Sashe 39
Ban Saketa Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cike da wani irin salo yake sumbatarta, lakwas tayi takasa yunk'urin kwacewa, shikam saiya k'ara k'aimi cike da nagarta. Sunkai tsawon minti18 ahaka sanan yazare bakinsa, idonsa yayi jajur, yarungumeta tsam yana hawayen farinciki, itama kukan take danji take zuciyarsa nafaman bugawa da k'arfi, hannu tasaka saitin zuciyar tasa ta danne wai ko zata dainajin bugun. Ahankali yad'agota yana murmushi, tacire hannunta daga k'irjinsa, yakama hannun nata yamaida ak'irjinsa, karki cire my life, kusantowarki gareni yasa zuciyata ta canja salon bugu ayau, jinake tamkar zata Faso k'irjina tafito, inasonki dayawa my life, bazan iya yafema wad'anda suka rabamuba har tsawon shera hud'u da Rabi, dolene su fuskanci hukunci da horo mai tsanani........ Lallausan hannunta tasaka tarufe masa baki, tayunk'ura ahankali ta tashi zaune sosai akan cinyarsa. Share masa hawayen tashiga yi yayinda itama idonta kezubar hawayen, tanason Dr Isma'il sosai, shiyyasa bazata iya jure ganin saukar hawayensaba, shikam aii saiya k'ame k'am, Ashe har yanzu iman d'insa tana sonsa?. Muryarta cike da taushi ta ce, "karka damu _Zuciyata_ muyarda da k'addara bana son zubar hawayenka, kad'auka mukeda nasara tunda gani nadawo gareka, iman takace kai kad'ai, kuma zan cigaba da kasancewa taka har a aljanna insha ALLHU RABBI. wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke ahankali, yakuma rungume iman tareda nuna mata wani sabon salon soyayya na musamman mai tsadar gsk, _(nidai bilyn Abdul kauda idona nayi gefe Dan lamarin yagirmi wayona),_ humm. So makahone. Ganin zai wuce gaba yasata rik'e hannunsa, duk jikinta yayi sanyi lakwas, ya tsura mata rinannun idanunsa wad'anda suka k'ank'ance, muryarsa a sark'e ya ce, " tashi muyi sallar godiya ga ubangijin talikai. Tsorone yashigi iman data tuno da Daren farkonsu, tasha wahala, nantake kanta yakawo mata haske, tayi k'asa da ido tana k'arema k'irjinsa kallo, muryarta dad'an rawa ta ce, "nifa ina danja. Ban gane kina danja ba?. Cusa kanta tayi a k'irjinsa cike da kunyar abinda zata fad'a, muryarta can k'asa ta ce, " ina fashin sallah. Shiru yayi na 'yan sakwanni, lallai danja kam, gsky kika fad'a Dan an6ata masa show daya dad'e yana shiryawa. Jin yayi shiru yasa tad'an d'ago dantaga lfy, murmushi yasakar mata, Wanda takeda tabbacin iyakarsa fuska, ta maida kanta tana gumtse dariya, Dan yabata dariya wlhy, ta ce, "yanaji kayi shiru?. Manneta yayi sosai da jikinsa, acikin kunnenta yarad'a mata wani abu, Wanda Nima banjiba. K'ara cusa kanta tayi tana wata irin dariya maicike da amo. Shikam saita k'ara narkar dashi, gudun kar ayi abin kunya yasashi d'agota, my life dariya kikemin ko??, hummm zan ramane aii, tashi kici abinci. Tashi tayi zaune tana kauda kai, nifa ba dariya nake makaba, humm to mikikeyi?, babu komai. Shikenan zamu had'une aii. Dakansa yabata naman gasashshiyar kaza mai dad'i, sukaci suka k'oshi suka d'ora da sassanyar fresh milk. Koda zata saka kayan barci saita shige bayi, murmushi kawai yayi, yaja filo yarungume. Can k'arshen gado ta lalla6a ta kwanta, azatonta yayi barci, batasan yana kallontaba yayi shirune kawai. Saida takwanta tayi addu'a, sanan yajuyo had'e da rungumota yana fad'in 'yammata aii tuni an wuce wanan k'arnin kokin mantane. Shiru tayi batace komaiba Dan kunya. Dukda baisamu abinda yake k'ulafucinba tasha jagwalgwala sosai, dan saida ta gwammace dama batayi masa k'aryarba, sai wajen k'arfe 2 yabarsu suka runtsa. Da asuba yatashi dak'yar yashiga bayinta, saida yayi wankan sanan