← Book details Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 97

Sashe 10

Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

M SHAKUR _Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._ _Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da sauran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128_ EPISODE 7 _FREE PAGE_ Toculan hannunshi ya kunna yana kallonta still, ahankali yabude bakinshi kaman wanda baiso yabude softly yace "stop crying" gyadamai fuskarta dake hannunshi tayi yana kallonta tahadiye kukan gabanta na faduwa sosai, haska duka idanunta biyu yayi sanan yasaki habarta yace "meke miki ciwo yanzu"? Kasa jure kallon dayake mata tayi tasake saukar da kanta kasa murya chan kasa tace "kaina" "damene kuma"? Dagokai tayi ta kallai saikuma tasake sauke kanta kasa takasa magana, karban folder hannun nurse din yayi sanan yace "raise her gown cover her legs with the bedsheet" sanan yajuya musu baya yana rubuce rubuce abinshi acikin folder ta. Fashewa tayi da kuka ganin yanda Nurse din ta kwaye mata riga ga namiji awurin, riganta har saman cikinta, saitaja bargon gadon tarufe mata cinyoyinta har zuwa kasan maranta, tundaga cikinta har maranta abude sanan tajuyo tace "angama Dr" ahankali yajuyo yamika mata folder yana kallon cikin nata dayay lakur kaman batacin abinci sai maranta dayadan kumburo, handglove yasaka sanan yakai hannunshi yataba maran yakalli fuskanta motsi yaga tayi tareda runtse udamunta gam alamun tanajin zafi, ahankali yace "zafi"? Murya chan ciki dake rawa sosai danduk a birkice take jin namiji nataba mata ciki tace "eh" dagowa yayi yadauki kwalaben allurai 3 dake tray injection da nurse din takawo ya fasa ya zuko alluran a syringe guda biyu da karami da babba sanan yadaga alluran sama yana saitawa kaman ance tabude idanunta tabude alluran data gani yasa tawani irin tsandara ihu. "Babaaaaa! Baba wlh naji sauki kazo mutafi gida ni kar amin allura" da sauri yajuyo ya kalleta kwaye zanin da aka lullube ta dashi tayi tawani zabura zata sauka hannu daya yasa yariketa dan faduwa zatayi tana tashi yamikama nurse din alluran, kokarin kwace kanta tayi tafashe da kuka sosai tace "wlh wlh naji sauki ku kiramin Baba mutafi Allah kuwan, inkanama Allah karkamin alluran nan dan Allah Doctor, dan Allah dan Allah" ayanda take kuka take rokonshi he could feel her fear tundaga heart dinta and is not a good condition ama patient allura haka, da hannu daya yariketa yakai hannunshi daya kan bakinshi yana kallonta yace "shiiiiiiii inbakiso namiki alluran kiyi shiru bake kadai bane a ward dinan ba am I clear"? Gyadamai kai tayi tana wani irin nishi tana neme nemen alluran taga batagani ba, hakanan saiyaji tana tunamai Rayyana haka take itama batason allura, juyawa yayi ruwan goran daya gani kan kantarsu yadauka yamika mata yace "sha ruwa and calm down" yabude mata goran tareda bata karba tayi takai baki tana kalle kalle kurba tayi kadan tabashi da idanu yama nurse alamu taje ta bayanta, ahankali yace "ya isheki"? Gyadamai kai tayi yace "to kwanta" yanda yake mata maganan sosoft ysata natsu, kwanciya tayi ahankali yaja zani yarufa mata kafa batare daya kalleta ba, hannunshi yamika ya karbi allura daya yace " ki kalli bakina kome nafadi kifadamin test zanmiki okay inaso nagane daga wani lobe ciwon kanki ke