Sashe 8
Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
zamu iya riketa na kwana daya ko biyu haka" shiru Baba yayi yana kallonshi cikeda damuwa, murmushi Dr yayi yace "karka damu zanyi settling hospital bill din wanan kudin hannunka ka rike na abinci dawasu abu ko" shiru Baba yayi saikuma chan ya nisa yace "Ya sunanka likita" anatse yace "sunana Imam Naseer Marafa" girgixa kai Babba yayi cikeda gamsuwa, yace "kaidan aljanna ne Naseer, Allah yamaka albarka, Allah ya saka da alheri da taimako na dakayi, azamanin nan da wuya ake samin likitoci irinku, awanan zamin likita iyaka kabiya yay treating naka, idan baka biyaba babu ruwan shi, Allah yamaka abinda kakeso kaji Naseer" shiru yayi yana kallon Baba kafin ahankali yace "Ameen nagode sir" Tashi ahankali Baba yayi yace "bari nabaka wuri" gyadamai kai kawai yayi Baba yawuce yafita, bin bayan Baba yayi da kallo yay shiru kaman wanda ke tunani kafin ya fuzarda iska ahankali ya jingina da kujeranshi tareda lumshe ido dan yagaji sosai. Bude kofanshi da akayi aka shigo yasa yabude ido kadan ya kalli kofar, wata female Doctor ce mace kyakkyawan gaske doguwa tana sanye da atampa golden da dige digen pink ajiki, ta yana kanta dawani pink gyale chiffon plain bakomi ajiki saikuma lab coat dinta fari kal yasha guga sai kamshi take bazawa wajen aljihun ta an rubuta Dr Zee ajiki, maida idanunshi yayi ya lumshe ganin itace, karasowa ciki tayi taja kujera tazauna tace "Dr Helper koma Dr Charity zankiraka am here i need help too pleaseDr" dan yatsine fuska yayi alamun he's not into her silly talk, murmushi tayi tace "okay joke apart Dr Imam, I just came in, namanta da stethoscope dina agida kuma idan HOD yaganni wlh zansha fada, please kindly aramin naka kaji kasan Helper is your second name right Dr nice" tai maganan tana kallonshi tana murmushi cikada tsokana, ahankali yabude idanunshi kadan yadan kalleta saikuma ya yatsine fuska yace "wai why are all this intern Doctors not serious haan"? Dan murmushi tayi, hakan yasa yadaure fuska yace "ina magana kina murmushi, alright go and find stethoscope awani wajen not here" da sauri cikin kara narkan da murya kaman zatai kuka tace "no fa, ni wlh badakai nake ba" ganin yaki kulata saima wayanshi daya ciro yana kunnawa yasa tace "kasandai idan HOD yakamani bani kadai zaiyi scolding bako dan ai yasani akasan kane" dagokai yayi ya kalleta baison surutu idan kuma akwai macen dayataba gani aduniyan nan datafi kowa surutu is this girl, baimasan mesa HOD su yasata under him ba, dan gajeren tsaki yaja strictly yace "tashi kidau stethoscope daga that drawer and get out of my office Zeenat" yay maganan yana mata pointing drawer dake facing su a other side of the office wall, tashi tayi ahankali tai wajen drawer tana kara nanata yanda yakira full name dinta yau, ahankali ta sanya hannayenta taja drawer tabude taciro wani sabon stethoscope mai kyau blue tadauka sanan tamaida drawer ta juyo ta kallai gani datayi yasake lumshe ido kaman mai bacci yasa murya chan kasa tace "thank you Dr Imam" sanan tadaga kafa tai hanyar kofa harta murda kofan zata fita sanan yace "Dr Zeenat" da sauri tajuyo tadan bude manyan idanunta da mamakinta jin yakirata, folder yamika mata yace "this my patient tana Emergency, monitor her, I've written everything anan idan time yayi push d injections ma left hand veins dinta, i repeat left hand, idan any complications arise give me a call, idan kuma condition dint a yay stabilising move her to ward, zanje gida yanzu under no condition should u leave his hospital saikinga dawowana" kaman zatai kuka da sauri tace "waimena maka daga zuwana zaka hadani da irin aikin nan, yanzu harsaika dawo zan tafi? Inada bridal shower dazanyi attending fa by 5pm" tai maganan tana batarai sosai, dauke kai yayi yashiga tattare kayanshi tana tsaye tana kunkuni, lab coat yacire yarage dagashi sai kananun kayan dake jikinshi yadau wayanshi da car key dawani folder yazo zai wuce ya watsa mata wani mugun kallo, hadiye maganan tayi tareda sunnar da kanta kasa dan jitayi yacika mata ido bazata iya kallonshi ko cigaba da korafin ba yawuce yafita yabarta tsaye anan, takai kusan 2min dukan kirjinta bai dawo daidai ba sanan tasamu tabude kofan tafita har lokacin kamshin shi takeji.* _DISASTROUS LOVE_ _MASIFAFFIYAR KAUNA_