← Book details Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 97

Sashe 32

Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

M SHAKUR
EPISODE 2
Yauma kaman kullum yau bata saka suit ba dan wlh tagaji dasakasu, suncika nauyi, cikin kayan tadauko wani fari da navy blue color t-shirt yana daya daga cikin kayan da Anty Ayobami tabata, sanan tasaka dogon wandon baki yamata kyau, ita yanzu ma abin harta soma sabawa dashi rayuwa akayan maza, zama tayi ta lallaba tasaka kito dinta data manta rabonta tasashi tagaji da saka cover shoe, sanan tadau p-cap da Anty Ayo tabata wanda bata taba sakawa ba tasaka tarufe kwaikwadon kan, sanan tafito bayan tayi salla tayi azkar tayi nafulfuli, dayake babu madubi kuma asuba ne yasa bataga kanta ba kawai tafito as usual Head Guard yakaita har gaban dakin prince sanan yatafi, shiga ciki tayi ahankali maranta na ciwo na ovulation fa zatayi wanan karan tayi MP tagama shiru bako ciwo daya sabida magungunan da likitan nan yabata da Mama tasaka mata ajaka, hawa sama tayi tana tafiya ahankali tagaji, kodan sabida batai bacci dawuri bane jiya dasuka fita da prince saida tanaji Babanshi yakira shi yana masifa kan yadena kaiwa dare haka gashi baya fita da guards sanan suka dawo gida, sukabar gidan kwallo stadium na lagos wuraren 12 nadare, ko kadan bacci bai isheta ba. Dakinshi ta shiga as usual taganshi yana bacci kullum inta shiga takanji kaman taje ta tasheshi yaje masallaci amman ina zata iya, aikace aikacenta na safe tayi tsaf tagama kafin six na safe sanan tadawo tai kneeling tana jiran farkawanshi as usual, gyangyadi yasoma dibanta sosai hakan yasa ta jingina da bango ta gyara kafanta ta zauna tanadan sake ware idanun tana kallon agogo ganin karfe 6 da minti biyar hakan yasa tacigaba da zama tana kokarin danne wani mugun baccin datakeji dabata tabajin irinshi ba tunda tafara aikin nan tun tana bubbude ido tana kallon agogo har idanun finally suka rufe kawai tabi lafiyar lallausan carpet din kasan dakin tawani lankwashe awajen sabida sanyin AC tana bacci ga P-cap din daya rufe fuskanta saidai bakinta dayay pink yirrr suka tattare sukai mugun kyau.
Karfe seven dot yafarka shima da kyar sabida rashin baccin dabaiyi dawuri jiyaba, wani irin slow yet ear piercing minshari ne yaji yana ratsa mai kunnuwa hakan yasa yasake bude idanuwanshi tangaras tareda tashi da sauri ya zauna trying ya gano daga ina yakejin karan minshari saikuma dawani irin sauri yamika hannunshi ya yaye labulen daya zagaye gadon nashi idanunshi suka sauka akan Fatima data takure akasa kana ganinta kasan sanyin AC yamata yawa P-cap din yarufe idanunta tass banda dan karamin bakinta da siririn hancinta ko kadan batada minsharin bacci tsabagen wahala da rashin samin ishahsen bacci tunda tazo gidan nanne yasa dazaran ta kwanta bacci zata fara minshari.
Tundaga kan fararen kafafunta dake cikin wani bakin simple kito yake kallo, yatsunta yan dogaye dasu masu kyau, kumbunanta fararen fat masu shegen kyau kaman ba kumban namiji ba, yabi trouser dake cikinta da kallo, harzuwa kan rigan dayasan rigan da Anty Ayo tabashi ne, sanan idanunshi suka sauka akan fuskanta, tunda yake da yaron baitama yaron kallon dayakai up to na one cikakken minute ba sai yau, yanda yaga yaron yatakure sosai yana minshari yasa yaji hakanan yabashi tausayi, this is yaro d he don't think yakai 20yrs, lokacin dayake his age mate baijin ko tsintsiya yataba rikewa ba but this small boy iyayenshi suka kawo aikatau, samin kanshi yayi da tashi ahankali ya sauka daga kan gadon yaja bargon saman gadonshi yaje har inda yake kwance ya tsugunna ya rufamai sanan still ya tsugunna yana kallon yaron, hakanan aranshi yace da ace yaron nan mace ne da anga kyau sabida yanda yakafe fuskanshi da ido, ahankali yakai hannunshi yadaura akan P-cap din, gently yacire p-cap din ya ijiye agefenta sanan yadawo da fuskarshi yadaura akan idanunta dakenan a kulle yana kallon gashin idanunta, friends dinshi na cewa yanada cikan gashin idanu amman saiyaga yaron nan yafishi, gashi dana cikan girama bakin kirin masu kyalli, sauke idanunshi yayi akan lips din yaron saikawai yaji yaron yabashi tausayi zai rage sashi yawan aiki dudda deep down yaron ya mugun kwantamai dan baida kiwuya, ga yaron nada tsabta gashi ya iya small small abunuwa dake burgess dazaran yaganshi zaune ko chatting yakeyi saida yaga yaron yakawo mai wani abu ko fruits salad kokuma dai something that made him to appreciate the boy deep down batare daya taba nunamai ba daidai da so daya. Tashi yayi ahankali ya shiga bayi wanka yayi yafito ya shirya tsaf yazo kusada ita ya shinfida dadduna yay salla, sanan yawuce yafita jogging as usual.
