Sashe 67
Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
M SHAKUR EPISODE 5 & 5 Parking yayi Abba shiya fara futowa yabudema Granny dake kuka har lokacin kofa yace "Hajiya dan Allah kiyakuri kidena kuka kinga bawani lafiya ce ta isheki ba" yay maganan yana fitoda ita daga mota sukai cikin gida, Ammi dake kokarin saita dinning ne ta tsaya chak ganin an shigo da Granny tana kuka dasauri ta taho takalli Abba tace "Hubby maiya sami Mama kuma take kuka"? Kafin Abba yabada amsa cikin kuka sosai Granny tace "barni kawai yau naga abinda tsawon rayuwata ban taba ganiba, tayaya zaka wulakanta yar karaman yarka? Meta maka? Wani laifi tamaka? Tanada wani mummunan haline? Ka wulakanta yarinya kamaida yarinya namiji, ta wahala, jibi yanda sauro dawata tsiyace duksun cinyeta amman mutumin nan ko'ajikinshi wai bayarshi bace idan mukama kawota saiya nakasata sanan yakorata, duniya ina zaki damu? Talauci nataba ma mutum kwakwalwane wai? Wlh wanan abun yay min ciwo sosai kinji Maman su Imamu, yarinyarnan tabani tausayi matuka" takara fashewa da kuka, bude kofa Imam yayi yashigo kaman ance yadaga kanshi ya shigo Fatima yagani aduke ta tsugunna akan stairs dinsu tadaura kanta akan cinyarta ga cup din tea agefe yasa yamaida kofar yarufe yay stairs da sauri hakan yasa duk suka kalli stairs din, ganinta yasa Granny tasake rushewa da kuka tayi stairs din itama daidai yakai gabanta tsugunnawa yayi ahankali agabanta yakira sunanta. "Fatima" dasauri Ammi data biyo bayan Granny tace "naga ruwan daka samata yakare nacire nasagale, nace metake sha'awaan ci tacemn tea, shine nabata nace bari nazo kitchen ina girki ne, halan tagaji da kwanciya ne tafito" ahankali Granny takai hannunta tadago kanta dagakan kafarta tace "Fatima" dagota sukayi sukaga fuskarta ko kadan babu hawaye ammam the kind emotions dakuma yanayi dake cikinshi zai iya saka kafashe da kuka, gyara zama Granny tayi tazauna kan stairs din sanan takai hannayenta biyu ta tallabo fuskar Fatima tace "Faty Zara na, nasan duk abinda muke cewa kinji amman inaso kisani mudin nan saimunfi miki iyayenki, tun kina karama naroki mahaifinki yabani ke yaki da dake zan tafi UK abina, ki dauki wanan rayuwan da wahalan dakikasha abaya as kaddara, ki manta dakomi ki manta da kowa na daki ada, saisama zan bar kanon dake Abuja zamu koma kifara karatu kinji, I will be your father and your Mother kinji, I gotcha Zara" sai alokacin tadaga idanunta takalli Granny ashanye sabida kalman datafadi na karshe wanda prince ne kadai yatab fadamata wanan kalman, hawaye taji yazubo mata dasauri takai hannu zata goge hawayen Granny tarike hannunta tace "no no no, yi kuka Zara, ki fitarda duka abinda ke ranki ayau dinan dam daga gobe sabuwar rayuwace, cry kinji kin cutu sosai" kaman jira take tawani irin fashe da kuka sosai tafad jikin Granny ta kankameta tace "Baaaabaaaaaaa, Baaaba nagaji dakomi kaman na mutu nahuta kawai nakeji" da sauri Ammi tajuya jin hawaye yazomata Baba kawai ya girgiza kai yabi Ammi zuwa kitchen din dayaga tashiga dan yasan kuka zataje tayi dan kowa yaji rayuwan da Fatima tayi dakuma abinda mahaifinta yamata xaisa kaji kana tausayin yarinyar, tayi kuka iya kuka sanan Granny tasamu tai shiru, tagoge mata hawayen tass tace "no more cry" sanan takalli Dr Imam dake gefenta yace "kadauki ATM card ajakana kaje kasamo mata cream dazaisa wanan kurajen da cizon sauran kona menene ma dake jikinta yabace pls" sanan ta kalli Fatima