Sashe 16
Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
taji wani iri yanda taga Babanta nakuka, sun dade sosai ahaka sanan tace "Baba tashi mutafi zamuyi latti" tana maganan wayanshi na ringing sakinta yayi yana duba wayan yaga Oga Abdul ne bai daukaba ya maida aljihu yatashi tareda karban hijabin ya share mata fuska sanan ya ijiye hijabin awajen suka fito yahau machine itama tahau yatada suka shiga titi, tunda tai wayau bata taba fita ba hijabi ba ballema har ba dan Kwali yau itace iska ke daka yana ratsa tundaga kanta, kunnuwanta da wuyanta haka, haka suka karasa hotel din mai suna Prestigious, yana shiga yaga Oga Abdul yaci suit sai kallon agogon dake daure a hannunshi yake, yana ganinsu yataho dagudu murya chan kasa yace "kayi latti sosai sokake kasamu a amtsala" ya kalli Fateema yace "good, from now sunanki Khalid understood" gyadamai kai tayi, yace "any question dasuka miki answer them da turenci, sukaga u are educated zasu yanka miki albashi mai yawa nan da nan agama biyan bashin babanki" tasake gyadamai kai, ya shiga gabansu da saurin shi yace "let's go" jikinshi har rawa yake hakan yasa taji gabanta na dukan uku uku, shiga hotel din sukayi sukai upstairs, wani babban hall suka shiga ga security guards gardawa aciki, hall ne da aka jera kujeru hadaddun gaske, ga maza manya magidanta amman irin talakawan nan haka kusan su 100+, ga yara samari maza agefe dabazasu wuce sa'oninta ba zuwa yan 22yrs suma zaune kan kujeru adayan bangaren kusan su 63 ko morethan ma, saikan hadadden stage din da akai decorating da flowers aka zuba wasu arnayen kujeru wasu hadaddun manya manyan lawyers ne da baristoci sunci suit suna rubuce rubuce ga laptops agaban su, da printers, kallon Baba Oga Abdul yayi yace "kujirani anan lemme talk to them nazo dan ankira sunanka yafi sau uku" stage din yayi zuwa wajen wani babban Barrister dan tsoho nema dukawa yayi yamai magana a kunne sanan yadawo yaje wajensu Baba kujera yanuna musu yace "kazauna za'a kiraku" zama Baba yayi yana rikeda hannun Fatima itama ta zauna a kujeran kusada shi, saishima Oga Abdul yazauna kusada Baba yace "yanzu nan police suka tafi dawani mutumi thank God kayi tunani mai kyau da....." "Muhammad Alhasan Muhammad" shiru Oga Abdul yayi jin ankira Baba, faduwa gaban Baba yayi haka itama Fatima dan yanzu saitaji tanajin tsoro sosai dan ga dukkan alamu wanan babban organization ne baba yaci kudinsu duk azatonta tazaci is just a small something, hannun Fatima yarike sukai stage, cikeda girmamawa ya gaida lawyoyin da duk suka zubamai ido suna kallon yanda danshi yay kama dashi, yace "yallabai bangama hada kudin ba amman ga......" kafin yagama maganan Barrister ya kalli Fatima yana gyara glasses din idanunshi yace "young Man akwai turenci" gyadamai Fatima tayi ahankali, yace "whats your name" gyara muryanta tayi ba yabo ba fallasa dudda muryam baiyi kaman na namiji ba hakama baiyi kaman na mace ba tace "ahhhm Khalid Muhammad" ajiyan zuciya Oga Abdul ya sauke, Barrister yace "how old are you"? Anatse tace "i am 19yrs old" documenting sukayi sanan yace "what level are you in school" ahankali tace "I just write waec this year" gyadamai kai yayi yace "what are you good at Khalid? What can you do what are your skills?" Shiru tayi saikuma ta kalli Baba taga kanshi na kasa sanan takalli Barrister tace "only house work" da sauri Barrister yace "don't you go to work" gyadamai kai tayi tace "only school and islamiyya i go" gyadakai yayi cikeda gamsuwa dan yaga yaron na kokari turenci shi dai ba laifi normal turenci yaro dan arewa dayaje school, juyawa yayi ya karbi wani bracelet dataga anciro daga wani akwati an rubuta 65 ajiki yace "give me your hand" bashi hannunta tayi ya nada mata bracelet din sanan yakalli Baba yace "because your son is educated and can communicate da English, salary dinshi every month will be 120,000 naira, yakama zaimana aikin watanni ashirin da biyar (25) shekara biyu da wata daya kenan" ya kalli Fatima da gabanta ke wani irin mummunan faduwa yanuna mata bangaren yaran yace "go and sit there with your mate, Abdul take her luggage to the car" gana masgonta Oga Abdul yafita dashi aka nunama Abba wajen zaman manya yawuce yaje ya zauna yakasa dagokai. Wuraren 12 suka gama, sanan aka shigo da abainci yaran aka rabamawa hadadden fried rice da chicken da salad da ruwa da juice Barrister yace "eat Boys" yara sai dadi sukeji ganin abincin da basaci agida nan da nan suka cika hall din da hayaniya sanan akai dismissing iyayen su, security guards na fitarda su suka fara fita, da sauri tadaga kai ta kalli Baba kin kallonta yayi harya fita tareda Oga Abdu