Sashe 14
Disastrous Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
M SHAKUR _MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number takira 07010439656 , sanan zaki samesu a watsapp ta wanan number 08106788714 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._ EPISODE _FREE PAGE_ Dawani irin sauri Baba ya kalleta yanda gabanshi yafadi har ita saida tagani, itama kureshi tai da ido kur tayi irin da magana ne amman yakasa furta uppan saima ya sunnar da kanshi kasa, wani takadirin murmushi tayi tace "aina zaci zakace wani abune" tadanyi shiru tace "Fatima itace yarinya babban damukeda shi maidan hankali kuma yarinyar nan zata iya komi tarufa maka asiri, ta mallaki hankalin kanta shekaranta sha tara duk inda muka kaita hankalinmu akwance sabida musan zata kare kanta" ahankali kaman wanda ke tsoron magana yace "Ruka mutanen nan kin manta sharadinne yaro namiji kadai suke karba basu karban mace" dan dariya tayi tace "ance maka ni dakikiyace irinka hmmmm" tadan girgixa kai sanan tace "inada plan, hadaddiyar plan" ahankali bakinshi har rawa yake yace "wani irin plan?" Murmushi tayi tace "zamu komar da ita namijii"!!!! Zuru zuru yayi yana kallonta kaman sauna ta gyadamai kai tace "zamu komarda ita namiji ta hanyar boye duka hallitun mace da Allah yamata Madam cema tabani shawaran nan dan itama tasan Habib yay karami ga Habib ba wayau, inada wasu kudi dubu goma zan ara maka gobe zan shiga kasuwa, zan sayo silkin doki dashi zamu kulle mata kirji wanan manyan maman datake dashi dauresu zamuyi tamau, kanta ko nida kaina yauzan zauna namata zane yan kanana zan sayo Bald cap (hulan fata na kwaiwaido) zan zauna nasaka matashi da gam, sanan zan sayo kayan maza riguma da wando na gwanjo burguza burguza dakuma Ghana masgo, hujin kunenta akwai wata yar fata dazan like awajen baza'a taba gane antaba huji awajenba saikuma takalmi kito, da kambas, wanan maganan dagani sai kai da madam da mijinta, duk wanda yatambayi Faty zakace tayi tafiya ta tafi wajen Baabarta na Abuja hatta su Habib bazasu sani ba kanajina" gyadamata kai yayi kaman maraya, hararan shi tayi tace "duk duniyan nan bakada mace mai sonka maikuma rufamaka asiri irina dan haka kadinga godemin, kuma bayau zaka sanarda Fatima ba sai gobe sanan agabana za'ai komi kanajina ko" gyadamata kai yasakeyi kaman maraya yakasa magana yakuma rasa abinda yasa yakasa magana, murmushi tayi har cikin ranta ganin yanda maganin sabon wajen da Madam ta kaita yay aiki sama dana tsohon datake amfani dashi da, murmushi tayi tabudemai hannayenta tace "zonan mijina" da saurinshi da rarrafe yashiga jikinta ta rungumeshi tana shafamai baya tace "inhar kanajin maganata kanamin biyayya bakada matsala wlh, komenene zan tsayamaka aduniyan nan, duk rashin kudinka ina sonka, ni bankibama kai zamanka agidaba nina dinga fita nema dan wlh banson mata na kallemin kai kafin wata ta kyatsa amin wuff dakai dole na tsaya tsayin daka aranka, dan kyakkyawan bafulatanina" ta shiga sarrafa shi wai ance duk wayan namiji yashiga hannun mace jariri yake dawowa, shida kecikin damuwa dayake rikakkiyar yar tasha ya aura tuni ta mantar dashi tana tsotse shi saigashi yafara ihu suka shiga cin juna yau harda ihauce ihauce barinma shi dayajita yau daban saida ta taushemI baki sabida ihun yasoma yawa sai sama Madam albarka take yanda taga lokaci daya Baban Habib ya susuce mata ba ita tabarshi ba sai wuraren karfe biyar daga ita harshi sun galabaita da kyar ta sauka ta zura hijabi tayi tsakar gida tana taku dai dai madam tafito yar gatan mijinta tawuce takaimai ruwa bayi sukuma suna gulman su Kullum yana gindin mace an maidashi sauna sai yanda akai dashi. ********* "Kewai mesa yar kauyece Zara"? Cewan Maryam da tundazu suke hira da Zara datazo tana bata labarin rashin lafiyan datayi just this two days, Abida kuma nachan dakin Maman su Maryam tanacin tuwon da aka dafa tana wasa. Hararanta Fatima tayi tace "ni wlh ko kallonshi nayi sai gabana yayta faduwa" wani irin dariya Maryam tashigayi tafada kan yar yaloluwan katifarta tana daga kafa, daure fuska Fatima tayi tace "me haka wanan dariyan fa"? Da sauri Maryam ta tashi ta zauna tace "ke wlh sonshi kike" da sauri Fatima ta zaro idanu cikeda wani irin mugun mamaki gyadamata kai Maryam tayi cikeda jinjinawa tace "eh ke matsalata dake baki karance karancen littatafan soyayyane dakin gane menake fadi, kinsan ko ance duk namijin dazaka gani gabanka yayta fadi shine zaka aura ko shine mijinka" wani irin kallonta Fatima take kaman tasami TV, Maryam tace "kuma shima wlh sonki yake, har yana barin aikin dayakeyi yazo yatareki dankarki fadi kice kaza kaza, ina gayamiki sonki yake kawai dai bai sami ta hanyar dazai fadimiki baneba kawai, kuma