← Book details Ban Saketa Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 49

Sashe 36

Ban Saketa Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

murnar ganinsu. Gwaggo tafito daga kicin danjin ihun murnar musayeef, Ita kanta tatsorata daganinsu amma dukda haka saita ce, "sannunku dazuwa. Yauwa suka amsa mata, ta ce, "kushigo. Iman dai tana tsaye tamkar gunki, Dr Isma'il yak'araso gareta tareda kama hannunta, da Sauri ta fisge hannun takoma ta zauna, sukuma suka wuce cikin falon Inda gwaggo take musu maraba. Bayan sun zauna suka gaisa da gwaggo, Yaya ya ce, gwaggo Abbah fa?. Yana wajen aiki mansur ALLAH yasadai lfy?. Alhmdllh gwaggo saidai munason ganinsa munzone dawata magana. Babu damuwa bari akirashi gwaggo tafad'a tana d'aukar waya. Bugu d'aya abbah ya d'auka tamasa bayani komai, ya ce, "gashinan zuwa gidan. Gwaggo takoma kicin ta had'o musu kayan sha tadawo, har yanzu iman tana tsakar gida zaune ta rabga uban tagumi da hannu biyu. Ita atunaninta kosunzo su k'ar6i musayeef ne, tab lallaikam Ashe yau da bala'i wlhy, Dan mairabani da yaronnan saiya shirya, wlhy koza'a kasheni bazan yarda su d'aukeshiba. Tana cikin zancen zuci abbah yashigo, a'a iman lfy?. Ta share hawayenta abbah Dan ALLAH karku yarda sunzo kwace musayeef ne nikuma wlhy bazan basuba. Abbah baice komaiba Yakama hannunta suka Shiga falon ,Dan shima komai za'ayi bazai basu musayeef ba. Bayan anyi gaisuwar mutumci da tambayar rayuwa Abbah ya CE, ALLAH dai yasa lafiya. Lfy lay Alhaji alkairine yakawomu. Yaya yacema Raihan ta maimaita abinda tafad'a agida. Tiryan2 ta zayyane komai, Dr Isma'il ma ya d'ora da nashi, salati su abbah sukaitayi, itako iman kuka Rurus takeyi tamkar ranta zai Fita, wlhy ko amafarkinta bata ta6a kawo hakan arantaba yanzu dama mijinta *bai saketa ba* aka rabasu kai ALLAH yarabamu Da saharrin mak'iyidai. Bayan maida zance abbah ya ce, " INA Neman wata alfarma agunku mansur da Isma'il harda ke mama. Suka amsa dato suna saurarensa. Abbah ya ce, "Dan ALLAH karku saki matanku kubarsu kawai, Haka ALLAH ya hukunta. Arazane Dr Isma'il yake kallon Abbah, abbah ya ce, " alfarma nanema inafata zakuyi mini. Mama ta ce, "shikenan Alhaji insha ALLAHU bazasu sakesuba. Dr Isma'il yay wani murmushi mugunta, azuciyarsa ya ce, " wlhy sai sungwammace inama mun sakesu, Dan zasusha mamaki humyimm k'yarrrk. Anan kuma Dr Isma'il ya ce, "yanason sutafi da iman yau. Itako tafashe da kuka ta ce, bafa yauba. Mama ta ce, " a k'yaleta to har sanda tasa shiya, aii bama zaiyuwuba Isma'il, kata6a ganin an raba mutum da gidansu tashi d'aya, kabarta har sai sanda ta shirya,....... A'a abbah ya katseta, insha ALLAHU nanda sati d'aya ko kwana goma zata dawo d'akinta shima nace hakane saboda shirye2. Dr Isma'il ya ce, "abbah kardai asayama iman wasu kayan d'aki tunda ba'a kwaso wad'ancanba, insha ALLAHU awanan karon nizanyi komai, iman kawai da musayeef nake buk'ata. Shike nan Isma'il ALLAH yayi muku albarka. Iman tashi tayi tashige d'akinta tana hawaye, Dr Isma'il yabita da kallo. Gado tafad'a tana kuka, wai Ashe Doctor yak'ara aure bata saniba, dama Ashe Raihan budurwarsa CE ya6oye mata, kuka take sosai, wlhy badan kar iyayenta sauce ta rainasuba da babu Inda zata, dabazata koma gidansaba saidai ya saketa kuwa, haka taita kuka zuciyarta na k'una saboda kishi, sai yanzu tagano canjin dayay mata. Dr Isma'il kam badan yasoba yabi su Yaya suka tafi, yaso ace ayau aka bashi iman suka tafi tare, amma yazaiyi dolene yabi Maganar many a............... *luv u oll my fan's* *(((S)))..............2017* [8/6, 6:02 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *miya kamata nayi?