Sashe 72
Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
kina mace kwallo kike kallo a TV sabida kin rasa film, nidai sakamin kwana chasa'in" haka zata chanza, tunani kala kala da kuka ahaka tai bacci. Dasafe shine yatadata still tatashi tai salla tai addu'a tafito ta gyara gidan ta kunna turare sanan tahada kari, saida tagama komi sanan tawuce dakinta tai wanka tafito tazauna tashafa sabon man da Mum tasiya mata daya karbi fatar jikinta sosai, sanan tasaka kwalli dayama idanunta kyau, tadauko wani riga da skirt na vlisco atampa da takalmin shi da gyale dan haka Mum tahada mata kayan, atamfan bakine da ruwan toka, hakan yasa gyalen yazamto mai ruwan toka sanan tadan fesa turare bodyspray kadai tafito, dayake Granny ne kadai da Amna yasa Granny tace "kallabin fa" zama tayi tace "idan zamu tafi saina daura" Granny tace "ni banjin zan bikuba fa sonake nai bacci nahuta anjima saina biku mu kaiki makaranta" gyadamata kai tayi, suka gama breakfast ta kwasa takai kitchen Granny tace "karki wanke wanken nan zata aiko yar aiki ta wanke kuku wuce ku tafi, Maman ku ta shirya, jeki dauro dan kwalin kidauko jaka kifoto" daki tawuce ta tsaya gaban mirror ta daura dan kwalin da kyar sanan tadau gyalen tayafa tanajin wani iri bata sababa sanan tasaka takalminta mai kyau flat tadauki jakan tasaka wayanta aciki tafito, tai wani irin kyau kaman diyar shugaba Buhari, hannunta Amna tarike tace "kinyi kyau Ya Zara muje Mum na mota" bye sukama Granny databisu da kallo tace "adawo lpy" sanan suka fice. Girgiza kai Granny tayi tace "Muhammadu dakasan meka haifa dabaka wulakanta yarinyar nanba, jibi yarinya yanda Allah yamata baiwan kyau ita kadai, yanzu datasami hutu da kwanciyan hankali cikin sati kawai jibi yanda asalin kyanta da hallitun jikinta kefitowa, wlh zakasan ka wahalar da yarinyar nan" tai kwafa ta tashi takoma kan doguwan kujera ta mikarda kafa tana chanza tasha. Saloon Mum takaisu aka tsefe musu kai aka wanke sanan Mum tasa aka mata kalaba hadaddu kanana, itakuma Amna tasa aka mata normal kitso, tana zaune tana jiransu tana karanta news paper amman kallon Zara kawai take datai wani irin kyau da aka kusa gamama kitso yarinya ga gashi, saida aka gamamata sanan tasa aka musu gyaran kumbuna sukai kyau, tabiya kudi suka fito tasakasu amota sanan suka dawo gida. Agurguje Mama tasa suje su sake wanka dan Dad yakira yacemata su shirya gashinan zuwa sanan suka wuce, kallon kitsonsu Kaka tafarayi sunyi kyau sosai sanan tace "to kuje ku shirya" sanan mai gadi ya shigo yashiga fitarda kayayyakin zuwa school dinta. Wani simple material tasaka wanan karan milk mai flowers red, ga red veil dayamata kyau sanan tajanyo akwatin ta daya Amna ya janyo nabiyun Granny datai shiga ta alfarma na ganinsu tace "iyye student" sanan ta kalli Amna tace "kai kwatinki waje kizo kidau dayan zonan Zara" ahankali tazo Granny tanuna mata waje akasa hakan yasa tazauna itama tazauna tace "Fatima Zara'u kinga makaranta zaki yanzu, bawai kaman secondary school yakeba, zaki hadu da mutane kala kala, iri iri banson ki bata wanan kakkywan tarbiyan naki, babu ruwanki da maza, komeke damunki kome kikagani kinaso ki sanardani mu zamu miki, kwadayi kesa yaran yanzu bin maza dan samin abinda basuda shi, daidai da magi idan naki yakare ban yarda ki karbi nakowa ba kifita ki sayo a shagon hostel kokuma ki kira mu aiko direba yakawo miki, saikuma last fadan daza miki banson yawan surutu, ba ruwanki da gulma, da labarai da sauransu kinajina ko" ta gyadama Granny kai, sanan Granny tace "kidinga kulle kanki kullum yanda kiked gashin nan hostel akwai aljanu ki tsare kanki da azkar da komi, nagode ma Allah ma dayasa two people per room ne hostel dinku so kinada roommate banda fada, zaman mutunci da amana, kidinga girkin ki banda yawan zuwa kanti kinji" ahankali tace "naji Granny, nagode" "tashi to mutafi" tashi tayi taji duk jikinta yamata sanyi, suka