Sashe 17
Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bacci yay awon gaba da ita. ******** Wajajen takwas nasafe tafarka ahankali take bude idanunta saitaga kaman all that happen jiya amafarki ne Baba yay biyan bashi da ita xataje aikatau, tarr tabude idanun nata tana kara kallon inda take ganin tana cikin motar har lokacin yasa taga ba dream bane, ganin har lokacin suna cikin mota ana gudu yasa tafara mamakin ina zasu kafafunta taji sun mata tsami sosai cikin kambas din da suke ganin yanda taketa motsi da kafar tana yatsine fuska yasa yaron kusada ita yace "kacire takalmin kafafunka susha iska inba hakaba zasu fara maka ciwo" kallon yaron tayi yananan shima kaman ita baida jiki sosai shima kuma dan farine, dauke kai tayi tashiga cire kambas din yaron na kallonta fararen kafafunta taciro dasukadan kumbura yaron yace "jibi kafarka mai kyau kaman kafar mace"! Faduwa gabanta yayi da sauri ta maida kafar cikin takalmi, dariya yaron yayi yace "kunya kakeji akira kafarka irin na mace to kafarne ba kaushi gashi batada wani girma daga gani baka aiki agida daman gaka shagwababbe sai kiran Baba kake cikin dare dakana bacci" da sauri ta kallai, dariya yayi yace "sunana Anas Abdulmalik kaifa" ahankali batare data kalleshi ba tace "Khalid" murmushi Anas yayi yace "aiman kai dan fulanine ko dan wlh kanada kyau inda kai mace ce da anga rububi gurin maza" wani irin mugun harara tamai tace "kadenamin irin maganganun nan banso" da sauri Anas yace "kai wlh kacika masifa me awanan maganan, by the way naji kasan ina muke yanzu?" Girgiza maikai yayi tace "kaika sani"? Girgizamai kai shima yayi yace "bansani ba wlh ni bantaba zuwa nan arayuwata ba amman kuma kaman garin yarbawa muke sabida naga signboard dinsu anata rubutun yarbawa akai" shiru tayi saikuma ta kalli window tai shiru, ajiyan zuciya Anas yasauke yace "irin wajen nan yakamata mutun yasami aboki dan we are all on our own, zaka zama abokina Khalid" yanda yay maganan ahankali yasa tajuyo ta kallai shima ita yake kallo, dan murmushi yayi yace "tunda baka sona da aboki shikenan amman still zan bada labarin dake cimin zuciya, kasan menene wlh na tsani Abba na sosai, bansan ina zaniba kawai yazo yacemin nahada kayana ya kalli Maman mu yacemata zai turani biyan bashi, saida mukazo wajen nagane ashe kudin dayaci kwanakin baya yakaro aure duk kudin bashine saikace yabani anini aciki dazai kama yadauken yabiya bashin dani, aikin shekara biyu da rabi fa zanyi ni bana makaranta ni inachan wata duniyan ina aikatau Mama na kewana" duka maganganun nan dasuke ahankali suke babu mai jinsu, ganin yanda hawaye yataru a idanunshi sosai yasa yabata tausayi ahankali tace "kayakuri wata rana sai labari, duk abinda d'a zaima iyayenshi koda cutanshi sukayi bai fadiba watarana zaka gane hakan kayakuri kaji" ahankali ya goge fuskarshi da bayan hannu sanan yamata murmushi ya kalli window ganin signboard na WELCOME TO LAGOS yasa da sauri yamata pointing da hannu yace "Khalid kalla" da sauri Fatima tajuya zata kalla amman sun wuce bata ganiba tace "menene" da sauri yace "naga welcome to lagos muna Lagos" dasauri tace "Lagos, Lagos din dana sabaji ana kira" gyadamata kai yayi ajiyan zuciya ta sauke, Anas nata mata hira hakan yasa tadan saki jikinta dashi kadan, saikuma daga baya sukai shiru ganin sun shiga asalin cikin garin lagos ga titina manya dake daukan kusan motoci kusan biyar a jere, ga dogayen buildings, ga hayaniga, ga yellow danfo buses, sukahau wani titi dake kan ruwa, ga jiragen ruwa manya manya irin wanda take gani a films su titanic akan ruwa, ga boat na gudu, sunyi kusan 20min sunabin bridge din chan ta hango wani babban UBA bank building tacema Anas "kalli UBA bank, banki su Baba yanada account awajen har number account dinshi nasani" dariya Anas yayi, garin yazamema yaran abin kallo securities duk suna jinsu sai murmushi kawai suke, sanan suka shigo wani hadaden kayataccen anguwa dake dauke dawani dankareren babban gida dagawani dankareren statue din mutum akofar gidan tsaye rikeda sandar girma, gaban gidan anyi wasu rubutu manya an rubuta ILE OTUN OBA LAGOS (GIDAN WAZIRIN SARKIN LAGOS). _MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number takira 07010439656 , sanan zaki samesu a watsapp ta wanan number 08106788714 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._ _DISASTROUS LOVE_ _MASIFAFFIYAR KAUNA_ EPISODE 1 _FREE PAGE_ Suna zuwa katafaren gate din mai kama da madubi wani babban mopol din yabude musu gate suka shiga cikin gidan, itadai tunda take arayuwanta na duniyan nan bata taba ganin hadadden gida hakaba, wani irin babban gidane naban mamaki, asalin mansion din dake compound din