zuwa" gyadamai kai tayi, ahankali yake mata wasu alamu da baki yakai alluran yamata daya gabaki daya batasani ba dan haka Allah yayishi baida zafin hannu ko digi, yamata dayanma, murya chan kasa yace "mena fadi"? Ahankali tace "banjiba" murmushi nurse tayi tace "cewa yayi yagama miki alluran" tanuna mata empty syringe din, da sauri takalli syringe din saikuma ta kalleshi abinma mamaki yabata, danharara yasakin mata yace "katuwa mai tsoron allura" ahankali tasaki murmushi dan yanda yace katuwar was a bit funny, da sauri yadauke kai yakama hannunta yamaida mata da karin ruwan sanan yawuce yafita daga wajen aka yaye labulen nata ya shiga duba sauran patient din da Zeena bata dubaba tai shiru tana binshi da kallo tanajin ciwukan datakeji ajikinta na sauka kadan kadan tana mamakin inda Baba yaje saikuma tai tunani yatafi salla, juyowa Dr imam yayi yakalleta kaman ance ta kalli gadon dayake hada ido sukayi da saurinta ta dauke kai gabanta nafaduwa kawai saima ta lumshe ido. Wuraren 10:30 nadare yagama komi zai tafi, fitowa yayi rikeda jakan laptop dinshi a hannu, hanyar ward dinsu Fatima yayi, awajen kofan ward din ya tsaya yana kallon ciki batare dasun lurada shiba danbai bude kofaba, yanabi bed by bed yana kallo haryakai gadon Fatima, zaune ya ganta Baba yasa filo abayanta yana rike da plate da indomie keciki da soyayyan kwai yana ganin plate din yagane namai shayin gaban hospital dinsu ne, indomie Baba yadeba da cokali zaikai bakinta, makemai kafada tayi tadan turo baki idanunta dake cikeda ciwo sukadan juya ahankali tace "ni Baba nakoshi" da sauri Baba yace "yakuri ci wanan shine na karshe, aini bansan akwai ciwon dazakiyi ki tsani indomie kiba, oya ci ci ci Zara'una" yakai cokalin bakinta yana mata murmushi, washe cute white teeth dinta tayi zata bude baki tai magana Baba yasamata indomie aciki dariya tahauyi tana taunawa shima Baba yahau dariya yace "yaushe aka haifeki yarinya bagashinan kinci ba" batarai tayi tana taunawa saikuma tahau dariya ahankali dan bata da karfi. Ahankali yasaki dan murmushi yana kallonsu yana tunani who ever says money shine happiness karyane, happiness kauna ce, just look at this father and daughter gwanin ban sha'awa. Kaman ance Baba yajuyo yaga Dr Imam tsaye da hannu Dr Imam yamishi alamu dayazo batare da Fatima ta gansu ba, tashi yayi ya ijiye plate din yace "ina zuwa Zara'u" hanyar kofa Baba yayi hakan yasa ta kalli kofan hada ido sukayi da Dr Imam da sauri ta dauke kai, abakin kofa Baba yasameshi yabashi hannu suka fara tafiya sukai hanyar waje Dr yace "Baba daman i wanted to see you kafin natafi ne, akwai abinda nakeson na tambayeka" da sauri Baba yace "menene likita"? Dan jim yayi kaman wanda baison yin maganan saichan yace "Baba naga tabon duka, fresh shaidan bulala ajikin Zara'u, waye yamata wanan dukan Baba?" _Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._ _Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da sauran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128_ Shiru Baba yayi yakasa cewa komi yama kasa cigaba da tafiya hakan yasa shima Dr ya tsaya kaman mai nazarin shi saichan ya nisa yace "Baba shirun dakamin ya tabbatar da kasan wanda yamata dukan kenan wanda nina tabbata bakai bane, ayanda naga kakeson yarka nasan bakaine zaka mata wanan dukan ba, Baba yarinyar nan bama