wuce da manyan motoci biyu suka tafi sabifa kayanta su suna cikin motar Dady direba kuma ya kwaso kayanta, har zuwa makarantan su. Makarantan yahadu sosai bana wasaba abunka da private school, shiga makarantan sukayi suka cigaba da tafiya akan shimfidadden titi har zuwa girls hotel sanan yay parking awaje, security dake tsaron wajen suka fito, takardan room number da aka mata allocating Dady yabama head security na mata ta karba tana dubawa sanan, tace "okay, muje" bayan sauran securities din sun tayata kwasan kayanta, Mum da Granny da Amna dakuma ita suka bisu ciki dan men are not allowed, hostel din yahadu sosai ko'ina kal kal wuta ba'a dauke musu, block C suka kaisu room 8, wanda yake akan bene sanan security tabuga kofa tareda budewa wata yarinya ce zaune akan gadonta tana sanye da doguwan riga tana rubutu ganin mutane yasa ta tashi tareda gaidasu, security tace "munkawo miki roommate" tanuna Zara, murmushi yarinyar tayi tace "welcome" sanan tanuna musu bangaren Fatima dake left, ga wardrobe dinta, na zuba kaya, ga kitchen dinta dan karami, dakin nada girma ga AC ga bayin su aciki, jera mata kayan ta Granny da Mum suka shiga yi, within one hour sungama gyara komi nata sun shinfida mata katfarta da zanin gado, sun jeramata kayan abincinta dakomi akitchen dinta ga corn flex nadara milo dakomi saikuma snacks dinta suka saka mata a wardrobe kafin six sungama komi sanan sukace to saitafiya, waje sukayi tabisu saida taga dagaske tafiya zatayi tafashe da kuka saikuma sukahau mata dariya danharshi Dad dabaida magana sosai saida yay dariya, yafito da kudi 50k yabata yace "gashi kirike wanan" karba tayi tace "Dady Allah amfana amma dan Allah kabarmin Amna tadinga zama anan" tasake fashewa da kuka dan dagaske take fa, fitowa Mum tayi daga mota tace "kinga sai kallonki ake kina kuka akan hanya, Amna can't stay with you a hostel itama tana zuwa school dinta, keda just on Friday zaki dawo common zaki ganta zaki ganmu stop crying now, wuce kitafi, bye" hannu tadagama Granny dake cikin mota da Amna itama tana kuka sanan tajuya ta tafi ciki tana kuka tana share kwallan, sukuma suka tafi cikeda kewanta. _Mumies akwai abinda nakeso nagaya muku, shin kunkosan like Did you know........?_ _Scent kamshi shine abu na farko da mutane ke lurada shi idan sun shiga gidan ka ko motan ka bawani abuba?_ _Be memorable.....in a good way Mumies_ _A Fragrant, shi kamshi is like a signature, kaman wani alamune so even after a woman leaves the room, her fragrance should reveal she's been there. Kamshi abune dake nuna kinzo waje idan ma kikabar wajen still zai nuna kinzo_ _Turare heralds a woman's arrival and prolongs her departure_ _The beauty of turare speaks to your heart and hopefully someone else's kunsan da haka Mumies?_ _Kamshi is a word, turare is a literature do you believe this Mumies?_ _Kamshinki amatsayin ki na y'a mace tells more about you sama da handwriting dinki kinsan da hakan?_ _Mata kusaurara kuji, namiji yana iya manta komi naki amman baya iya manta kamshin ki_ _da hakane nake muku introducing turarukan UMMIE COLLECTION dazai baki duka qualities dinan and even MORE tested by M SHAKUR dinku, suna saida turarukan daki, na jiki, na wanka, turarukan tsinke, body oils da sauran su, zaki iya tuntubar su ta wanan number ko awaya ko a watsapp 08186968736, dan samin karin bayani, zaku iyashiga group dinsu dan ganin duka turarukansu, zakuma ku iya following nasu a_ Instagram @UMMIE COLLECTION. Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/Fov2UbNr4CH0reP9K9zltu Instagram Handle dinsu https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1c3np4d6vwqbv&utm_content=1g4qyjp _PRODUCT DINSU_ _SANDAL EXCLUSIVE_ _SANDAL FLAKES_ _SANDAL BANGI_ _KAJIJI_ _DOROT_ _DAMBU_ _DEVINE (PURPLE)_ _REGAL (YELLOW) _LOVELY (MAROON)_ _DAISY (ORANGES)_ _KHuMRA_ _STAR_ _BELOVED_ _Body oils._ SIGN M SHAKUR _DISASTROUS LOVE_