yaki juyowa ya kalleta saidai yana tafiya ahankali kaman baida jini ajiki, ahankali taji hawaye yazubo mata kaman daga sama taji an rungumota takafad. "Dalla karkai kuka saikace wani mace eh guy" da sauri ta daga kanta wani saurayi tagani dabazai wuce 20 ba yana sanye da riga da wando shima kabar da hannunshi tayi cikin sabon muryanta tace "dalla malam karka kara tabani" taja kujeran ta ta matsar tabude jakan bayanta tasa takeaway aciki ta ijiye jakan akasa ta kafa fuskarta akan kafafunta kawai ta shiga kuka mai taba zuciya. _MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number takira 07010439656 , sanan zaki samesu a watsapp ta wanan number 08106788714 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._ _DISASTROUS LOVE_ _MASIFAFFIYAR KAUNA_ M SHAKUR EPISODE 1 _FREE PAGE_ Sauran yaranne sukahau dariya though not all dan wasuma sunyi shiru sun natsu daga gani suna kewan iyayensu, shikuma yaron wani hararan shi yayi yafaracin abincishi kawai, takai kusan 20min ahaka, sanan ta tashi tagoge fuskarta tas da idanunta tass, ahankali taduka tadau jakan budewa tayi tadauki takeaway ta tabude ahankali tashiga turama kanta abincin sanan ta ijiye acikin jaka duk suna zaune wajen su kadai sai hayaniya yaran suke har wajajen karfe uku sanan securities suka shigo sukace "kutashi kuyi layi masu son amfani da bayi suyi, ga bayi nan anbude muku night journey zakuyi so get ready, prepare use 10min to do everything" bayika hudu dake dankareren hall din suka bude musu, ahankali ta tashi ta goya jakanta tai hanyar bayin wasuma nabinta abaya, shiga daya daga cikin bayinka tayi tarufe harda key sanan ta tsaya ta kalli kanta really fa batada banbanci da namiji da sauri ta dauke idanunta daga madubi dan bataso tana kallon kanta, fitsari tayi kaman tasani ta soke wani pad a aljihun wando dudda bata wani heavy flow dan gobenema zata gama amman saida ta dauka wanan dataji night journey zasuyi yasa ta chanza ta gyara kanta tareda flushing old one din ta shirya tsaf sanan tafito goyeda jakanta, tana fitowa security yanunata yace "kai kagama?" Gyadamai kai yayi hakan yasa security yanuna mai kofa yace "jemota ajeraku" fita yayi ahankali ya sauka kasa tareda wasu yaran, wani babban luxurious bus tagani kaman irin nasu landstar wanan hadadden bala'i kaman ma sabo, security dake tsaye gaban mota yace "oya zoka shiga" karasawa tayi ahankali ta taka tahau motan wani sanyi ne taji motar ga dankareren tv a kunne ga sanyi ga labulaye, security dake tsaye a tsakiyan motarne yana nunama kowa inda zai zauna yanuna mata sit yace "jeka zauna achan" karasawa tayi ahankali ta zauna kusada window, wani yaro aka turo yazauna kusa da ita dan sit bibbiyune jere akowani side, kafin agama jerasu tass karfe hudu, sanan taga wanan babban lawyer dayasa mata bracelet yana magana da security dukansu su biyar yabasu kudi wrapper yan dubu guda biyu har kasa suka duka sunamai godiya suna Allah iso dasu lafiya gobe da alamu su flight zasubi sanan dukansu biyardin suka shigo motan, daya ya zauna mazaunin direba, daya adayan bangaren mataimakin direba, sai uku suka zauna a first row na bayan direba dabasu saka any of the children akaiba, sanan suka tada motar suna dagama Barrister hannu harsuka fita daga hotel din suka dauki hanyar barin kano motar yay tsit sai securities din dake hira abinsu. Ahankali ta lumshe ido azuciyanta tace "ina zaki Fatima Zarah? Wani kasa ko gari za'a kaiki? Nazaci anan kano zanyi aikatau amman wanan damuke barin garin kano ina zamu? Yau nice nake rayuwa amatsayin namiji ina amsa sunan Khalid, yau nine nake wani wuri da babu halitta daya dana sani, nine bana tareda mahaifina ko kannaina, nine nake barin garin danake zuea wani wuri daban ma saniba, Ya Allah kaga zuciyata Alkhairi nake nufima mahaifina Ya Allah na fawwala maka al amarina da rayuwata gabaki daya Ya Allah ka kareni ka tsareni, I am so scared, har kasan zuciyana inaji dabanyi wanan abinba amman kuma har kasan zuciyana inaji zan iya mutuwa aka kullemin Baba" hawaye ta share ta kalli gefe tadan bude labulen window ta kadan tana kallon hanya, itadai tunda take da wayonta bata taba tafiya tabar kano ba amman wanan tafiyan da ake motarsu na famfala uban gudu tasan Kano zasu bari, idanunta biyu harsuka fita daga kano suka kai zaria suka isa kaduna harsuka dauki hanyar Abuja lokacin dare yasoma yi, ganin tafarajin yunwa yasa tabude jakanta tasauki abincin taci takoshi tasha ruwa sanan ta ijiye ta gyara zama tadan saci kallon yaran dake gefenta taga shi yamayi bacci, hakan yasa ta zubama TV dake aiki a motar ido tana kallon film din da akeyi nafada, ahaka wuraren goma nadare