← Book details Ban Saketa Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 49

Sashe 32

Ban Saketa Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Kaitsaye gidansu iman suka nufa Dan a can itama Xoxo ta kwana, mintuna kad'an suka fito harda Abbah da deeni, su Dr Isma'il suka fito suka kwashi gaisuwa a wajen abbah sanan yaymusu 'yar nasiha da Addu'ar ALLAH ya tsare.
Iman da Xoxo suka Shiga baya suma Dr Isma'il suka Shiga su deeni suna d'aga musu hannu.
Su iman suka gaishesu, cike da fara'a Dr Nabeel ya amsa, amma Dr Isma'il gaisuwar Xoxo kawai ya amsa yashare iman.
Ko ajikinta wai antsikari kakkausa, ita dama zai had'e ran harsuje Inda suka nufa hakan zaifiyimata dad'i, tunda suka shigo bai kalli Inda takeba ammafa yana satar kallonta ta madubi batareda ta saniba.
Tun bayan gaisuwa babu Wanda yasake cewa komai, da Alama iman da Xoxo ma barci sukeyi, Dan barcin bai ishesuba aka tasosu.
Jin shirun yayi yawa yasa Dr Isma'il lek'owa saiyaga Duk sunyi barci, ya ce, "kai sufa wad'annan barci sukeyi.
Aii gara suyi anjima manna maka tuk'innan zanyi Musha hirar soyayya.
Ashe zaka dad'a Baka shaba malam, dama ka ajiye wata soyayya saimun sauka kawai.
Tab wanan ganganne aii idankai anyi maka fu
skar shanu nikam Baka hanani.
'Yar dariya Dr Isma'il yayi batareda yayi maganaba.
Sunyi tafiya sosai wadda had k'arfe 12:47pm su iman suna barci abinsu, Dr Nabeel da Dr Isma'il suna 'yar hira ahankali.
Isarsu wani k'aramin gari suka tsaya, sai anan su iman suka farka, sunyi mamakin barcin da sukayi, bayan su Dr Isma'il sun fito sukace su iman suka fito, iman dai saifaman had'e fuska takeyi.
Wani gurin cin abinci sukaje, bayan sun zauna masu kula da wajen suka tanbayi mi sukeso, su Dr Isma'il suka fad'a, ya maida kallonsa Kansu iman ya ce, " mikukeso?.
Iman ta ce, "tak'oshi.
Dr Nabeel ya ce, " kinga 'yammata kawo mana iri d'aya kawai.
Bayan sunci sunsha suka mik'e wadda iman tacine kawai visa tursasawar xoxo, Dr Isma'il yabiya suka fito.
"Hanya suka k'ara d'auka bayan sunyi sallar azuhur".
Tunda suka fara tafiya abincin yake juyama iman, sai yatsine fuska takeyi, Dr Isma'il yana kallonta ta madubi.
Tafiya yayi nisa ha suka k'ara tsayawa sukayi sallar la'asar, sanan suka ci gaba.
Sosai iman takejin amai tana dannewane kawai, ruwa tad'auka tasha kozata samu a man datakeji Yakoma, amma INA lamarin k'ara ta azzara takeyi, candai ta ce, " atsaya zatayi amai, gaba d'aya kallonta sukeyi, Dan yanzu Dr Isma'il yake tuk'in, gefen hanya ya gangara.
Tun kafin yagama tsayawa tafita da gudu, amai tafara shek'awa, da Sauri Dr Isma'il shima yafito, ko motar bai kasheba sai Dr Nabeel ne yakashe.
Rik'e iman yayi tacigaba da aman, duk d'an abinda taci ta amayar dashi, saida tagama sanan yad'agota yana mata sannu, Dr Nabeel yamik'o MASA ruwa, da Kansa ya wanke mata bakinta da Inda tad'an 6ata ajikinta, duk tayi laushi so kawai take ta kwanta.
Xoxo ta ce, "sannu iman, agalabaice ta d'aga kai, Dr Nabeel ya ce, " kozamu koma bayan asamu k'yamis.
A'a mudaije gaba koza'a samu.
d'aukarta Dr Isma'il yayi cak yakai cikin mota, bayan shima ya zauna ya CE, Xoxo takoma gaba Inda Dr Nabeel yacigaba da tuk'in.
Kwantar da ita yayi yasaka kanta acinyarsa yana shafa fuskarta babu dad'ewa barci yay a won gaba da ita, ajiyar zuciya ya sauke yasunkuya ya sumbaci goshinta, tsurama fuskarta ido yayi nawani lokaci, saikuma ya kwantar da bayansa jikin kujera ya lumshe idanu.
Duk abinda ke faruwa Xoxo da Nabeel suna kallon ta madubi, Dr Nabeel yay ajiyar zuciya tareda d'an kallonta gefen Xoxo yamaida Kansa ga titi yana fad'in toke 6arauniyar zuciya INA muka kwana?.
Harararsa Xoxo yayi ta ce, "saika gayamin zuciyar Wanda na sata?.
Yayi murmushi tawa mana, duk kinbi kin wani sukukutani yakamata aji danifa, kafin na koma Romeo irin Isma'il.
Dariya abin yabama Xoxo Dan haka tadara.
Dr Nabeel ya ce, " ngd da aka kar6eni.
Ta kalleshi da Sauri waya gayamaka ka kar6u?.
Dariyarki da fuskarki.
Humm to Baka fahimta bane, abinda yabani dariya daban.
Haba 'yan mata aii kuma kinzo hannu matar Dr Nabeel.
Shiru Xoxo tayi masa shikam yacigaba da tsarata, _(aii ko kafin na farga har Xoxo ta afka, dama itama tanaso
lol.)_
Chapter 32 · 0% Book details