* _humm hattara 'yammata rayuwar kece raini had'ari CE, duk Wanda yace shi wani ne, kosai yazama wani, tofa yana tareda wahala arayuwarsa._ _wanan rayuwar tana bala'in wahalar da 'yammata da matan aure, abinda wance tayi nima sainayi kota halin k'ak'a, hakan ba daidaibane, wanan rayuwar tana jefa mata dayawa fad'awa zina mad'igo kowani mummunan yanayi, burin sainafi wance kosaina tarar da wance yajefa matan aure dayawa bin maza._ _haba 'yar uwata miya rud'eki saboda San duniya kiringa zina da aurenki?, shin kinmanta da d'unbin zunubin dake bibiyarki ga cin amanar Addininki, cin amanar aurenki, ga cin amanar 'ya'yanki, ga cin amanar iyayenki, ga cin amanar 'yan uwanki._ _tsaya matsayinki domin haka ALLAH yayimu wani yafi wani, indai zaka ringa kallon na sama dakai to kanatare da wahala da asarar rayuwa kuwa._ *ALLAH yasa mugane* *(page 31)* Haka iman tawuni ad'aki tana kuka, da musayeef yaje wajantama koroshi tayi, yafito yana kuka, gwaggo ta ce, "lfy na gwaggo?. Aunty maa ce takoroni wai na 6ace mata dagani anan. Jawoshi gwaggo tayi jikinta tana share masa hawaye, kaga ishirunka yau aunty maa batada lfy ne, kabarta ta huta, kaji na gwaggo. Kai yad'aga alamar to, yauwa na gwaggo, Abbah yafito daga d'aki yana shirin fita, a'a Na gwaggo lfy dai ko?. Shida mamansane, kasan iman da zuciyar tsiya. Murmushi Abbah yayi, yakama hannun musayeef kaga muje karakani anguwa. Tsalle musayeef yafarayi na murna, suka fice shida abbah, gwaggo kuma tanufi d'akin iman. Kwance take akan gado idonta arufe amma hawaye sunata zirara, filon duk yajik'e alamar tadad'e tana kukan. Gwaggo ta girgiza kai tareda k'arasawa Inda iman take, bakin gadon ta zauna tad'ago da kan iman tamaida kan cinyarta. Batayi maganaba amma tana shafa kan iman tareda d'an bubbuga bayanta alamar lallashi, sunkai tsawon minti15 ahaka, har iman tayi shiru saidai ajiyar zuciya datake saukewa ahankali. Gwaggo ta ce, " haba iman miye kuma abin kuka muda yau abin farinciki ya riska, kinsan kuwa yanda muke farinciki nida abbahn Ku?, kobakison komawa ne?. Da sauri iman ta gyad'a kai. Humm to saboda mi?. Gwaggo yafariga ya k'ara aure, gwaggo tayi murmushi, yo iman Dan isma'il yak'ara aure shine bazaki komaba?, kowa bada halinsa zai zaunaba agidan, karki mantafa yanada hurumin auren mata hud'u fa. Nifa gwaggo bawai ina nufin haka bane, wlhy ina tsoron abinda zaije yadawo, tunkafin tazo gidan suka iya fiddani balle yanzu tana cikin gidan amatsayin matarsa. Gwaggo ta ce, "hakane iman, nidai abinda nakeso dake kizama mai yawan addu'a da Neman kariyar ubangiji, kid'auka abinda yafaru a baya yana cikin k'addararki, jiyanki tawuce yanzu gobenki zaki tsunkanya, fatana kiyi nasara a gobenki da jibinki, amma ta yaya?. Ta sanadin hak'uri da yawan juriya akan lamarin rayuwa, indan kika rik'e k'yautatawa da biyayya tsafta tattalin mijinki da 'yan uwansa ina mai tabbatar miki kece mai nasara insha ALLAHU. Isma'il yana sonki karki manta asanadin rashinki yakamu da ciwo mai ban tsoro, Dan ALLAH ina rok'onki karki maida hannun agogo baya, nasanar da 'yar uwarki tanata murna itada mijinta, muma gamu muna cikin farinciki, haka family d'in Isma'il suna cikin farinciki, mizaisa kebazaki kasance a farincikiba?. " kebak'ya buk'atar farin cikinmune?, kobaki so musayeef yarayu agidansu cikin 'yan uwansa, wanan yawon da'ake dashi bashida wani fa'ida". Ina buk'ata gwaggo, iman tafad'a tana share hawayen idonta. Yawwa 'yar albarka toki kwantarmin