← Book details Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 97

Sashe 4

Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

rungumota side dinshi yace "kiyi addu'a Allah bama babanki kudi, zan sayamiki waya tunda kema yanzu kin dawo budurwa kaman kowace budurwa, da sababbin zannuwan da takalma kinji, da kayan kwalliya" murmushi tayi akunyace tace "Baba karka damu komi lokacine, Allah ya azurtaka da arziki na halas katafi karkai latti" tai maganan tareda juyawa da sauri batason ta nunamai kalamanshi sun tabata, tsayawa yayi shima yabita da kallo harta shige ciki, maganan da Ruka tamai dazu ya sosamai rai ba kadanba kuma deep down yasan da gaskene Zara batada ko mashinshini guda, kuma laifinshi ne yarinya batada kayan arziki tana mace kuma budurwa datake tasawa yanzu amman kayanta sunfi name abincin saidawa kodewa, hijaban ta biyu kacal da maroon dawani mai ruwan toka sun kode harsun fara ja akai tsabagen kodewa, batada wani takalmi na fita sai silifas, kullum fuskarnan nata fayau babu komi aciki yaza'ayi saurayi zai gani ya yaba, koya sami kudi yace zai mata Ruka tahana, saisa yakeson yarinya yanzu ta shirya taje wajen Babarta hutu amman yasan Ruka bazata bariba, ganin dogon tunanin dayake yasa kanshi yafar*a sarawa yasa yajuya yafita kar hawan jininshi yatashi, machine yatada yafice daga anguwan gabaki daya _DISASTROUS LOVE_ _MASIFAFFIYAR KAUNA_ _G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&G_ M SHAKUR EPISODE 3 _FREE PAGE_ Koda takoma daki bataga Maman nasuba hakan yasa ta shiga dakinta ta ijiye komi taboye kudin da Baba yabata sanan tafito tatattare falon inda sukaci abinci ta share tafita da kwanukan ta wanke sanan tadawo ta kunna turaren tsinke afalon ganin ana kiran la'asar yasa tadauro alwala ta shigo tai salla sanan ta shiga dakinta ta sanya Ash color hijabin ta har kasa dan shine na islamiyyan su sanan tadauki jakar islamiyyan tafito, gaban dakin Maman su taje ta tsaya tai sallama ahankali, daga ciki maman tace "lafiya kin isheni da sallama yarinya saikace rainon mayu" batadamu da maganar ba dan inda sabo tasaba, ahankali tace "zantafi islamiyya ne Mama natafi"? Ihu tamata daga taciki tace "au so kike ubanki yazo yace nahanaki zuwa islamiyya ko uwar shairi da kinibibi wuce ki bacemin daga gaban daki, mayya mai neman rabani da mijina" juyawa tayi ahankali tafice tai waje da sauri sauri take tafiya kaman mai jiran wata, tayi nisa sosai tahango wata yarinya kana ganinsu kaga sa'oinnin juna itama tana sanye da Ash color hijabin kaman nata tana tsaye karkashin bishiya tun kafin takaraso wajen tace "wlh kika samu latti Fatima saina rama dukan lattin da za'a min ajikinki" dan dariya tayi ta bangaje mata kafada tace "dalla chan bamuyi latti ba har yanzu hudu bata cikaba" binta da sauri yarinyar tayi tace "au hakama zakice"? Murguda mata baki tayi tace "eh din" dariya yarinyar tayi tace "tokijirani sai sauri kike FatynBaba" juyowa tayi ta tsaya chak tareda rike waist dinta tace "ohkay ke Maryam dinan kin cika wayau, sabida muyi lattin kirama dukan ajikina ko saisa kike cewa najiraki" dariya Maryam tayi takaraso inda take tareda mika mata wani leda tace "gashi nakine" da sauri ta karba tabude taga sabon hijabin islamiyyan sune Ash wanan ma anyi dinkin mai hula mai kyau juyowa tayi ahankali ta kalli Maryam din dake kallonta, murmushi tayi ta bangaje mata kafada tace "ke dalla common, Babanmu nacema hijaban mu na Islamiyya sun tsufa, shine yace nazo shago anjima a aunani a dinka mana, shine naje kinsan yanada yadin hijabai masu kyau, na zaba yabama yaron shagonshi ya dinka mana dinki daya, nima bansa nawa bane sabida nasan bazaki saka naki yauba, sai gobe zamu saka mu fasa islamiyyan tareko" gyadama Maryam dinkai tayi saikuma ta rungumeta kawai, da sauri Maryam ta tureta tace "dalla ke dadina dake son jiki awaje zaki wani rungumeni sabida hijabi, har yanzu maganana nanan kikasa mukai latti saina rama dukan ajikinki" Maryam tai maganana tana dariya taredayin gaba, share hawayenta tayi ahankali sanan tabi Maryam din da sauri tace "toni kijirani" haka suka dinga tafiya suna shirme cikin ikon Allah koda sukakai ba'a fara taron latti ba hakan yasa suka wuce ajinsu direct aka fara karatu. _G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&G_ Karfe shida aka tashesu daga islamiyan, saidaa ta tattaro kansu Sadiq dasuka taho tareda Habib sanan suka fito Habib yay gaba da kannin nashi itakuma suna jerowa tareda Maryam suna hira har sukakai wajen bishiya suka tsaya Maryam tace "kinga yanda Malam Sani keta