← Book details Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 97

Sashe 40

Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

M SHAKUR _Erotic Ideas group na matan aure zalla ne, group ne damuke program guda HUDU aduk sati, ranakun sune ALHAMIS, JUMMA'A ASABAR da LAHADI._ _Duk ranan Alhamis munayin program mai suna MARRIAGE LIFESTYLE, wato ZAMANTAKEWAN AURE, inda nakema mata lectures kan yanda ake zama da miji dakuma dabarun zama da miji, ranan jumma'a kuma muna program din damuke kirada TALK & HEAL wato yi magana ka warke, inda matan aure zasu gayamana matsalolin dasuke fuskanta agidajen mazajen su, zasu iya turamin ta pc idan basuson asansu nisainai forwarding group mu taimaka musu da shawarwari dakuma dabarun dazasubi su magance wanan matsalolin, sai ranan asabar shine ranan LECTURES, inda zan dauki darasi dake dauke da dombin ilimi abu wanda ya dace mata su iya dangane da aurensu, mu koya musu ayi magana akai sosai, sai ranan Lahadi zamuyi lectures akan ilimin daya danganci yanda zaki gamsar da mijinki sanan ki gamsar da kanki, kisaka mijinki ihu agado yana kururuwa yana sambatu, mukoyar dake yanda zakiyi spicing up sexlife dinki, and yanda zaki dinga rayuwa da mijinki kullum kaman sababbin aure._ _Idan kinason shiga wanan group din zaki turo 2000 to 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din, wata daya ne group din, idan kinason ki cigaba da zama duk wata dubu dayane 1500 ne subscription, sababbin zuwa kuma new member zakiyi register is 2k ne, don karin bayani zaki iya tuntubata a number ta 07012181461_ M Shakur EPISODE 3 FREE PAGE Shiga flat dinshi Maman shi tayi tana tafiya ahankali ganin baya kasa yasa tai sama, ahankali tabude kofar dakin bedroom dinshi tana Tobi Tobi, but shiru baya ciki bayi tabude baya ciki tabude closet dinshima bayanan hakan yasa ta sauko kasa bayan ta duba sauran dakunan, ta shiga kitchen dinshi tabude kofar wajen daya sadata dawani hadadden garden mai kyan gaske, hangoshi tayi zaune kan wani stool mai kyau ga wani katon whiteboard agabanshi, kunnenshi sanye da head phone hannunshi rikeda paint brush yana zanen wani hadadden lion kato, tsayawa Maman shi tayi abayanshi takai hannayenta tana wasa da kitson kanshi tace "wowww, this looks son, My artist" dan dagokanshi yayi yajuyo ganin Mamanshi ce yasa ya zare headphone din daga kunnenshi yajuyo yacigaba da zanenshi sanan yace "Mum" kujeran dake wajen ta dauko ta ijiye kusadashi ta zauna tareda dafa kafadarshi ahankali tace "OluwaTobi kayakuri kaji, I am still begging you nasan bamu kyauta maka ba but look at this from our perspective okay, we are doing everything to protect you My Love" taidan jim ganin ko kallonta bayayi aikinshi yakeyi abinshi yasa tace "guess what I come to tell you that an kada securities dinan sun tafi, my son is now free, u can go duk inda zaka kaji OluwaTobi" tunda tafara maganan ya tsaida zanen dayakeyi saida tagama tass sanan yajuyo ya kalleta irin juyowan nan na neman assurance, gyadamai kai tayi hakan yasa yadan saki murmushi, rungumoshi jikinta tayi sosai tace "I love you Son sosai, I will do anything in my power to give you wat you want kaji" gyadamata kai yayi ahankali tareda sakin murmushi kadan, tace "nakira Ayoka tazo kufita tare" batarai yayi yace "no" shiru tayi kaman tana kokarin tuno wani abu saikuma ahankali tace "Tobi kaga irin maganganun dana fadama yarinyar nan kuwa ranan kafin tahakura, I told her to calm down tagama service tukunna kafinma tafara maganan wani soyayya dakai" tabe baki yayi yace "Mum I am not interested in Ayoka period, I took her as a sister, and now data kaucema layi I don't even want her close to me ban iya yaudara ba, ban iya raising hope na mace up ba" ajiyan zuciya Mum ta sauke sai kawai ta tashi dukowa tayi ta manna mai kiss a kumatu tace "I love you son" ahankali yace "love you too Mum" wucewa tayi tafita shikuma ahankali yasaki murmushi sai kawai ya cillar da brush din yatashi dagakan kujeran yawuce sama wanka yayi yashiga closet dinshi ya shirya tsaf yana mamakin ya akayi boy baizo aiki ba yau, ko ansashi wani abune, jeans da riga yasaka na gucci masu color brown and white, yadauki p-cap yasa white yasa, slippers din maza ya saka na Prada white shima ya daura agogon hublot a hannunshi sanan yabude wani drawer a closet dinshi dake dauke da keys din motoci kusan 12, key wata hot range rover yadauka da wallet dinshi yafito yana baza uban kamshi, Taye da fitowanta kenan tana sanye da jeans da riga masu kyau tai murmushi tace "we are officially free" hararanta yayi, da sauri tace "Tobi please go with me am bored" hararanta yasake yi, cikeda lallashi tace "please nowwww munfa shirya fa, am sorry for everything kaji little brother" motarshi da kullum sai awanke yayi fara kal, yabude batare daya kalli su guards din dake kokarin budemai ba yatada motar kana ganinshi kaga dan mai kudi asalin definition of yoruba demon ajebota, jan motan yayi da hannu daya dayan hannu kuma