tace "muje kiyi wanka" tadagata sua wuce ciki yabisu da kallo kafin ahankali yatashi yawuce yafita. Haka ranan tawuni babu wani zazzabi kodaya ajikinta kawaidai kana ganinta kasan she is not happy, batada magana su Rahma sun shigo sun jajjatada hira amman shiru, Granny ne kawai kesata tai magan tayi ko Dr Imam batamai magana sai ido, abinci ma taci ba laifi, gabaki dayansu sunawani irin jida ita kaman sun sami kwai. Da daddare Lawyer Abba yazo yakawomai documents din da Baba yay signing kan ba yarshi bace sanan yakawomao credentials din yarinyar dayasa lawyer ya amsa wajen Baba dan dasu Ibrahima zai nema mata makaranta. WASHEGARI!! Tunda sassafe aka fara musu girke girke ana loda kayan Granny a mota dan da motan gida za'a kaisu sudai suna kasa yaran na sama wai acewansu zasu taya new kawarsu Fatima shiryawa. Dudda yadda take bai hanata tai mugun kyau ba, wata doguwar bakan riga sabuwa Ammi takawo mata datajw Umra tasayo, sanan suka sakamata kwalli a ido dan idanunta sun kore dayawa, saikuma suka samata ban baki akan lips dnta daya bushe sosai sai abin yayi kaman tashafa jan baki, murmushi Rayyana tayi tace "kinga yanda kikai kyau kuwa, banson ina zuwa hutu gidan Baffa sabida yacika fada amman yanzu sabida je zan dinga zuwa I promise" gyadamata kai Fatima tayi, Rahma tace "kunji Granny na kwala mana kira muje" ahankali ta tashi dagakan kujeran tayi kyau sosai Rahma tabude kofa Ya Imam suka gani agaban dakin, yau yana sanye da kananan kaya, farin riga dakuma jean dogo baki idanunshi sanyeda fararen glass ganinshi yasa da sauri kannen nashi suka wuce itakuma takasa tafiya ta tsaya chak kanta akasa tana wasada yatsunta, ahankali yashigo dakin yamaida kofan yarufe tareda jingina da kofan yay folding hands dinshi akirji sanan murya chan kasa yace "Fatima" kasa amsawa tayi hakama takasa dagokai ta kalleshi, fuzarda iska yayi ahankali yace "take care of yourself idan kinje Abuja, be serious with school, I will try na karbi transfer zuwa Abujan idan ban samuba zan dinga zuwa weekend, forget everything about your past and move on kinji" gyadamai kai tayi ahankali batare data kalleshi ba, dan jim yayi sanan yatako ahankali yazo gabanta ya tsaya still kasa dagokanta tayi but you could see yanda gabanta kefaduwa, hannunta yakama ahankali sanan yasaka mata ledan sabuwan wayan da yanzun nan dawowanshi kenan daga zuwa siyomata yace "be using this phone, u will need it idan kika fara school sabida assignment and the rest, Allah kiyaye hanya" yana maganan yajuya yafice daga dakin dasauri. Tadade tsaye awajen kafin ahankali takalli ledan wayan hannunta, ita kanta batajin dadin kanta she just loose interest in anything and everything, jin Granny ta kwalamata kira yas tabude kofan ahankali tafito ta shiga saukowa kasa Granny na kallonta tace "Ammin su Imamu zokiga yar wajena yanda tai kyau" dariya Ammi tayi tace "ahhh lallai tawajenki kam tahadu wlh" shide Abba dake zaune afalo murmushi take, da sauri Rahma tace "Granny kinga ninefa na shiryata" dasauri Rayyana tace "its a lie, nine wlh Granny" duk dariya akayi saida tazo wajen Granny sanan tace "gani Baaba" murmushi tamata tace "jekima Abba da Ammi sallama" har wajen kujeran da Abba kekai Mama nazubamai ruwan lip tea akai taje, ta tsugunna har kasa tace "Abba zamu tafi, Ammi, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi" kanta Abba yashafa yace "Allah yamiki albarka Fatima Zara" Ammi tace "Allah yakiyaye hanya