← Book details Ban Saketa Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 49

Sashe 49

Ban Saketa Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Amarya kam tunda su iman suka tafi tak'ara tsananta kukanta, dama angon yana gidan, kuma bai gayyaci wani abokiba domin sayen baki.
Suna tafiya yashiga d'akin amaryar tasa, tuni tausayinta yakamashi, jiki amace yahau gadon, d'agota yayi yarungume, yana lallashi.
Sorry my Khadee kibar kuka plzz, kukanki yana cin zuciyata, yau ranar farincikinmu ce mun mallaki juna amatsayin zaman dindindin.
Namiki alk'awarin zan kula dake tamkar agidanku.
Itadai tana jinsane kawai, amma ita kad'ai tasan k'unar da zuciyarta take mata, ga tsoro fal ranta.
Da lallashi yasamu taci wani Abu, sanan sukayi sallah.
Hummm dagananfa oga Umar yanuna kwad'ayinsa afili, yayinda tuni idon dee..... Ya raina fata.
Tana ganin yafita zaicanjo kaya, tasakama d'akin key, shirin barci tayi tahaye gadon ta kwanta.
Bayan kamar minti20 saiga Umar yadawo, yanata6a k'ofa yaji GAM, komawa yayi d'akinsa yad'akko wani key d'in.
Barci yafara d'ibar dee..... Taji motsin mutum akusada ita, afirgice tabud'e ido, tako daddage zata kurma ihu, dasauri yasa hannunsa yarufe mata Baki, ninefa khadija yafad'a cikin kunnenta.
Jikinta na rawa ta ce, to Dan ALLAH nidai kafita.
Murmushi yayi yana rungumeta, habadai kinta6a ganin ango da amarya sun raba wajen barci?.
Tabud'e baki zatayi magana ya........ Hummmm saida safe my dee.... Asha amarci lfy.
Haka rayuwa tacigaba da shurawa, akwana atashi babu wuya wajen ubangiji.
Zuwa yanzu cikin iman yashiga watan haihuwa, haihuwa koyau ko gobe.
Reefat ta haihu tuni, tasamu mace maisuna Fateema Zarah, su iman sunje sunan suma, to ALLAH yaraya mana fateema.
Itama Xoxo cikinta yafito sosai, anan ana zubama Dr Nabeel shagwa6ar da'aka saba
Su dee..... Amarya, yanzukam andaina kuka, sai amarci da'akesha babu k'arya, tayi wani bul bul da'ita, Umar kam jiyake tamkar yacinyeta saboda so da k'auna, abin Nasu acan acan.
Yau tunda iman ta tashi takejin garin sama sama, gashi Dr bayama garin, yana wajen aiki.
Tana kwance akan kujera doguwa sai cije le6e takeyi, marwan yashigo da sallama rik'e da hannun musayeef daya d'akkosu daga makaranta, bata cikin hayyacinta ta amsa sallamar.
Atsorace marwan ya ce, aunty lfy kuwa?.
Murya asark'e tace marwan kiramin mom..... Aii kafin tak'arasa yayi waje, musayeef yazo gabanta yana kiran aunty maa miya sameki?, bakida lfy ne?, bata amsashiba Dan bazata iyaba.... Ahaka mom tashigo da gudu itada mama, hasbinallahu wani'imal wakil, iman haihuwa?, marwan muje fiddo mota.
Haka suka taimaka mata zuwa mota, dole da yaran aka tafi suma Dan gidan babu kowa.
Saida aka shiga da iman d'akin haihuwa sanan mom takira yaya ta shaida masa.
Cikin hanzari yabaro kasuwa.
Yana zuwa likita yana fitowa, yauwa yaya dama kaina fito nema wlhy, inagafa zamu bud'e tsohon aikintane na haihuwar musayeef kawai.
Babu damuwa Dr yaya fad'a ahanzarce, hannu yasaka musu amadadin Dr Isma'il.
Babu 6ata lokaci suka Shiga aikinsu.
Bayan wani lokaci aka fito da k'atuwa baby mace, masha ALLAHU suka Shiga fad'a suna amsar yarinyar kowa bakinsa har kunne.
Yaya ya ce, "maman fa?.
Itama tana cikin k'oshin lfy, mun kaita d'akin hutune.
Kafin kace mi, asibiti yacika da 'yan uwa da abokan arzik'i, su dee..... Amarya duk an iso, hakama Xoxo tazo danata kayan itama.
Dr imsa'il ma an sanar masa, farinciki kam aii ba'a magana, haukacema yaya yai da ihu awaya.
Satin iman biyu a asibiti aka sallameta, sukadawo gida cike da farinciki, zuwa sanan Dr yazo.
