Sashe 21
Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
prince ne Olori tace abashi wajen kwanan shi amatsayinshi na yaron dakema prince aiki, wani karamin daki head Guard din ya kaishi dake dauke da gado daya da katifa irin nayan boarding school, dakin dan karami babu komi ciki banda gadon sanan yace "ga dakin yaron dakema prince aiki nan, sanan dole kadinga wanka kullum kafin kaje bangaren shi dan baison datti, daga karfe biyar na safe, anyway yadawo dai da kanshi zai gayamaka kome yakeso prince kullum yake chanza rules dinshi" sanan yaa fito dashi ya nunamai bayin su masu aiki sanan aka bashi abinci akace yaci yay wanka sanan yahuta aka shigo da ganamasgon shi ta tura a karkashin gado, fita tayi ta tafi bayi, wanka tayi tai wankan tsarki gabaki daya sanan tadawo dakin nata ta kulle daki tasa sakata, amfani da masallacin data gani a gidan dazasu shigo dazu tayi ta gane gabas agurguje ta nemi wani clean zani dake cikin gana masgon ta ta rufa dashi tai salla sanan ta shirya tacire sakatan tahau gado ko cikakken minti daya batayiba bacci yay awon gaba da ita. Ba ita tashiba sai wajajen Magrib, abinda yamugun bata mamaki yanda taga suna harkan gabansu babu wanda yadamu da ita, bayi ta shiga tadauro alwala tadawo dakin tarufe kofa tasaka sakata sanan tai la'asar tai magrib ma dataji an kira sanan tazauna tana addu'a, wanan babban gidan da aka kawota tana mugun tsoronshi tana kuma addu'a Allah yafitar da ita daga gidan nan lafiya, Allah ya tsareta sanan Allah yakareta Allah yabama Baba aikinyi yasami kudi yazo yacirota takoma gidansu cikin yan uwanta tacigaba darayuwa abinta tafara school, tai kewan Habib, Sadeeq dakuma Abidan ta. ***** Washegari. Bayan tai sallan asubahi ta linke komi tazare sakatan sanan ta kwanta akan gadonta tana lazimi da yatsa sanan aka bude kofarta, head Guard ne ya shigo muryanshi ba wasa yace "yau Prince ke buga final match dinshi, ka'idan shine babu wanda zai kalla match din zadai muyi addu'a club dinshi chelsea suci amman kallo sai gobe idan ya iso, nan kowa na gidan nan gabaki dayanmu harda me martaba dashi zamu fito compound a kunna projector a compound muhadu dukanmu akalla ana celebration, yau za'ama fadan nan gabaki daya special sanitation, but kai kana cikin wayanda zasuje bangaren Prince ku gyara dudda bazaka taba komiba kawai zaka tsayane kana kallon mesukeyi karka taba komi kagane" gyadamai kai yayi ahankali, yace "muje" tashi tayi tadau keto dinta tasaka sanan tabishi suka fita, daman bangaren dasuka shiga jiya guda biyune, dayan bangaren taga sunje, bude kofan head Guard yayi ya shiga tabishi abaya, baki tabude waaaa tana kallon dakin, wani irin curved duplex building ne da benen na tsakiyan falonne kuma yatafi sama kaman wani bishiya a malkwade ga chandelier light dasuka kara haske milk color dakin yasa sukai kyau, dakin kana shiga kasan dakin dangata ne, gawasu kujeru dabata irinsu aduka bangaren dataje ba, stairs head guard yahau haryay nisa yajuyo ganinshi har lokacin a tsaye a kasa yasa yace "let's go" bedroom dinshi suka shiga inda taga wasu ma'aikata suna gyarawa kaman suna gyara kwai, tunda take aduniya ko'a mafarki bata taba ganin irin gadon dake dakinshi ba, gashi an zagaye gadon da wasu fararen sharasharan labule, ga wani dankareren katon hoto dake manne jikin bango saman gadon, kallon hoton tayi taga saurayine tsaye ya juyama hoton baya yana rike da ball yana sanye da kayan jersey na chelsea bayan rigan an rubuta Tobi sanan ga kanshi anmai wasu yan fici ficin twisting kaman gashin kan mawakin nan Omalay, kafafuwan shi tabida kallo yanda suka b bubbude yanada boleg aranta tace "aiko zai iya kwallo daga gani, Sadiq dinmu shima gwame ne ya iya kwallo dudda yarone shi, danma Mama tana hanashi kwallon sabida yadinga zuwa aiki da yanzu yadawo pro. Magana guard din yama cleaners din sanan yabarta awajen yawuce yafita, haka suka cigaba da gyaran tana kallonsu tana binsu duk inda suka saka kafa. Suna cikin aikin aka shigo Matar jiyace, Mum tareda wasu Maza guda biyu suna rike dakayayyaki a hannunsu biyu suka hayo saman tana musu magana da tureci tace "hope kayan nan