yay alwala, bai tada iman ba dan yasan bata sallah, d'akinsa yanufa yasaka jallabiya yanufi masallaci. Iman kuwa yana fita tabud'e ido, gwalo tamasa sanan tasakko daga gadon tashiga bayi, alwala tayi tazo tayi sallar asubahi, tamaida kayan barcinta ta haye gadon kamar komai bai faruba. Saida gari yafara haske suka dawo daga masallaci shida marwan da Yaya, kowa 6angarensa yanufa. Sanda yashigo d'akin iman takoma barci Dan bai barsu sunyi barci ishashsheba da daddare. Kwantawa yayi shima tareda rungumeta sai barci. *_7:48am_* iman ta farka, ahankali ta zare jikinta daga NASa gudun karya tashi ta saka masa filo, falo tafito, dukda babu wani datti mai yawa saida ta k'ara gywarashi, tabaza k'amshi, d'akinsa tashiga, tabi ko ina da kallo, ancanja komai bawanda tasani bane, tagywara d'akin tabaza k'amshi nanma, anan tayi wanka tad'anyi kwalliya sanan tanufi d'akinta. Ahankali take komai dankar ta tadashi, tasaka kaya dasuka kara fidda tsarin halittarta, siket ne da Riga na atanfa, kai telan nan ya iya fidda d'inki gsky, ta nad'a d'aurin d'ankwali mai tsari sanan tafeshe lungu da sak'o najikinta da turare. Ahankali Dr Isma'il yabud'e ido yana kallonta, tunsanda take d'aurin d'ankwali yake kallonta, tajuyo danufin fita saitaga idon doctor akanta, lallausan murmushi tasaki tana fad'in dama katashi?. Baiyi maganaba saidai ya mik'o mata hannunsa alamar yanason tashi, matsawa tayi gaban gadon ta kama hannunnasa, ahankali yatashi zaune har yanzu idonsa akanta. Ita kallon nasama kunya yake bata, ta daure ta ce, "kallonnanfa ya Isa haka. Kamo hannunta yayi yazaunar saman cinyarsa, akunnenta yay magana wadda tasakata saurin saka tafin hannunta ta rufe fuska, da sauri tamik'e daga jikinsa ta gudu........ Yakatseta dafad'in ni wazaimin wankan?, ashagwa6e yay maganar. Da d'an gudunta ta ida fita daga d'akin, yay 'yar dariya, my life sarkin kunya, mik'ewa yayi yashiga bayinta, tawanke bayin tsaf sai k'amshin dad'i yake, ga ruwan wanka anhad'a Wanda yakeda tabbacin nasane. Wankan yafarayi zuciyarsa cike da tunanin iman, gabad'aya yarinyar ta canja masa, komai nata yak'ara girma musamman ma k'irjinta, duk motsin datayi saita kuma rikitashi, yakuma nutsa kansa cikin ruwan yana murmushi. Iman tana fita sukaci karo da Raihan tafito sanye da kayan barci, da alama yanzu ta tashi, har iman tayi niyyar wuceta saikuma tadawo baya tana murmushi. Taje gaban Raihan ta tsaya fuskarta fes, ta ce, " Raihan kin tashi lfy?. Wani k'ududun bak'in ciki yatokare zuciyar Raihan amma saita dake, itama ta CE, "lfy lau. Ashe kin dawo?. Iman tayi murmushi danjin tambayar rainin wayo daga Raihan, tad'an dafa kafar Raihan tana cigaba da murmushi, nadawo Raihan cikin huncin ALLAH, mammallakin zuciya da abinda ta sak'a, tad'aga mata gira, ina fata kema bazaki tafiba zaki zauna murayu tare, harmu haifo k'annan misayeef k'yautar ALLAH...... Tana gama fad'a tayi gaba tana wata irin dariyar rainin hankali, saida taje dai dai k'ofar shiga d'akin doctor sanan tajuyo, cikin wani salo ta ce, *_" BAN SAKETA BA!."_* tadafe saitin zuciyarta sannan tayima Raihan jinjina da hannunta d'aya tad'an gira sannan tashige. Sagade Raihan tayi tanabin iman da kallon harta shige d'akin Dr, zuciyarta cike da d'aci, wai waccan 'yar yarinyarce take gaya mata bak'ar magana a fakaice?. Hummmm iman kikira kanki sorry kawai, fuuuuuu tashige d'aki, tafasa kuka tareda fad'awa kan gadonta daya had'a kwana uku babu gyara. Iman kam tana d'akkoma Dr kaya tana faman murmushi kamar wadda akayima albishir da aljanna, k'anan kaya ta d'akko masa masu k'yau, tafeshesu da