Koda yadawo flat dinsu yawuce for breakfast, as usual yaga yauma shisuke jira, kujera yaja ya zauna bayan yagaida su Mum tace "where is your Boy"? Ganin batagansu tareba, dan jim yayi saikuma kaman baison yin magana yace "I left him yamin aiki saisa yau bane dashiba" "oh I see" Mum tafadi tana hadamai abinci, Dad yace "namaka magana fara zuwa company ka so that you will get use to the place bakace komiba" dan yatsine fuska yayi saikuma yajuyo ya kalli Mai Martaba yace "Dad i don't want to, end of this month zanyi tafiya inada match a Saudi" wani kallo Babanshi yamai saikuma yarage murya yakai hannunshi yadaura abayanshi yace "Tobi I allow you kana buga kwallo because I know is ur hubby sanan kai yaro ne then, but yanzu kasoma girma and I am getting old, inaso kabar kwallon nan concentrate anan in yaso kana zuwa company ka sanan ana koyamaka kan sarautan da wasu abubuwa na al'adun mu so that u will start getti
ng use to you sabida inaso na sauka dazaran I clock 80 adanaka tun inada rai muyi celebrating" jiyayi zuciyarshi na tafarfasa hakan yasa shima yajuyo ya kalli baban yace "Dad football is my purpose, is what I want, and is wat I want to do, nifa bantaba gayamuku I want to become a king ba, Dad I am not interested in this king abubuwan nan dawanan bokan dakuke ijiyewa da sunan tuba, banso nika kyaleni kona tattara nabar muku gidan saikun ganni" tabe baki su Dami sukayi yanda Tobi kema iyayensu magana, su basu isa suyi hakaba, ga mamakinsu saisukaga cikeda lallashi Dad ya shafa kanshi yace "haba Tobi calm down ai ba fada mukeba, just take your time and think it through kaji, oya yanzu yi breakfast dinka" daure fuska yayi tamau saikawai yatashi yace "ni banmajin yunwan yanzu bari nai wanka saina dawo naci" tashi yayi yawuce yafita Baban nashi yabishi da kallo, ahankali Mum tace "Tobi is too stubborn horny but not to worry zanmai magana" gyadama Mum kai Dady yayi suka cigaba da breakfast".
Flat dinshi yawuce direct yabude yashiga yay stairs, bedroom dinshi yabude ahankali ya shiga har lokacin tana kwance tana bacci takara cukurkude bargon kaman yar mage kana ganinta kasan rabon datai bacci mai dadin nan ta manta, shida ranshi yake abace samin kanshi yayi da yin murmushi ganin yanda yaron ke baccin kaman mage yasami lallausan katifa, kaya yacire yakoma yasake wanka sanan yafito ya shirya cikin 3quater da black v neck t-shirt, yadauko MacBook dinshi hakanan yaji baison yabar yaron shikadai so yake ya kwanta and watch him harya tashi yaga reaction dinshi tunda yau bacci yazoyi ba aiki ba, yagama thought din wearing a smirk akan fuskanshi.