zakigani nan....." da sauri Fatima ta tareta tace "ni mubar maganan dan Allah banmaso wlh meneke dashi da irin wanan mutumin zaiso mace kaman ni ke kinganshi ne kuwa? Hanyar jirgi daban hanyar mota ma daban abar maganan" tashi Maryam tayi tace "anbarta bari naje na dauro alwala nai salla gwara ke aurenki da gata for now Allah ya yafemiki" murmushi tayi saikuma tamata gwalo irineh din jedai kiyi, Maryam tafice daga dakin tana dariya tace "dadin abin nimadai nakusan zuwa nawa hutun sallan" samin kanta tayi da tunanin maganganun Maryam saikuma tai maza ta kawarda zancen daga zuciyanta, ranan wuni tayi tareda Maryam har Magrib itama Abida batai kukaba dan tasami tuwo taci takoshi tai nak sai wasa take abinta sunama Maman su Maryam barna adaki itada kannin Maryam, koda takoma gida taga Baba na nan baifita ba suna hira shida Mama ta gaidasu Mama ta dauki Abida itakuma tawuce daki. Washegari Asabar batabar Baba yaje ko'ina ba bamata barshi ya zauna shi kadaiba sabida batason yay tunanin abin, sai wajajen 9 nasafe suka fita ita dashi sukai kasuwa tare suka sayo kayan gwanjo riguna masu kyau kala biyar dogayen wanduna jean burguza burguza kala biyar, sai kito sabo da cambas na gwanjo guda daya, da ganamasgo da fatar kwaikwadon kan Bald cap, da fatan kunne da silkin dokin dakomima sanan suka dawo gida wajajen karfe daya suka shiga uwardakan su da kayan bata bari Baba yaje mallaci ba sukai salla adaki already yara duk sun dawo gida since abincin rana sukaci suka koma aiki, saida sukaci abincin da Fatima takawo musu sanan Mama ta kalleshi tace "lokaci yayi kira yarka muyi maganar anan uwar dakana" gyadamata kai yayi abin tausayi muryanshi har wata yar dishewa tayi ya kwalamata kira. "Za.....Zara, Zara'u, Zara" dag daki ta amsa da "na'am Baba" fitowa tayi tazo ta tsaya agaban dakin batare data shigoba ahankali yace "shigo" sallama tayi ta shiga dakin tasami waje tabakin kofan ta zauna akasa tace "gani Baba" shiru yayi yana kallonta duka duka yaushe yarinyar nan taji sauki dahar zai iya mata wanan maganan ganin yakasa magana sai kallon yarinyar yake kaman yauya fara ganinta yasa Mama ta kalli yarinyar tace "Fatima ayanda mahaifinki yawahala dake aduniyan nan inhar kika kasa rufamai asiri awanan bakin yanayi dayake ciki wlh sai Allah yay mummunan ykamaki, tun kina yar shekaru biyu mutumin nan yake wahala danya sami kudi yaciyar dake" Mama tai shiru tana kallon Fatiman dataga bata gane komiba kan zancen datake fadi, Mama tace "lokacin dakika gama Js3, zaki shiga SS1 wato shekaru uku kenan dasuka wuce lokacin muna wanan tsohon gidan damuke ada, Babanki fatara ta isheshi baida hanyan samin kudi yasakaki a school gashi har anfara first term kina zaune damu agida, wata kawata mai suna Razika tare muka taso tai aure mijinta Lawyer ne amman karamin lawyer yana kiranta da Madam hakan yasa sunan yabita, muna cemata madam, akwai wasu lauyoyi da mijinta kema aiki, suna taimakama musulmai ta hanyar basu bashi kona miliyan nawa kakeso kekona biliyan nema zasu baki sanan babu interest, ayanda suka baki kudinsu ahaka zaki mayarmusu dashi batare dakin kara musu ko ficika ba, su kalan tasu yanayin taimakon kenan, sanan idan kika karba keda kanki zaki fadi ko shekara nawa, wata nawa koma dai yaushe kikeso ki biyasu kudinsu bak sharadin dayane duk randa kika fadi zaki biya back ranan zaki biya, idan ranan tazo baki dashi akwai abu biyu kodai su kulleka agidan yari kokuma kabada danka namiji babba yaje yamusu aiki zasuyi calculating sufadi maka albashin danka misali suce alabashin yaronka dubu dari duk wata to haka yaron zaiyi aiki harna watananin dazai daukeka kudin dasukebin ubanka yakare, but duk randa uban yasami kudin zai iya kiransu yabasu adawo maka da danka cikin koshin lafiya, danaji wanan labari mai kyau dan tunda nake arayuwata ban tabajin wanan kalan taimakon alheri hakaba, aduniyan nan yanzu ko kawarka tabaka aron kudi saita cemiki idan kin juya zaki dawo mata dashi ki kara mata wani abu akai, amman wanan kam ga makudan kudi ko nawa kakeso sanan kaida kanka zaka fadi ranan dazaka biyasu back babu ko anini asaman kudin da gudu nadawo na sanarda mahaifinki duk wanan bayanin dana miki nidashi muka shirya na kaishi wajen mijin madam Oga Abdu, yamana hanya dan irin kudin nan sai kanada hanya kanada kafa, yamana hanya aka saka sunanshi cikin masu neman bashi akace za'a nemesh i l, bayan kwana bakwai aka kira babanki aka dauki information dinshi, Mijin Madam ya tsayama Babanki amatsayin guarantor na Babanki kuma witness na babanki dan bansan kowa yasani asan bashi mukaci, aka kirga miliyan uku cash yan sababbin dubu dubu aka bama babanki yadawo da miliyan uku cash a hannu gida, kafin yadawo bayan anbashi