daughter zamu dinga waya kinji, tashi abinki" tashi tayi ahankali Granny na murmushi tace "to saduwan alheri" rungumeta su Rahma sukayi tabasu kudi sosai sanan duk aka rakosu har mota, shiga motan sukayi, Granny tace "tundashi miskilin vazai iya fitowa yamin addu'a ba acemai natafi" duk dariya akayi Ammi tace "hospital fa yacemiki xai tafi dazun nan daya sakko kasa" dan ware ido tayi tace hakane fa sanan suka shiga musu bye su Rahma na suna hutu zasu taho Abujan, har suka fit daga gidan. Sundanyi nisa sanan tadauki ledan wayan tabama Granny ahankali tace "Baaba Ya Imam yabani" dasauri takarba tace "masha Allah menene aledan" tai maganan tana cirowa daga kwalin Samsung wayace mai kyau A72 sabuwa gal, murmushi Granny tayi tana bata back tace "iyye Yaya Imamu yasaima y'ata waya, to akashe lafia enjoy your phone, bansan ko kadan ina ganin damuwa kan fuskarki kinji" tai maganan tana kamo kanta tareda daurawa kan cinyanta tace "kwanta" kwanciya tayi ahankali, Granny tashiga shafa kanta tace "zan rikeki amana Fatima, nine mamanki nine babanki, banson komi kina boyemin kome kikeso komeyake damunki kidinga fadamin, I mean komenene kinji, banson ina ganinki so sad, kinga inda zamu gidan Ibrahima ne matarshi nada kirki sosai kuma tanama fita aikin ta, shi datake rikakken dan bokone yara biyu kacal ya haifa, first yaronshi is just 15yrs old yanama boarding house, SS2 yake, sai yarshi tabiyu tanada 7yrs Amna ita kuma tana primary six ta iya surutu, so you will not have any problem with them, idan mukaje ma bakison gidan inada my own personal house dina saimu koma, dama Doctors ne suka hana ina zama nikadai sabida ciwukana, ga diabetes, ga hawan jini, gakuma asma, saisa nake zama da yarana but yanzu ma naji sauki sosai Dr's din UK na sun iya aiki I hardly have attack yanzu, so I want you to be happy, idan kina murna nima I will be fine hankalina ya kwanta nasan cewa ban tauyeki dakomiba, muna kaiwa zankira telana adinko miki kayayyaki kala kala, zamu fita shopping, muje dunes kisai jakunkuna da takalma da gyaluluwa sabida ki shirya fara school kema ki shiga cikin yaran manya ki more yanmatakan ki kaman kowace yarinya of your age kinji" gyadama Granny kai tayi ahankali, fuskanta Granny tashafa tace "to yimin murmushi mana Zara na" batason matan tadamu hakan yasa tamata murmushi bako karamin Dady Granny tajiba haka tadinga mata hira har bacci ya kwasheta Granny na shafa kanta tana kallon fatarta tace "suna isa kaduna zata mata order su scrub glow oil dasauran kayayyakin Glow & Go naturals, sabida hasken fatarnan nata dayadan dishi yafito tadawo da kyanta gashinta zatakaita saloon gobe awanke ayaryada mata kitso, zata gyara yarinyar nan this is just her promise zata zuba kudi ajikin yarinyar nan zasuga yanda yarinyar nan zata dawo, saima tafara makaranta tafara ganin yanda sa'onninta ke gayu sosai zata kara kilewa ne. Saida suka shiga Abuja sanan Granny ta tadata tace "tashi ki kalli Abuja" tashi tayi tajuya tana kallon waje ta glass harsukakai wani anguwa locust agaban wani dankareren gida dayamafi nasu Imamu girma taga sunyi horn, aduka yaranta Baban su Imam Dr nema wanda baida kudi sosai dudda yanama mallakin private asibitin kanshi, gateman taga yafito yana ganin Granny yakoma ciki dagudu yabude kofa suka shiga cikin katafaren gidan, daidai anbude kofan flat wata cute yarinya fara sol tafito tana sanye da short gown nayara, hannunta rike da sweet mai tsinke