Shirin suma akafarayi, dafarko iman ta ce, " bazatayi taroba, Dr ya ce, "wlhy bai yardaba, ba'ayi haihuwar musayeef ba yanzuma ta ce, " baza'ayiba, aii wlhy suma kamar anyi angama.
Su dee... Ne 'yan zuga Dan kullum tana gidan, danma Dr ya ce, "karya k'ara ganin k'afarta sai ranar suna.
Badan tasoba ta hak'ura, amma tak'udiri anan zata kwana ana gobe suna.
Na ce, " humm.
Masha ALLAHU munsha suna yarinya taci sunanta Nafeesa, tom ALLAH yaraya mana nafeesat.
Bayan anci ansha anrak'ashe an k'walle kowa Yakama gabansa, xoxo da dee... Da aunty Salma kawai aka bari sune amarori k'irjin biki, saida suka gyara ko'ina sanan kowa mijinta yazo d'aukarta suka tafi.
Umar kam dayazo dee.... Ta tubure saita k'ara kwana d'aya, bayason 6acin ranta Dan haka yabarta sai goben, babu Wanda yasan yanda sukayi, tatsula k'arya wai shiyace tak'ara kwana.
(Haba dee.... Nagane wayonki sokike sai kun soya rago kawai, zan turo miki Rano ta tayaki Dan nasan tana son hanji
++++++++++++++
Iman zaune tagama shirya baby feena dakaya masu azabar k'yau, musayeef na saman gadon yana game d'insa na fama da wayarta, yanayi yanacin biskit, yauwa yarinyar daddy kinga ki kwanta ga yaa musayeef nan naje nayi wanka.
Musayeef ya ce, "aunty maa goyamin ita to kafin kiyi wankan.
A'a kabarta takwanta tagaji da goyo bari nayi wanka nafito kaga daddynka yakusa dawowa.
Tana Shiga wanka Feena tafara kuka, musayeef yajuyo yana mata magana cikin wasa baby feena ta daddy, yafad'a yana lakayar kumatunta, biskit d'in ya 6alla yasaka mata abaki.
Iman batasan hidimar dayakeba tazata feena tayi shirune saboda was an da musayeef yake mata.
Hankali kwance tayi wankanta ta fito, zuwa sanan biskit d'in ya narke abakin feena, shikam yak'ara saka mata wani azatomsa ta shanye, da sauri iman taja k'ofar bayi tarufe tak'araso gaban gadon tana fad'in na Shiga Tara ni saudatu musayeef mika batt?.
Adaidai nan Dr yashigo shima, iman tad'ago feena tana girgizata musayeef bakada hankali kabata biskit.
Da sauri Dr yak'aro gurin biskit kuma, wlhy habibi biskit yabata nikam naga takaina, kar6ar feena Dr yayi da sauri, bakinsa yad'ora akan na yarinyar yafara zuk'e biskit d'in daga bakinta, saida yatabbatar babu komai abakin sanan yamik'ama iman ita, kinga bata nono tasha.
Musayeef dake zaune yana kallonsu yayi shiru Dan yagane abinda yayi ba daidai bane, Dr yakalleshi oh kai musayeef haka zakayi naka rainon kai kuma?.
Wanefa raino, aii sainama zaneshi, haka kawai zai kashemin yarinya.
Musayeef najin zancen duka yasa kuka, daddy Dan ALLAH kabama aunty maa hak'uri karta dakeni, nibansan feena batacin biskit ba.
Jawoshi Dr yayi kaga karkayi kuka, amma daga yau karka sake bata kaji, ita bata fara cin irin wad'@nnan ba sainan gaba, nono ne kawai abincinta kaji.
Kai yad'aga masa, daddy bazan sakeba aii.
Yauwa d'an albarka.
Itadai iman tanajinsu bata tankaba, saida feena tak'oshi sanan tamik'ama Dr ita, shikuma yad'auketa yanna fad'in Ummm my sweet feena.
Iman ta harari musayeef kaikuma zamu gamu.
Dariya Dr yayi ya ce, "babu wani gamuwa aii mun baki hak'iri dai.
To ban hak'uraba.
Hummm to mikeso muyi miki yanzu.
Zaneku zanyi kawai.
A'a kiyi hak'uri, amma albishirinki?.
Goro tafad'a tana kallonsa.
Hafsat ta haihu yanzunnan namiji................
*luv u oll my fan's*
*(((S)))........2017*
[8/6, 6:04 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*
*_NA Bilyn Abdul_*
_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*
https://mrsbilkisa.blogspot.com
*_(page 50 to 60)_*
Wani ihun murana iman tasaki, shima musayeef ganin haka saiya fara tsalle, Dr kam dariya kawai yake musu.