is perfect bansan abinda zai batama Tobi rai yadawo gobe, gobefa warhaka ya iso" gabaki dayansu daga cleaners din har ita zubewa sukayi akasa suna gaisheta tsaki tayi tare da dauke kai tai hanyar dakin dashine closet din dakin tabude suka shiga, kayane cike, ga bangaren takalma, sneakers sunfi kala hamsin, ga flat shoes, ga cover shoes ga palms, ga takalman kwallo duka designers, ga bangaren turaruka da mayunkan shafa, ko'ina a closet din wardrobe ne, nuna musu wajen kayanshi tayi tace "oya kujera anan" jera kayan suka shiga yi tana kallon kayan tana murmushi sanan suka gama suka fito suka sauka suka fice. Saida yamma suka gama aikin dakin tafito tadawo ta mugun gaji wani zubinma tsayuwa kallon aiki yamafi wahala kan asalin aiki ita har gwara asata aiki dantafi sabawa da wanan tsayuwan datakeyi this days bayanta ciwo yake hakama boobs dinta lallabawa tayi ta dauro alwala ta shige dakinta tai salla. Yau tun safe kamshin girki kala kala yahana hancinta sukuni, gidan kaman biki ake, daman tunda sassafe take wanka ta shirya tsaf, yau wata dark blue riga tasaka da akai zanen mota agabanta saikuma tasa dogon wandon jeans burgujeje as usual sanan tasa kito dinta tafito tana tafiya ahankali tana kara kallon gidan fita tayi daga bangarensu nayan aiki ta shiga bangaren Olori (Queen) tana tafiya ita kadai ahankali kaman wata matsoraciya tana kallon yanda kowa ke aikin gabanshi. "Hey You" taji muryan mace daga sama, kafin tadaga kanta taji wata tace "who are you calling Dami"? Cikin wani irin yanayi na wulakanci tai pointing Fatima dake kasa tace "that boy, Tobi's house boy, Hey you don't you hear that am calling you" da sauri Fatima ta daga kanta tareda kai hannunta ta dafa kirjinta tace "me? Are you calling me" hararanshi tayi tace "with his stupid hausa intonation malo boy, go back to your side i hate seeing workers like you rooming about a side dinmu" dariya sauran sukayi dayan mai suna Kende tace "but the boy is cute though, with his big bald head" suka kwashe da dariya, dukansu ukun, mai suna Taye dansu yan biyune, bayan Ayobami wacce tai aure sai yan biyu, Taye da Kende, sai Damilola wacce suke cema Dami, sai OluwaTobi dasuke cema Tobi, ahankali wacce kekan swinging chair wajen tana kwance tana danna waya tace "but deep down I miss him fa, almost 6month bamu ganshi ba I miss his stress, his stubbornness and his anger" hararanta Dami tayi ta tashi tawuce fuu tabar wajen, sauka kasa tayi sabida itama kamshin girkin ya isheta dining taje tashiga bubbude hadaddun warmers din da aka jera hartakai kan warmer dake dauke da peppered gizzard da sauri ta dauki plate da spoon zata deba Mum data fito kenan daga kitchen tace "don't touch that food" da sauri ta kalli Maman nata rai abace tace "why"? Hararanta Mum tayi tace "because I didn't make it for you na Tobi ne" maida kulan tayi tarufe tawuce fuuuu tafice daga dakin tawuce fada bata damu da mutanen dake fadaba tawani fashe da kuka tafada jikin Babanta ashagwabe tace "Daddy i don't like what Mum is doing to me, Mummy bata girki sai in Tobi na nan, wai yanzu dan zanci gizzard din datayi shine tahanani" daga Oba har Otun murmushi sukayi, Waziri yama mutanen fadan alamu dasu fita sanan Oba yay magana, dagota yayi ya share mata hawayen datake yace "common Dami, waike mesa jealous princess ce kinbama Tobi good 4yrs but kina all this eh, dan Maman shi tamai gizzard we all know he likes dat idan kinason gizzard kisa kuku yamiki naki special one" makemai kafada tayi tace "nina Mum nakeso" shiru yayi yana kallonta saikawai yay murmushi yace "tashi kitafi to ganinan zuwa gida, kice nace tabaki" murmushi tayi da gudunta ta tashi tafita, Waziri yace "Dami Dami, Dami trouble" Agogo Sarki ya kalla yace "is almost 1, afara shirya motoci mutafi airport" gyadamaikai Waziri yayi ya kalli guard, dasauri guard din yafita daga fadan dan fara shirya motoci. _MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number 08106788714 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._ _DISASTROUS LOVE_ _MASIFAFFIYAR KAUNA_ _FOR BUSINESS ADVERT, PROMOTION CHAT ME M SHAKUR AWANAN NUMBER 07012181461_