Sashe 2
Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
M SHAKUR _MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP, SHAHARAREN GROUP NE DASUKA KWARE KAN HARKAN ORDER, IMPORTATION DIN KAYA DAGA KASASHE DABAN DABAN NA DUNIYA AKAN KUDI DAN CINGILI, INDAI A MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP NE KARKAI FARGABAN YIN ORDER DA ITA DAN AIKINTA NE, TA KWARE A BANGAREN TANA HARKA DA AGENT DABAN DABAN DAGA KASASHE DABAN DABAN, ZAKU IYA TUNTUBARTA AWANAN NUMBER 08069493528, DAZARAN KUNYI SAVING ZAKU GANTA A WATSAPP KUMATA MAGANA, KARKU BARI WANAN GARABASAR TA WUCEKU_ EPISODE 1 _FREE PAGE_ Tsaye take cikin shagon kafen komputa, tana tsaye agaban kantan shagon tana sanye dawani dogon maroon hijab daya kode sosai yana jamata kasa tana kallon mutumin shagon wani dogon matashi dake zaune kan kujera gaban system yana danne danne a system din, daga gani kasan aiki yake aikin ma hala na yarinyar dake tsaye ne sabida yanda take kallonshi kaman tana hango abinda yakeyi akan system din. Zare manyan oily idanunta kawai take tana kallonshi gabanta nafaduwa tana fargaban karta fadi waec dinan bayan tasan da kyar Baba yabiya mata kudin tazana, batason abinda zaisa bazata shiga koda dan FCE bane, tana cikin dogon tunaninne taga Matashin mutumin yatashi dagakan kujeran dayake kai yay wajen printer dan daukan paper data bullo daga printer, cigaba da faduwa gabanta yayi tana kara zare idanun kaman kwan lantarki, daukan paper yayi yakoma table din yadau katin waec dinta yazo gaban kanta yamika mata takardan yana murmushi yace "congratulations Fatima Zarah an tsallake Waec kinada credit guda shida, 6 credit gareki natayaki murna, Allah ya sanyama takardan albarka" yay maganan yana mika mata takardan, karban takardan tayi da sauri tana kallon takardan tanada C a maths English da sauran important topic din dayakamata science student nadashi, wani wani irin cool charming murmushi daya lobar da dimples dinta duka biyun tasake fararen hakoranta suka bayyana, batai wata wataba tawani irin zube akasa tai sujjada, dariya mai shagon yayi yajuya abunshi yakoma kujeran zaman shi yana dariya yace "wayaga su ustaziya Faty" tashi tayi tana murmushi tasauke yar jakanta da fatar jikin jakan dukta daye tsabagen wahala ta bude zip tasaka takardan da katin ciki sanan ta maida zip din ta zage sanan takalli mai shagon tace "nagode Yaya Habu" juyowa yayi ya kalleta ya kureta da ido ita bamata lurada kallon dayake mataba tajuya tafita daga shagon da saurinta tana tafiya takasa daina murmushi tsabagen yanda take murna kaman ba gobe, ahaka taketa tafiya ita kadai har zuwa anguwan su da yara suka cika layin suna wasa ana ihu ana wasa, wucewa tayi ta shiga cikin wani dan babban gida dakeda dogon zaure, gidan na hayane dake dauke da dakuna biyar, kowani daki falo ne sai uwar daka guda biyu, bayin gidan guda hudu biyu na wanka biyu na kashi General bayi, ga makwarara wajen wanke wanke ga dankararen kitchen dinsu inda kowa ke zuwa yay girkinshi, gidan yaci uban siminti kal kal kaman zaka taka ka zame. _MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP, SHAHARAREN GROUP NE DASUKA KWARE KAN HARKAN ORDER, IMPORTATION DIN KAYA DAGA KASASHE DABAN DABAN NA DUNIYA AKAN KUDI DAN CINGILI, INDAI A MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP NE KARKAI FARGABAN YIN ORDER DA ITA DAN AIKINTA NE, TA KWARE A BANGAREN TANA HARKA DA AGENT DABAN DABAN DAGA KASASHE