turare sanan fito. Tayi murmushi Dan ganin babu Raihan, tayi zaton zata fito ta isketa aii. Dakinta tawuce, agurguje tagyara ko'ina tabud'e d'akin da k'amshi, sanan tadawo falo ta zauna. Fitarta babu dad'ewa Dr tafito, yabi d'akin da kallo yana mai jin dad'i, iman akwai tsafta, amma awannan karon tazo masa da sabon salon k'amshi na musamman. Tsaf yashirya tamkar wani matashin saurayi, babu Wanda zaiga Dr ya ce, "iayi aure harda d'a, falon yanufo shima. Musaueef yashigo falon da d'an gudunsa, cak yatsaya yana kallon iman, fuskarsa d'auke da mamaki, tayi masa murmushi tareda bud'e hannayanta alamar yazo. Zuwa yayi yashige jikinta yana 'yar dariya, aunty maa yaushe kikazo?. Bata bashi amsaba sai faman murmushi take zabgawa na jin dad'in ganinsa, ta ce, " I miss u my derling. Dr Isma'il yana tsaye yana kallonsu fuskarsa d'auke da murmushi. Iman tashare 'yan kwallan dasuka taru mata agefen ido najin dad'i, tad'ago Musayeef daga jikinta ta sumbaci kumatunsa sanan tamik'a masa nata, shima sumbatarta yayi. Sai asanan yaga dadinsa, dagudu yasaki iman yanufi Dr dake tsaye. Dr yatsugunna tareda ware hannunsa musayeef yazo yashige. " daddyna!." "Musayeef d'ina!." Shima yafad'a cike da jin dad'i. Yad'agosa yana dariya, katashi lafiya?, lfy lau daddyna, da k'yau na gwaggo. Musayeef ya ce, daddy!. Ma'am, Dr Isma'il ya amsa. Daddy itama aunty maa tadawo gidanmu. Saida ya kalli iman suka had'a ido tayi k'asa da kanta tana murmushi, sanan yadawo da dubansa kan musayeef, kai ya d'aga masa tareda lumshe ido yana murmushi. Yeeeeeeee musayeef yashiga fad'i yana tsallen Murna, Dr da iman kallonsa suke sunata dariyar jin dad'in ganin farincikin tilon d'ansu. Raihan dataji ihun Musayeef tafito tawani doka uban tsaki tashige cikin, babu Wanda ya kulata danshi Dr ko kalloma tata isheshiba, da ita da babu duk d'ayane agurinsa. Mik'ewa yayi yad'auki musayeef suka k'arasa Inda iman take zaune, zama yayi Kusada ita yad'ora musayeef kan cinyarsa. Kinga yanda musayeef yake farinciki momynsa tadawo ga daddynsa. Murmushi iman tayi batareda ta ce, komaiba. Musayeef ya ce, "aunty maa ina uncle deeni da gwaggo da abbah. 'Yar harara tamasa ta ce, "sai yanzu katuna dasu?. Musayeef ya kalli daddynsa, daddy aii dai Kaine kace zaka kaini ko?. Kai yad'aga masa ya ce, " insha ALLAHU big boy. Dariya sosai musayeef yakeyi wadda tasaka iyayen NASA dariya suma. Iman tamik'e kunga bazan iya wannan shiritarba bari naje na gaida mama dasu Yaya. Shima Dr mik'ewa yayi d'auke da musayeef muma Baza a barmu abaya ba aii, muje muyi breakfast ma. Haka suka rankaya abin sha'awa kamar kasacesu ka gudu, sunsan su yayama suna 6angaren mama, Dan haka suka nufi can kai tsaye, ilai kuwa suna can. Sunbama su mama sha'awa, marwan ya ce, "family ya had'u dee.... CE kawai babu, dariya akayi harda su Dr dake shigiwa. *_(Ni bilyn Abdul na ce, " tofa, mi marwan yake nufi, bayan babu aunty da Raihan agurin, naga suma duk suna cikin family )_*. Gaisuwa aka shigayi, kowa saiji da imam yake, itakam kunyarsuma takeji, ta ce, "marwan yaushe dee...... Zata zo?. Aina San weekend d'innan saitazo, dan taji haushi kin dawo bata nan, murmushi iman tayi ta ce, ALLAH yakaimu lfy. Ya CE Ameen. Sun dad'e anan anashan hira, sannan suka koma 6angarensu. Suna zama wayar iman tahau wringing, takalli wayar. My sweet hafsy tagani, tasaki murmushi tareda d'agawa................... *_" kuyi hak'uri idan nadad'e INA typing wayar k'amewa takeyi"_* *luv u oll my fan's* *(((S)))...............2017* [8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *miya kamata nayi?* _6arna