taga sun wuce suyi kasa nan ma wani dankareren gate ne aka bude musu suka shiga, wani babban gidane dabaikai wanchan kyau ba ga yara da sunkai su 60 suma maza a compound din suna zazzaune wasu nawasa wasuna hira, parking motar sukayi, securities dinne suka fara saukowa sanan sukace su sauko, ahankali suke saukowa aka nuna musu wani babban Palo mai kama da hall suka shiga sukai layi atsaitsaye, sanan sega wani sabon mutumi yazo da turencin shi dabata da kyau kana ganinshi kasan bayerabe ne yanuna musu toilets dasuke ajere guda 10 yace "go bath get ready" hanyan bayi sukayi, kusan 4 to 5 mutane abayi daya, tsayawa tayi tana kallo ganin anshigo da ganamasgon ta yasa tai wajen jakan security dayakawo yace "mezakayi"? Bakinta har rawa yake ganin yanda ya murtuke fuska sabida tsoro tace kayan dazan sa zan dauka, hararanta yayi yawuce yafita ahankali tabude jakan tadauko wani wando da riga, bakin wando ne shima sai bakar riga t-shirt mai zanen Paris aciki sanan ta tashi, tana ganin wani yafito daga bayi tawuce ta shiga da sauri kafin wasu set subiyota ta kullo kofa tareda saka sakata da key duka, yanda bayin ke warin jikin mazane yasa ta taushe hancinta takai kusan 1min atsaye sanan tabude boturin riganta tacie rigan tacire singlet dinma kafin ahankali ta kwance daurin silkin kirjinta, dawani irin sauri ta tsugunna tareda rike boobs dinta sabida wani mahaukacin azaban ciwo dasuke mata tadade ahaka sanan ta tashi tacire wandon ta madubi ta kalli boobs dinta sunyi jajir abunku da fara da kyar tacire wando sanan tai wanka agurguje ta shirya tsaf bayan tasake kulle kirjinta da silkin, bakaken kayan data saka sun mata kyau bakadan ba, kallon kanta tasakeyi amadubi ahankali tadaura hannunta kan saikon fatar kanta tana kallon kanta wai yanzu itace wanan, wani irin mugun tausayi tabama kanta saikuma tafashe da kuka ahankali Allah kadai yasa irin tsoron datakeji azuciyanta wani irin bubbuga kofan bayin da akayi yasa afirgice tajuyo cikin ihu security guard yace "ubanwa yace maka ana rufe bayi kai kadai ke jiran bayin bude kofarnan" da dauri ta tattare kayan data cire tarike a hannu sanan tabude kofan daya daga cikin security ne tagani tsaye gaban bayin ga yara tsaye abayanshi duk sunaso suyi wanka, cikin fushi yakai hannu zai watsamata mari da gudu ta tsugunna wani daga cikin security yarikemai hannu yace "kayakuri mana he's just a boy, baku fadamusu ga yanda ake yi ba" cikin fushi shima yace "just 30min fa aka bamu musasu su shirya su fito ya shiga bayi shi kadai ya kulle ga mutane dayawa nan basu yi wankan ba abinda mutum biyu ko uku yakamata su shiga at once" dayan security dake bashi hakuri ne ya kalli Fatima da jikinta ke rawa sosai tana tsugunne kanta akasa yace "kaikuma tashi kaje ka maida kayan daka cire jakanka kadau jakan ka maida mota sanan ka shiga cikin assembly dakukeyi awaje" tashi tayi da sauri tana goge hawayen dasuka zubo mata, wajen gana masgonta tayi tasaka kayan sanan taciro kiton da Mama ta saimata baki shima ta saka ta manna igiyan dan kafarta yagaji da kambas din jiya tasaka kambas ajakan sanan tadau ganamasgon ahankali tafita har lokacin jikinta rawa yake, wajen motarsu tayi ta shiga ta ijiye jakan sanan tafito tana kalle kalle bataga yaro ko dayaba sanan bataga inda ake assembly ba hakan yasa ta tsaya tana kalle kalle, tana cikin kalle kalle kaman daga sama taji anwani irin zubamata dorina wani irin ihu tayi da mugun kuka arude tajuyo tana kuka sosai jikinta narawa tana kallon mutumin daya zuba mata wata muguwan sharbebiyan dorina dake hannunshi da tsayinta yafi tsawon mutum. Cikin harshen turenci yace "angayamaka uban gidana uban kowa najiran mutane ne ance kaje assembly ka tsaya anan kai wayekai" yasake daga nabiyun zai shaula mata da gudu tashiga mota tana kuka sosai hartana fadi har lokacin tana sosa bayanta kaman wacce ta zare bulalan gawani mahaukacin zafi sanan ga mugun kaikayi, zai shigo motar kenan security daya ceceta dazu taga yazo harda dan gudunshi yama mutumin magana mutumin yajuya yatafi yana masifa, shigowa cikin motar yayi yana kallon yanda take kuka da hausa yace "wai ka dauka har yanzu a garinku kano kake ne? Idan baka natsu kasan mekake ba duka zaka dinga ci agidan nan harsai kadawo abin tausayi ba assembly nace kaje ba" cikin kuka sosai tana soshe soshe tace "ai ban gansu ba sunake nema" hannu yamika mata alamun tashi, tashi tayi ahankali batare data rikeshiba har lokacin tana kuka, hannunta yakama yajata suka fita daga motan tana kuka sosai sanan yay gate da ita, bude gate din yayi daya sadasu da mansion din dasuka fara wucewa kafin su shigo nan, nan taga yara dayawa basu kadai bama harda wasu another set