DABAN DABAN, ZAKU IYA TUNTUBARTA AWANAN NUMBER 08069493528, DAZARAN KUNYI SAVING ZAKU GANTA A WATSAPP KUMATA MAGANA, KARKU BARI WANAN GARABASAR TA WUCEKU_ Babu kowa a tsakar gidan, ganin machine wayyo kudina agaban dakinsu yasa tagane Babanta na nan da sauri tai dakin nasu bayan ta gaida matan gidan datagani sun fito daga kitchen suka amsata ba yabo ba fallasa, sallama tayi ahankali ta shiga falon, falone mai dan kyau daidai, yaci ledan daki, ga kujeru masu kyau ga TV bango amman karami ga labule masu kyau da agogon bango bango dakin yaci fenti milk color, yarane adakin su hudu suna wasa, dan shekara sha biyu shine babban cikinsu mai suna Habib, sai mai binshi Ishak, saina ukun Bashir, ta hudu mace karama auta wacce dabo takeyi daga ganima ba'a yayeta ba mai suna Abida, yaran gasunan kai da kai kaman gwaranni farare kyawawa dasu, Babban cikinsu Habib dake sanye da kayan kanikawa ne ta kalla tace "Baba yadawo Habib?" gyadamata kai yayi yana tashi daga inda yake yace "eh yana daki shida Mamanmu" gyadamai kai tayi sanin idan Baba da Mama nadaki duk basa shiga ciki yasa tawuce dayan dakin dake facing dakin su Baba ta shiga katifa ce katuwar gaske akasa mai tudu takusan mmaye dakin sai wata yagaggiyar katifa yar karama da aka jefa adan space din gefen dakin dayarage kusada inda ganamasgon kayansu yake, kan katifar taje ta zauna ahankali tana murmushi tasake ciro takardan waec din tana kallo shikenan itama zata shiga University kaman su Hafiza, idan Baba yafito zata gayamai yabata wayanshi takira Mami ta tasanar da ita. _MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP, SHAHARAREN GROUP NE DASUKA KWARE KAN HARKAN ORDER, IMPORTATION DIN KAYA DAGA KASASHE DABAN DABAN NA DUNIYA AKAN KUDI DAN CINGILI, INDAI A MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP NE KARKAI FARGABAN YIN ORDER DA ITA DAN AIKINTA NE, TA KWARE A BANGAREN TANA HARKA DA AGENT DABAN DABAN DAGA KASASHE DABAN DABAN, ZAKU IYA TUNTUBARTA AWANAN NUMBER 08069493528, DAZARAN KUNYI SAVING ZAKU GANTA A WATSAPP KUMATA MAGANA, KARKU BARI WANAN GARABASAR TA WUCEKU_ Tana zaune akan katifar taji muryan Maman su tafito tadauki Abida dake kuka tana lallashi sanan taji tana tambayarta. "ina Zakiyya kai Habib"? Kafinma Habib yabata amsa daga ciki sukaji muryan Baban su yana. "haba Habee nafa hanaki kiran yarinyar nan Zakiyya ki kirata da Fatiman ta, wani irin zakiyya yarinya nada suna mai kyau haka sunan diyar Annabi kina chanza mata" cikeda masifa tace "kai wlh Baban Habibu korafin ka bayi karewa kana daki kunenka na nan kana sauraron abinda mukeyi, yanzu dai me acikin suna dakake wanan bala'in da ranan nan" tai kwafa ta zauna tashiga bama Abida nono. Sanin zata sake kiranta yasa ta mike kawai tafito da saurinta tazo gabanta ta tsugunna cikeda girmamawa ahankali tace "gani Mama" harara ta watsa mata tace "kina ciki kina jina kikai shiru, saida ubanki yasa bakine sanan zaki fito mai halin munafukai, sai shegen yawo da hijabi kaman matar boka, oya ga Abida goyata kije kitchen akwai ruwa dana daura akan murhu ki hada ki kaima Baban ki bayi yaje yay wanka ki daura abincin rana" gyadamata kai tayi ta karbi Abida da zanin goyon ta datake mika mata, zata goyata kan hijabin ta daka mata tsawa tace "wai bazaki cire hijabin nan ki goya yarinyar nan ba kosaikin sakamin ita kuka nasamu tai shiru, autar Tawa zaki kashemin da zafi"? Batace komiba tacire hijabin ta ijiye sanan tajuya mata baya