yana saka dark shade yaja motan yafice batare daya kalli su Dad dake gaban fada atsaitsaye ba babanshi yabishi da kallo yana addu'a. Wani babban saloon yaje akamai gyaran fuska aka gyaramai gashin kanshi aka mai wani sabon style bobmarley dayama bakar fuskanshi masifar kyau, sanan yafito yatafi wani beauty spa skin 101 all this are abubuwa da he can order azo amai agida but shi yafiso yaje komi yayi da kanshi. Facials akamai hadaden gaske, face treatment, akamai lip therapy, lips dinshi suka kara so pinkish dakuma taushi, sanan akamai pedicure da manicure kumbanshi sukai kyau sukai haske, saiyay topping komi with a deep tissue massage dakuma sound deep sleep na two hours!!! That's how the rich roll fa, Allah kamana arziki. Saida ya farka sanan ya shiga bathroom yay hot bath yanajin dadin jikinshi sosai sanan yasaka kayanshi yafito yatafi sai godiya sukemai, awani masallaci ya tsaya yay alwala yay sallan azahar da la'asar wuraren biyar na yamma saikuma ya shiga mota wani boutique yagani dayaga an rubuta the Teens hakanan yaji Boy yafadomai arai hakan yasa ya gangara yay parking ya shiga, hadaddun kuya masu kyau yasiyama yaron dahar cikin ranshi yakeso, yaron nada hankali even at his young age, and he always takes care of him, yasaimai takalma da sneakers masu tsada yafito aka samai komi a mota sanan yatafi stadium zaije kallon kwallo, saida ya tsaya a hanya awani masallaci yay alwala ya shiga jam'i sukai sallan magrib sanan yafito ya shiga motarshi yahau kan titi, yana tafiya ya hango wani mutum yana sanye da suit da wasu textbooks manya guda biyu a hannunshi, saikuma jaka abayanshi daya rataya yana kokarin tsallaka titi, from no where saiga wasu thugs guda uku lagos boys sunzo sun bangajeshi sun fizge jakan harda textbooks dinma yafadi akasa dan kokadan bai ankara dasu ba, da sauri Tobi ya gangara yay parking a gefe sanan yasauko daga motar yataho da sauri yadagashi ahankali yace "sorry" ahankali yatashi yana gyaran white glasses din idanunshi ya kalli Tobi yasaki murmushi yace "thank you" tareda waigawa yana kallon hanya ganin ko alamunsu baigani ba, ahankali Tobi yace "do you need your things back"? Da sauri ya kalli Tobi yace "yes please all my whole career is in that bag pack, I came to lagos for now exam dazanyi for one week gobe zamu fara niba dan nan bane" yamai magana shima da turenci, Tobi ya kalleshi daga sama har kasa he looks damn neat amman kallo daya yamai yasan badan garin nan bane yace "can you fight" da sauri guy din yace "fight"? Dan ware manyan idanunshi Tobi yayi yace "don't you want your things back"? Da sauri yace "oh I want" ahankali Tobi kaman wanda baison yin magana yace "then gather your strength and techniques dinka na kaucema harin wuka, let's go" Tobi yay hanyar motarshi bin Tobi yayi da kallo danjim yayi baisan mesaba saikuma yaji he trust d guy hakan yasa yabishi ya shiga gaban da Tobi yabude mai ya zauna tareda rufo kofan Tobi kuma ya kunna motan yana murmushi, da sauri mutumin dake kallonshi yace "kasan inda sukene"? Kallo daya Tobi yamai ya dauke kai yace "I was born in lagos anan nan girma, I told you kawai shirya, zamuyi mini wrestling yanzun nan" yaja motar dawani irin gudu dayasa da sauri mutumin yaja seat belt ya daura. Wani anguwa yaga sun shiga da local street ghetto Boys suka cika ko'ina, parking sukayi agaban wani uncompleted building sanan Tobi ya kalleshi yace "ready"? Gyadamai mai kai yayi, hakan yasa Tobi yabude motan ya sauka shima ya sauko suka shiga cikin gidan atare, daidai sun tarar dawasu gang da sunkai su kusan 25 yara haka dabazasu wuce 20 zuwa 25yrs ba, ga jakan shi dakomi a jakan akasa sun zaxzage, ga kudi ga textbooks dinshi da credentials, suna ganin su Tobi duk suka mike tsaye suka cicciro wukake da sauri mutumin ya shige bayan Tobi dan kallonshi Tobi yayi yay murmushi sanan ya kalli wanda yaga shine Ogan su danshi ke rikeda laptop din yace "Hey Bro we came for that bagpack and everything naciki, kindly give it back ba fada mukazo ba ko hayaniya" tashi Ogan yayi cikin harshen yarbanci yace "kaci haukace ko bakason ranka ne dakazo nan inda bazaku fita rayeba" dan murmushi Tobi yayi yana jujjuya wuyanshi irin yana shirin fadan nan da turenci yace "I think you are the one that wants to die dakuka mana sata" da sauri Ogan ya kalli yaran yace "kukai mazan nan lahira" hannun riga Tobi ya tattare yace "get ready my man and now the fun begins" yay maganan daidai yaran sun taho kasu da wukake hakan yasa dayan mutumin ya manne bayanshi dana Tobi sosai jikinshi na rawa baisaba ganin wuka haka ba koyan daba, kwashe su Tobi ya shiga yi da nushi daya yana protecting mutumin dayaga baida karfi a tsorace yake yace "Hy Man be attacking bayan kunnensu ko balls dinsu" jin haka yasa wanda yakawo mai wuka zai chakamai ya kauce da sauri yawani irin tsugunna yakaimai naushi mai kyau a gwailo yaron ya zube agefen Tobi, washe baki Tobi yayi kaman yanda shima mutumin ya washe
Chapter 40 · 0% Book details