilet rolls najan kasa, ajiyan zuciya ta sauke ahankali tace "yarone wai wlh ko Sadiq dinmu bazaiyi wanan aikin ba" wani karamin basket da ak nuna mata jiya na kwashe kayanshi daya cire ta dauka ta tattare su ciki dan annuna mata mai wankin kayanshi da zata dinga bama kayan sanan ta shiga tattare bayin ta share madubin fess, tai mopping ta tsane bayin cikin 10min ta gyara bayin harda wankewa tasake yi sanan tafito dan ita inhar aikine baya mata wuya, dudda bata kalleshi ba but taga yana kan dadduma yana salla hakan yasa ta shiga closet dinshi tana rike da basket din kayan dattin shi, gani tayi ashe baiyi komi abayi ba, towels din duka daya cire ya wurgasu akasa, haka mayyukan daya shafa batare daya rufeba su ba ya jejjefar da marafen su akasa har zuba suke sabida bai kulle ba ya wurgan, turarukan kuwa wasu bama taga marafan su ba nan tashiga nemeneme takai kusan 20min tana aikin closet din sanan tai putting nashi back in shape tafito, ganinshi tayi zaune bakin kan gado yana saka sneakers na gudu data daukomai, daukekai tayi bata kalleshi ba tabude kofa tafita waje taje Guard din dake gaban dakinshi na ganinta da basket din kayanshi kafin ma tamusu magana suka amsa takoma ciki, daidai shima ya sauko kasa yana kokarin sake headphone dinshi a kunne yay wani irin kyau fuskanshi yadan kumburan bacci lips dinshi sunyi mugun pink, sai kamshi yake zubawa, batare daya kalleta ba yace "follow me with the bottle water" da sauri tai dinning ta dauki goran tabiyo shi dashi, yana jogging tana biyedashi abaya. _DISASTROUS LOVE_ _MASIFAFFIYAR KAUNA_
Chapter 26 · 0% Book details