Hawa kan gadon yayi yana aiki da system dinshi....... wuraren shadaya da rabi tai wani irin juyi takife cikinta akan lallausan rug din tana murmushi ahankali cikin muryan bacci chan kasa tace "Habib ka kashe toculan nan" janye kanshi yayi dagakan system dan juyo da kanshi yayi ya zuba idanunshi akan yaron jin yay magana da muryan mace yakira Habib dawasu kalamai kumada yaren dabayaji wanda ya tabbatar da hausa ce dan yaran bahaushe ne ai, wani irin cute murmushi tayi cikin baccin daya bayyanar da kananun fararen hakoranta dakuma cute two sided dimples dinta, sanan ahankali tasake dan motsi sanan idanunta suka fara rawa budesu tayi ahankali saikuma tabude su tarrrr ido da ido sukayi da Tobi dake kwance kan gado, laptop nakan pilow akan cikinshi ya janye idanunshi dagakan laptop din yana kallonta gabaki daya, dawani irin sauri ta maida idanunta ta kulle gam tanaganin kaman amafarki taga prince din gidan nan na kallonta sanan ahankali ta shiga bude idanuwanta kaman wacce tai sata har lokacin tana akife tai rubda ciki sanan tabude idanun tatas tasake kallonshi ganin still shidinne dai tana kallonshi yana kallonta kurr yasa tawani fasa uban ihu da kuka duka alokaci daya danyau tai mugun laifi sanan ta shiga tashi da sauri jin abu mai shegen taushi kan jikinta yasa ta kalli abun ganin bargonshi nakan gadonshi dayake rufa dashi yasa tamugun fashe da kuka ta kalleshi still yana kallonta ko kyafta ido baiyi ba ta tashi sosai tana tattare bargon tai kneeling tahade hannayenta biyu duka tana kallon agogon bango ganin sha biyu saura yasa tafashe da mugun kuka tace "sir please please forgive me, please forgive me sir, I don't know how I slept off pls sir dan Allah kayafeni, kayakuri, Sir please don't ask those people to beat me, please I am so afraid of the cane, I promise to never sleep again, pls don't make them beat m.......e....." "go to Mum's flat and get me food I am damn starving" yay maganan ahankali yana mayarda kanshi yana resting akan filo ahankali, tsagaita kukan datakeyi tayi tadan kalleshi ganin yacigaba da abinda yakeyi yasa da sauri ta tashi, kinkiman bargon tayi tai hanyar fita waje dashi dan tabayar awanke harta bude kofa yace "where are you taking my duvet to Boy" da sauri tajuyo ta kalleshi hada ido sukayi ya zubamata mayun idanunshi da sauri ta saukar da idanunta kasa sanan ta taho ahankali ta ijiye agefen gadon tawuce tafita tana share fuskanta hankalinta na kwanciya ganin baimata fadaba towa ya lullubeta da bargo,shine? Ta tambayi kanta, samin kanta tayi da murmushi ahankali tace "yanada kirki, shikadai ne baitamin ihu ba, saidai bai kallon mutane yanada wulakanci kuma" tawuce tafita tajita garau ta watsake ashe tuntuni bacci ne ke neman kassarata.
Flat dinsu zata shiga guard suka tareta ahankali tace "Aremo sent me to collect his food" budemata kofa sukayi ta shiga, falon babu kowa aciki, saidai uban manya manyan hadaddun kulolin abinci akan dining, rasa mezatayi tayi saitahau ihu tana ."Ma Prince sent me" Dami na falon upstairs taja tsaki, tacigaba da chatting datake tana addu'a Allah yasa kar Mum taji balle ma tafito, yabata yakai kusan 10min yana Ma an aikoni, jin shiru yasa wata zuciyan tace takoma tacemai bataga kowaba wata xuciyarta tace mata tobaga abincin nan akan dinning ba ki deba ki kaimai yace yunwa yakeji, tunanin hakan yasa takarasa wajen dinning dudda gabanta nafaduwa zuciyanta na gayamata kul kul karkiyi, ki koma ki gayamishi bakiga kowaba amman takasa dinning din ta tsaya, tray mai kyau datagani awajen ta dauka ta ijiye, sanan tashiga bude kulolin abinci sunfi kala goma, babban plate tadauka ta debanmai jello rice dake kamshin abincin biki, sanan tadau wani bowl tazuba mai salad tadau cream tasa ta ijiye cream din kenan yafadi akasa karan dayayi yasa Dami ta sauke wayar datake tattabawa jin karan abu a downstairs.
Tsugunnawa tayi ta dauki bottle din ta maida inda yake ta ijiye, sanan tadau wani bowl tazubamai farfesun kan ragon datagani dayake tiriri tsabagen zafinshi, ta ijiye akan tray sanan tadau wani plate ta sakamai plantain da namomi soyayyu sanan ta ijiye shima kan tray, ta maida kulolin tarufe tass, sanan tadauki tray tafito daga dinning tafara tafiya hartakai tsakiyan dakin taji an daka mata tsawa. "You this stupid animal Boy!" Da sauri tajuyo jikinta yadan fara rawa ganin wanan yayan prince dince data radama suna mai masifa ce tanamata wani kallo kaman takama barauniya.
_MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number takira 07010439656 , sanan zaki samesu a watsapp ta wanan nUmber 08106788714 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._
_DISASTROUS LOVE_
Chapter 32 · 0% Book details