Dandanan tashirya suka nufi gidan Xoxo.
Tana shiga suka rungume juna cikeda farinciki.
Iman tad'auki sargad'ed'en yaron fari tas masha ALLAH.
Kai tawan yarona yafiki k'yau.
Hhhh ALLAH ya kiyaye, kuma kunsan nagaba yayi gaba aii.
Dariya iman tayi ta ce, ''ki k'ara kallon madubi to, babu wani kalla dazanyi nasan nafi k'yau, Haka sukaita gardama suna tsokanar juna.
Ansha sunan baby Wanda yasami sunan muhammad, ya ALLAH karayamana Muhammad mai babban suna.
Sunakam yayisuna Dan munrak'ashe mun k'walle, su Rano ne 'yan suyar hanji, kunsan nantafi afana
, Dr yayi hidima sosai, to balle uban gayya Dr Nabeel Wanda bakinsa yak'i rufuwa, kad'an kad'an saiya lek'a maijego, safaman soyayya suke agaban mutane ko kunya babu
------------------------------------------
*Banyan wani dogon lokaci.*
Abubuwa dayawa sunfaru, masu dad'i da akasin haka, rayuwa tayi nisa sosai.
Zuwa yanzu Reefat tanada yaranta uku, hakama Xoxo tanada biyu, dee.... Ma ta silli6o mana 'yan biyu mace da namiji, Dr yasamu jika kamar yanda yake fata.
Anyi bikin marwan dawata yarinya Zuh'ra, harma da tsarabar ciki.
Su aunty da Raihan sunyi aure suma, sunan zaune acikin garin sokoto, suma yanzu komai daidai sun shiryu tareda tsaida zuciyarsu waje d'aya, sunan zuwa kano zuminci hakama su iman suna zuwa, aunty dai har yanzu bata haihuba, amma raihan ta haifi d'iyar mace.
Hummmm masu gayya da aiki kam yaransu hud'u yanzu, bayan musayeef, feena, an haifi ummukhursum, da Al'mustapha, Wanda take goyo yanzu haka.
Dr anzama babban soja kuma aikinsa yadawo kano, yana kula da iyalinsa yanda yakamata.
Musayeef yazama d'an saurayi masha ALLAH, yanzu rayuwarsa tafi yawa wajen mom da yaya, dansun kwaceshi.
Lokaci lokaci yana zuwa gaidasu gwaggo shida k'annensa, deeni ma anzama samari masha ALLAH, Dan shirin aurensama akeyi.
Hakama aunty Salma tana zaune gidanta lfy tareda 'yan yaranta biyar masha ALLAH.
*_BAYAN SHEKARA 25_*
feena tashigo dagudu tana kwala kiran aunty! aunty!!.
Dr da iman suka fito da sauri suna fad'in feena lfy dai ko?.
Bayan Dr taje ta mak'ale, daddy ya Musayeef ne zai dakeni Dan kawai nad'an d'ebo shamfo d'insa na wanke kai.......
Kafin tarufe baki musayeef yashigo rik'eda belt d'in wandonsa, ganin iyayen nasa tsaye yasa shima yatsaya yana Harar feena.
Dr yagirgiza kai, saboda tayi anfani da shamfo d'inka kabiyota zaka Daka?.
ALLAH daddy bafa yau tafaraba, hakama ranar itada husaina da Nawal d'in aunty dee.... Sukaje sukamin 6arna ad'aki, nahukura bance komai, shine danta rainani yau takoma d'ibarmin shamfo.
Iman ta hararesa to ba k'annenka bane, dansuyi amfani da kayanka shine kaketaman yima mutane wani babbotai, ALLAH ya shiryeka musayeef, taja tsaki takoma d'aki rik'e da hannun al'mustapha dayazama d'an saurayi shima.
Dr ya ce, "tom kayi hak'uri bazasu sakeba kaji ko.
Kai ya jinjina yafita, aransa kuma yana fad'in wlhy nakamata saina rankwashi kanta sau bakwai Dan Nasan bazata dainaba, itama husaina k'atuwa da ita tana biyema feena.
Wai kuma ahaka ake shirin auramin ita kanta na rawa, hummmm yarinya zan saitakine.
(Nikam Bilyn Abdul nayi dariya, wai yakaga musayeef da mata gwangwazo
*_TAMMAT BI HAMDULLAH_*
```INA FARINCIKIN KAMMALA WANAN 'DAN LITTAFI NAWA.```
kuskuren danayi ALLAH ka yafeni, abinda nafad'a daidai ALLAH yasa ya amfanemu gabad'aya.