kallonki kuwa dakike biyamai karatu" dan hararanta tayi tace "kallo, kallon lafiya, ni banmasan anyi hakaba kin iya sa ido Maryam" murmushi kawai Maryam tayi tace "nidai kidinga saka nikabi, kyanki yay yawa yarnan" hannu takai zata kwadama Maryam din duka ta kwashe aguje tadau hanyar layinsu itakuma tacigaba da tafiya tana dan murmushi, ana magrib suka shiga gida, gaida mutanen gidansu tayi sanan tai dakinsu Mama tasamu afalo zaune tana bama Abida nono tana ganinta tace "wuce kije ki kada miyan dake wuta" dakinsu ta shiga ta cire hijabin islamiyyan ta tasaka maroon tafito zatai kitchen, da sauri Mama tamata ihu. "sokike kije ki kone a kitchen Babanki yakusa cinyeni, wuce dan ubanki kicire hijabin nan bansan ubanwa kike boyema yan kirgan dangin nan dakika faraba" cikin kunan rai Habib yace "waike Mama kullum saikin ma Ya Faty fada dawani wai kirgan dangi mehaka dan Allah, ni wlh kidena damun Ya Faty" cikin fushi ya kalli Fatima da kanta kekasa yace "Ya Faty jekiyi da hijabin ki kinji ai Malam yace bakyau mace na yawo haka ba lullubi" mugun dundu Mama takaimai abaya tace "kai dan ubanka ko ubanka bayaja da maganata balle kai yaushe aka haifeka? Duka duka shekarunka sha biyu kake gayamin magana eh dan ubanka" cikin kuka da fushi yace "to meta......" da sauri Fatyma tajawoshi taredakai hannu bakinshi ta taushe tahanashi magana dan Allah ya zuba mata son kanninta kaman me, cikin fushi Mama ta ijiye Abida kan kujeran ta tashi tace "ni uwarka kakema rashin kunya kan wanan yarinyar eh Habibu" da sauri Faty ta tura Habib din bayanta tace "kiyakuri Mama dan Allah" gauramata mahaukacin mari Mama tayi da saida yasa tai layi kaman zata fadi sanan ta fizgota da karfi ta kumata da bango tareda shake mata wuya tace "ni zaki juyawa yarana akaina? Yaran dana haifa zaki batamin su? Harda kama Habib kina boyewa a bayanki irin ga danki dinan ke uwarshi wlh yauna lahira saiya fikijin dadi" tai maganan tareda fizgo wayan TV tashiga lafta mata tun tana daurewa bata ihu tahau kuka sosai tana ihu tana yakuri Mama, Habib na tsaye gefe yana kuka sosai kaman ranshi zai fita, duka yaran harda Abida ma saisuka hau kuka ganin ana dukan yayansu ga Mama sai uban ihu take tana jibgarta kaman daman tana tikeda ita, wata makociyarsu ce dake shiri da Maman tashigo tana zuwa rike Mama tayi tace "ya isa hakanan Maman Habib" cikin kumfan baki tace "barni na kashe yarinyar nan nahuta Zainabu, yarinya tarabani da mijina, mijina saiya hanani kudi yabama wanan makiran, komi ita komi ita, yanzu kuma nema take tarabani da yarana, to wlh bata isaba saina kasheta nakashe banza taga idan da abinda ubanta zai iya yayi kuma zama daram sai yanda nayi da uban nata datake takama take tunkaho dashi" tai maganan tana haki sosai kaman zuciyanta zai fito baki, kallon Fatima dake duke tana kuka sosai tayi kanta akan guiwanta tace "kekuma tashi kibar nan kije kiyi girkin, kafin natayata kara miki algunguma mai kama da larabawan jahannama" ahankali tashiga tattaba bango tamike tsaye da kyar jikinta har kyarma yake tsabagen wayan wutan datasha sanan tawuce ta lallaba tafita daga dakin tai kitchen, saida tafita sanan matar tace "kiyakuri kedai kiyita addu'a Allah bata miji ta tattara tabar miki gidan nan ki sakata ki walada mijinki" da sauri tace "ina Allah yabata, yarinya sai bakin jini gadon uwarta, ko mashinshini batada shi" da sauri matar tace "duk kyan nan nata" da sauri Maman Habib tace "kyan dan maciji ne, tayi gadon bakin hali ina zata samu wanda zai kwasheta yakaita gidanshi amatsayin mata"? "adai dinga hakuri Maman Habibu amman dai ina bayanki kitashi tsaye karki bari tabata miki yara" murmushi tayi tace "nagode Maman Zainab, bari ta sauke abinci zan aiko miki dashi, wlh nagaji dacin shinkafa taliya kullum yau kawai nai marmarin tuwon shinkafa da miyan taushe da kan rago zai aiko miki dashi nariga nagama miyar" cikeda jin dadi har wani sude baki Maman Zainab take tace "Allah bar mana Maman Habibu kap gidan nan babu kaman ki, godiya nake, bari naje to", fita tayi tana karamata godiya, itakuma Mama ta kalli Habib dake kuka har lokacin tace "zonan" zuwa yayi yazauna agabanta shafa kanshi tayi tace "kaga kasa nadakeka a banza ina ruwanka da wanan shegiyar nace muku ba yar uwarku bace, ya isa dena kukan jedaki kadauko biredin dana ijiye muku kaci kaida kanninka" ko kallonta baiyiba yatashi ya shige dakinsu fuuuu, tabe baki tayi tadauki Abida tace "mayyar nono ungo kafin ki kashemin dodon kunne" . _G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan
Chapter 4 · 0% Book details