sabida kunya ta shiga goya Abida, binta da harara Mama tayi, shegun nonuwan nan dasuke nema sufi karfinta take boyemata yarinya kullum niki niki da hijabi, goyata tayi sanan tafice daga dakin tai hanyar kitchen itakuma Mama tajuya ta shiga ciki, ledan biredi ta dauko tafito tawurgama Habib tace "acici, shabiyu batayiba amman ka gudo daga wajen aiki kaman bakaci na safe ba, yaro saici uwa an aikoka duniya ne dankaitacin abinci, gashinan raba kaida kanninka ka kora da ruwa ka kama hanya ka koma aiki kadaiga sai yanzu zama adaura sanwa, ka kwashi su Ishak ka ijiyesu amakarantan allon malam idi" tai maganan tana watsamai harara yaron na turo mata baki yana kunkuni tawuce ta shiga dakinsu batare data karabi ta kansu ba. Kwance wani magidanci yake akan gado wanda duka duka bazai wuce 45 to 50yrs ba yana lullube da zanin gado yadaura hannunshi abayan keyanshi yana kallon fankan dake kadawa ajikin silin din dakin, kana ganinshi kasan yayi nisa a tunani gyara labulen kofan tayi ta tsige dan zanin datake daure dashi tahau kan gadon tadaga zanin gadon ta shige takai hannunta kan joystick din ta taba jin ya kwanta yasa ta kalli fuskarshi, turo baki tayi saikuma ta shiga mannewa cikin jikinshi sabida tasamu ta tayardashi sucigaba, cikin dan fushi yatureta kaman jira yake yace "Haba Rukayya ke ina cikin babban matsala bakida damuwa, kinjefani cikin matsalan keko ajikinki, kawai kin kirani gida baki barni wajen nemana ba kawai nazo gida naita miki wanan abin uwa banda wani aikin yi" yay maganan cikeda dan takaici, yace "wai sabida kinga ina sonki saisa kikemin hakane Ruka? Miliyan uku fa Rukayya ina naga hanyar miliyan uku yanzu iyye nanda sati daya zasu zo kuma, idan ban basu ba kinsan mizasuyi, kuma kekika turani naciyo bashin nan bakisa na tsinana komi dashi ba saidai kikasa nazo na kama wanan gidan hayan dayafi karfina, na saya miki kayan daki harda TV bango kikasa muka saya da fridge da katifun mu na daki yara da wanan rantamemen gadon dana siya miki kaman na amare, inda ace nai sana'a dashi da nasan inada at least wata hanyar biya amman bandashi kuma ko ajikinki, ke kawai daga safe har dare ki ganni manne dake kaman da tarayyan zamu biya bashi" cikeda kulewa tace "ya za'ayi kace ban damu da bashin da ake binka ba? Kanata wani cewa nasa ka kashemin kudin, naga aidai kaima kasai galleliyar machine wayyo kudina kana paparazzi akan titin gandujiyya, kai bakajin dadi yanda yan gidan nan suke bautamana mune yan uwan yan gayun gidan nan fa, yau taliya gobe farfesu, kullum ina jefar da ledan tsiren daka sayamin a tsakar gida suna gani, ga fridge ga TV, irin namasu kudin nan, kai bakaga yanda suke maula wajena ba, komi Maman Habib kai bakajin dadi? Babu abinda fa ba'a rokonmu, karka damu kudi zaizo zamu biya bashin sati daya ai akwai lokaci" cikeda fada yace "waini kika maida yaro Ruka? Tsafi zanyi dazan sami miliyan uku acikin kwana bakwai? Wai inama adashin dakika dinga karban kudin kina zubi kince min kwasa dubu dari biyu at least koshine nasamu nabasu wani abun" turo baki tayi tace "ni titini na kwasa nayi hidima da ita, nasoma yima Abida tari ne" wani kallo yamata yace "Abida ko Fateema"? Dauke kai tayi tace "nidai nasan kajini da kyau kakemin wanan tambayar Abida nace nafara ma tarin kayan daki, kana duba karkashin gadon nan zakaga abubuwan danasiya ma" wani irin kallonta yake saikuma yanisa yace "Abida dako shekara biyu batayi ba kokuma nace ko