wanan dukan bane na farkon dukan da aka mata ba dan jikinta da tabo dayawa, koma waye ke dukanta Baba hakkinka ne amatsayin ka na mahaifinta ka kareta, ka tsareta, mace ce tanada rauni sosai, abu kankani zai iyasa rayuwar ya mace yabaci dan haka dole ka kula, idanma rashin ji take bada duka zaku gyarata ba ai" ahankali Baba yace "bantaba ganin salahar yarinya mai biyayya irin Fatima ba, ko kadan batada rashin ji sai dumbin biyayya da girmama nagaba da ita" Shiru Dr Imam yayi yana kallon Baba ahankali yace "mahaifiyarta ke dukanta"? Girgizamai kai Baba yayi yace "batada mahaifiya" shiru Dr yayi saima yakasa magana, ganin haka yasa Baba yace "ni fulanin Maiduguri ne, mahaifiyarta buzuwar Maiduguri ce amman dukanmu dagani har mahaifiyarta rainon kauyene muba yan burni bane, a kauye mukai aure muka kuma tare cikin dangi da yan uwa da abokan arziki harta haifamin diyata Fatiman nan dakake gani ayau, bazan manta ba, lokacin Fatima nayar shekara biyu da watanni zan fita kiwo da safe tahau kuka zata bini, haka takemin and muddin tabini tosaina siya mata plantain chips da ake saidawa a bakin gari nadawo da ita gida sanan zata barni nafita kiwo, haka na dauketa nace bari naje nasaimata wanan plantains chips dinan abakin express sabida tanason abin sosai, kauyenmu nakan express road ne na zuwa asalin cikin garin Maiduguri, kuma masu saidawa anan bakin titin kake ganinsu (hawkers) na dauketa namata makawuya da nufin innaje nasayo mata mukoma nafita kiwo, muna fita bakin titi nakira mai plantain zan siya mata, na karba daya nasa mata a hannu nasa hannu zan ciro kudi a aljihu nabashi bangama cirowa ba mukaji wani irin kara da girgizan kasa dabansan lokacin dana dauki Fatima data rusa ihuba na kankame ajikina, kafin kasani naga ana ihu ana gudu, ga hayaki wuta natashi daga cikin dajin dana fito...." yadanyi shiru tareda lumshe ido, yanda Baba yay shiru yasa yagane end of the story, ahankali cikin wata murya dazai nuna asalin damuwa yace "Allah ya jikansu" ajiyan zuciya Baba ya sauke yace "Ameen, hadadden bomb yan boko haram sukai amfani dashi suka tada kauyenmu tass wai warning sukama gwamnati, dagani sai Fatima muka rayu a kauyen mu gabaki daya dasu bomb din yatashi dan safiya ne basuriga sun fita ba, nida Fatima mun wahala aduniyar nan, neme neman aiki, kwadago, da leburanci shine yakawoni nan Kano, inda nasami wata baiwar Allah matar nada kirki sosai tabani machine ina express tana tayani rainon Fatima dan tanason Fatima sosai matar Fatima ke kirada Baaba, yaranta duk suna waje, da aikin danake nasamu nahadu da wata budurwa dake saida mana da abinci a tasharmu na yan achaba Rukkaya, naji ina sonta namata bayanin kaina tace taji tanaso na, nadauki Fatima na kaimata tanason Fatima sosai, Fatima na yar shekara biyar mukai aure, Hajiya tabamu yarmu tabarmin machine din cewa zasubar Kano, ranan Fatima tai kuka amman ta hakura, a kasan waje take zama bata cika dawowa Nigeria ba, amman duk intazo Fatima na zuwa wajenta" ahankali yace "step Mum din Fatima tamata dukan nan"? Gyadama Dr kai yayi ahankali saikuma yace "da farko dana aure Ruka tana bala'in son Fatima sosai, dayake bata haihu dawuri saida mukai kusan shekaru biyu Fatima na shekara bakwai ta haifi Habib to daganan kaman asiri son datake ma Fatima yakoma ki, kodan
Chapter 10 · 0% Book details