_Godiya mai tarin yawa ga masoyana abin alfaharina, bansan dawana baki zan godema masoyaba, amma zuciyata tana tsananin k'aunarku, kunacikin abubuwa muhimmai na rayuwata, ya ALLAH kabarmu tare, yak'ara dank'on zuminci atsakaninmu, ngd ngd sosai da k'ok'arin bibiyata._
*Bazan iya mantawa dakuba Dan tun farkon fara rubutuna kuna tare dani.*
deexerh.
sa'adatu sa'ad.
zulaiha.
my Ikilee.
Riddallah.
marak'isiyya (k'anwata).
Aysha Manshat.
Reefat yahaya.
Ayeesh.
'Dan mom.
Teema.
Adama gages.
Uwargida.
Sakina gages.
Hafsy.
Binta (kakus)
*_HOUSE OF NOVELS_* (gidan Abba Gana)
Kuntaka rawar gani sosai atafiyata, Dan shine gida nafarko dasuka fara karanta buk d'ina, shiyayasa bazan ta6a mantawa dakuba har k'arshen rayuwata, ALLAH yabar zuminci.
*_(Kaima Abba Gana ngd kana taka rawar gani arayuwata ta rubutu, ngd sosai)._*
_godiya gadikakanin groups na Novels ALLAH yabar zuminci ngd da k'auna kuda Admins naku, ALLAH yabar zuminci_
*_"yan Group d'ina abin alfaharina, ALLAH yabarmu tare
."_*
*_taku har kullum BILKEESA IBRAHEEM (Bilyn Abdul)_*
_marubuciyar_
*_RASHIN SANI_*
*_AUREN K'ADDARA ko BIYAYYA?_*
*_K'ANWAR UWACE ko KISHIYAR UWA?._*
*_NIDA AMINIYATA_*
*_NAWAFF_*
*_SABON AL'AMAREE_*
*_KUKAN KURCIYA...._*
*_BAN SAKETA BA!_*
sai mun had'u asobon littafina mai suna_ *ABDUL-MALIK (Bobo)*
Shima zaizo muku danasa sabon salon na musamman.
Inafata zaku watsar daduk wani kuskure danayi kasancewata ajiza.
Inakuma Baku hak'uri wajen jinkirin akan rubutun littafinnan ngd ngd ngd.
Luv u oll
*Bilyn Abdul*
[8/6, 6:04 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*
*_NA Bilyn Abdul_*
_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*
_Assalamu alaikum masoya na, godiya tamusamman agareku, k'auna mai yawa agareku, jinjina da fatan alkairi su tabbata agareku, banida bakin gode muku, lallai Ku wani 6angarene narayuwa da tarihina, duk inda masoyina yake ina alfahari dashi, kuma ina k'aunarku_
_ngd da d'umbin k'aunar dakuka nuna mini, ALLAH yasaka da alkairi yabar zuminci._
_naga sak'onninku, wasu na amsa wasu ban samu damaba saboda matsalar network dana fuskanta ajiya, kuyi hak'uri ngd sosai, kuma ina alfahari daku arayuwata._
_abaya nace muku Next Novel d'ina *ABDUL-MALIK* to yanzu ansamu canji saboda wasu dalilai, yanzu Next Novel d'ina shine *CIKI DA GASKIYA......*, insha ALLAHU zai zomuku anan kusa danasa sabon salon, Dan gsky ban ta6a rubuta Novel makamancin wannanba, Dan haka ina Neman addu'arku agareni gudun shiga had'ari._
_```masoyi abin sone, masoyi abin alfahari ne, masoyi abin tunk'ahone, masoyi abin k'aunane, inasonku fiye da tunaninku, ALLAH yabarmu tare_```
_nasan wasu zasuyita tunani saboda nace atayani addu'a a buk d'ina nagaba, kunsan rayuwa kowa da irin fahimtarsa, wasu zasu iya tunanin labarin nawa ya shafesu, kuma ko kad'an ba haka bane..... Bari nabarku karna cikaku da magana, saimun had'u a *CIKI DA GASKIYA, WUK'A BATA HUDASHI* zaizo muku cikin cikakkiyar Hausa kamar yanda yadace_.
SAIYA ZO...
*_masoyi abin alfahareee_*
*_CIKI DA GASKIYA.....!_*
*_CIKI DA GASKIYA.....!!_*
*_CIKI DA GASKIYA.....!!!_*
Bilyn Abdul.
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
TECNO LD7
WPS Office
Normal
Times New Roman
Times New Roman
Calibri
Calibri
!%),.:;>?]}
$([{
896e4e0230ef4dfb9936762644f3703a
Chapter 49 · 0% Book details