← Book details Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 97

Sashe 49

Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

ya budun mana ina gab da samin aiki mai tsoka ma, karki sake ki sake kirana da Baba, karkuma ki kara kiran number na, insunga dama su kasheki idan sun gano ke mace ce wlh ko ajikina zan fada musu nima a namiji na sanki kuma dama ke ba abinda na haifa bane kawai yarone dana taimaka, karki sake kirana mai farar kafa kawai annoba, jechan dajin Maiduguri ki nemo ubanki baniba" yana maganan ya katse wayan, dudda bayajin hausa amman zai iya cewa kusan kowani kalma ya fassara ma kanshi ita yakuma san tsaf abinda Baba yace, ahankali yaga ta kakalo murmushi tamikamai wayan nan nashi sanan tasake murmushi ta tashi ahankali tabi ta gefenshi ahankali tace "I want to drink water" sanan tabude kofa tai bene tanabin benen da sauri bata damuda ciwon datakeji ba dan maganganun Baba ayanzu yafi komi ciwo da azaba agareta, idanunta har rufewa suke da duhu mutuwa kawai takeso tayi ayanzu, bude kofan kitchen din falon tayi ta shiga ta shiga neme neme tana kabar dakome tagani kasa tana neman wuka, tashiga bude drawers din kitchen din, nan tai idanu biyu da wuka, mika hannu tayi tadauki wukar daidai Tobi yawani irin bugo kofa ya shigo kitchen din daidai itama tadaga wukan sama zata chakama kanta ta rufe idanunta, wani irin jump Tobi yadaka yawani tadiye kafarta dan yace zaije dagudu kafin yakai wukan ya isa cikinta, hakan dayayi yasa tai kasa wukan yafadi daga hannunta, dawani irin sauri ta tashi zata sake daukan wukan yay Ball da wukan da kafarshi tareda kamota dakarfi tashiga fada dashi tace "leave me alone i want to die, leave me alone, My Father said he is not my father, he said ama kasheni is not his business lemme die first before then" duk yanda take kokawa dashi saida yasata a kirjinshi ya rungumeta tareda matseta sosai yana bubbuga bayanta yace "cry cry, just cry let it out" wani irin rushewa da kuka tayi ta kankameshi kaman zata karyashi, bata tabajin bakin ciki da kunci irin nayauba, duk kukan datake kwanakin baya na azabane da tashin hankali da tsoro, but wanan kukan nayau kukan bakin ciki, kunci, tausayi da sorrow ne, cikin kuka tace "I don't have anybody, I don't have anyone, what's the point of leaving? I want to die" tafashe d_a kuka tana neman kwace kanta amman ina yahanata karfin namiji dana mace ba dayaba, shima idanunshi sunyi jajir bana wasaba. _DISASTROUS LOVE_ _MASIFAFFIYAR KAUNA_
Chapter 49 · 0% Book details