da hankalinki kinji, kizama mai tawakkali arayuwa, kefa yanzu uwace, idan kina saurin karaya arayuwa yaza'ayi ki k'arfafama musayeef gwuywa shikuma?. Kinutsu kicigaba da walwalarki, kinga nanda kwana goma abbahn Ku yace zaki koma, to yakamata mufara shirye2 Dan yanzu bake kad'ai baceba. Itadai iman batace komaiba sai kai data d'agama gwaggo alamar to. Haka gwaggo tayi ta mata kalamai masu dad'i harta saki jikinta. Su Dr Isma'il kuwa suna zuwa gida yanufi 6angarensa, Raihan madai ganin kowa yanufi NASA 6angaren yasa itama jiki a asanyaye tabi bayan Dr Isma'il. Afalo ta iskeshi zaune saman doguwar kujera, yajingina bayansa da kujera Kansa Asama idanunsa alumshe sai faman murmushi yakeyi. Tayi tsaye tana kallonsa, jitake wani bali'in sosa yana k'ara ratsa sassan jikinta, tamkar taje ta rungumeshi haka takeji, amma babu dama. Gwuywa a sa6ule taje gabansa ta durk'usa, muryarta narawa ta ce, "yaa Isma'il!. Yanajinta yay shiru, amma ya daina murmushin dayakeyi. Takuma fa d'in my One!. Ak'ufule yad'ago ya ce, " a'a uban my one, yanunata da d'anyatsa "k kishiga hankalinki wlhy, idan kika k'ara kirana da wanan sunan sai jikinki yayi tsami, kuma tun wuri ki 6acemin dagani kafin na 6a66allaki na 6allah banza. Da Sauri ta mik'e tabar falon tashige d'aki tana hawaye. Yarakata da wata uwar harara, yana tsaki ai bama kiyi kukaba yariya sainan gaba, saikince inama sakinki nayi yafimiki alkairi, yamaida kansa ya kwanta, kiran Dr Nabeel ne yashigo wayarsa, yad'aga suka gaisa. Isma'il ya jikin?. Da sauk'i d'an uwa, wai kasan miya faru kuwa?. A'a saika fad'a cewar Dr Nabeel. Labarin duk abinda yafaru yabashi, Al'ajabi da mamaki suka cika zuciyar Nabeel, ya ce, " lallai nayarda kaidin mata yafi na shaid'an, irin wananan k'ulli haka, amma miyasa Abban Iman yahanaka sakin banza?, aii daga ita har yayarta sun cancanci saki wlhy. Humm karka damu Nabeel wlhy saisun gwammace mun sakesu da zamansu atare damu, nikad'ai nasan abinda nake shirya musu zasuci ubansune aii, kaidai zakasha labari. Nanda kwana goma iman zata dawo, ka saurari zuwana gobe idan ALLAH ya kaimu. To shikenan ALLAH yakaimu goben saikaxo, Nima zan lek'a gidansu Hafsat ne, wlhy harnayi kewarta. Humm mutumina kaimafa kashiga dayawa. Dariya Dr Nabeel yayi, bama kasan nashigaba sai hafsat tazo gidana. To ALLAH yakaimu lokacin, aii gara mu aurar dakai muhuta da tuzurancinka. Hhhhhh zan rama sai iman tadawo. Zadai karame na hafsat. Wayar suka yanke kowa yana dariya. *bayan kwana uku* Dr Nabeel yabama Xoxo labari, Dan haka tazo har gida tak'arajin bayani, tayi farinciki, takumayi bak'incikin Auren Raihan da Dr Isma'il yayi, amma zata bar gidanne da k'afarta wlhy. Xoxo tabama Umma labari, lamarin ya girgiza Umma sosai, kuma tad'au aniyar gyara iman Dan jinta take kamar Xoxo, har gida taje tarok'i gwaggo da abbah suka bata iman ta taho da ita. d'aki guda aka ware mata, gyara na rikita guys ake mata, bata fita ko k'ofar d'aki, duk abinda take buk'ata Xoxo take mata. Humm masu karatu kunga kuwa yanda iman takoma, abin sai Wanda yagani, dolenefa mace ta rikice balle namiji, (nace humm su Dr Isma'il za'a baridai nayi shiru). To a6angaren Dr Isma'il mafa gyara sosai akema 6angarensa, Dan yayansa ya ce, "shine ya cancanta yayi komai, ALLAH sarki Yaya da ana samun yayye irinku da k'anne bazasuyi kukaba, gaba d'aya gidan ansake MASA fenti tamkar za akawo sabuwar amarya, Raihan da Aunty sunata kallon ikon ALLAH, _(lallai zakaran da ALLAH yanufa da cara, ko ana mazuru ana shaho saiyayi)._ Suna cikin
Chapter 36 · 0% Book details