Sashe 40
Ban Saketa Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
NATA yawa a bayan k'asa, amma anrasa miye tushenta?._ _hummm akwai tushe tushema ba tusheba, misali idan na d'auki yanda al'ummarmu suka maida zina a yanzu._ _zakiga uba mai cike da kamala ariga da fuska, amma idan yaje office shida sakatariyarsa saidai addu'a, zai makad'awa matarsa k'arya yatafi k'asar waje kasuwanci amma yana hotel da 'yammata, k'ilama harda k'awar 'yarsa, ko k'awar matarsa, ko k'awar k'anwarsa._ _to jama'a Dan ALLAH, indai maganarnan da ake fad'in Wanda yayi zina da uwar wani sai anyi da tasa mizai hana matar magidancinnan fad'awa tarkon zina, tunda k'ila harda matar wani yakeyi, mizai hana 'ya'yan magidancinnan fad'awa zina, tunda yayi da 'yar wani, mizai hana k'anwar magidancinnan fad'awa zina, tunda yayi da k'anwar wani, mizai hana yayar magidancinnan fad'awa zina tunda yayi da yayar wani._ _kunga tadalilin mutum d'aya mutane dayawa sun fad'a tarkon 6arna, shikad'ai ya wargaza family d'insu, Dan abin zaita bibiyarsune har 'ya'ya da jikoki._ _wa'iya zubillah, Dan ALLAH magidanta kuji tsoron ALLAH kodan katange family naku fad'awa cikin bala'in fasik'anci, saimun gyara ALLAH zai gyara mana, sakawa 'ya'ya da k'anne sasari na hana Fita bazai hana ubangiji ya aiko wani k'ato har gidanka ya6ata maka rayuwar mata, 'ya'ya, k'anne, yayye, ba a yima ALLAH wayau d'an uwa._ *ALLAH yasa mugane* *(page 35 & 36)* Ayyeee mata kuk'ame k'am sabuwar rawa. Iman Doctor Ku k'ame k'am kusami nutsuwa......... Dariya iman tayi kai sisi ALLAH yashiryaki wlhy, ina kuma kika samo wanan wak'ar?. Hhhhh sabuwar wak'ar gwanja ce amaryar, k'amshi, ya amarci. Hummmm amarci kuma?. Eh mana. Yana wajenku. Tofa mu asuwa, haryau banbar kwana agadon Umma ba, aiiko bana amsa sunan amaryaba. Karki damu lokaci kad'an yarage kikoma kwana kusada....... Saikuma tayi shiru tana kallon Dr isma'il dayake kallonta. A'a yakikayi shiru fad'i mana, Xoxo tafad'a tana dariya. Iman takauda kanta daga kallo sa ta tashi tashige bedroom, 'yar duniya aiba kasa fad'a nayiba, doctor ne akusadani, kuma yakafeni da ido yanajiran mizan fad'a. Hehehe 'yammatan gaya ga k'yau ga gayu, kice soyewa ake nakira, bari nabarki sai anjima....... Kafin iman tace wani Abu Xoxo ta yanke wayar tana dariya. "ALLAH yashiryaki iman tafad'a itama cikin dariyar. Falo tayi yink'urin dawowa Dr yashigo d'aukeda musayeef dayayi barci, kad'an yarage suyi karo tad'anja baya. Saman gado yad'orashi sanan ya zauna, iman dake tsaye tana kallonsu cike da sha'awa tayi murmushi. Dr isma'il yad'ago yana kallonta, ya ce, " har angama gulmar?. gulma kuma?, gulmarwa mukayi?. Ya za'ayi nasani tunda kin gudo d'aki. Hu'um to ba gulmar kowa mukeyiba mudai. Murmushi yayi yana mai k'are mata kallo cikeda shauk'i.......garammm aka bugo k'ofa, da sauri iman tamatsa Dan k'ofar tad'an daketa kad'an. Auntyce da Raihan, iman taimusu kallo d'aya ta d'auke kai, Dr Isma'il yatashi zaune yana kallonsu. Shigowa sukayi cikin d'akin, (amamakin iman saitaga sun durk'usa ak'asa), tofa sabon salo iman tafad'a azuciyarta. Raihan ta ce, yaa isma'il Dan girman ALLAH kuyi hak'uri Ku gafarcemu, Dan ALLAH kabama Yaya hak'uri shima ya yafema auntyna wlhy tana bala'in sonsa. Wani kallo yakemusu, amma kuma bai fahimci zancen nasuba, baikuma tambayesuba. Itadai iman tana tsaye tana kallonsu. Aunty tajuyo tana kallon iman, iman Dan ALLAH kiyafe mana kema, munyi kuskure ki gafarcemu..... Tak'are maganar hawaye sunan sauna a kumatunta. Sumba iman tausayi Dan haka tabud'e baki zatayimusu magana, Dr Isma'il ya ce, "my life karkice musu komai. Shiru tayi tana kallonsa, yataso ahankali yakama hannunta, saman cinyarsa ya d'orata, dukda tanajin kunya haka ta dake ta zauna, yajuyo da fuskarta suna kallon juna. My life ke harkin yarda da tuban wad'annan shaid'anun?, sunefa masu kulla raba aure, abinda ALLAH bayaso, dukda bansan abinda Yaya yayiba nasan yayi dadai wlhy, banaso ko a mafarki kiyafema Wanda ya rabani dake NA tsawon shekara hud'u, wand'anda suka jawo na kwanta a asibiti natsawon wata uku, wad'anda suka hana zukatan dangina nutsuwa, nasan basuyi nadamaba Dan har yanzu basu riski makarantar nadamaba. Iman ta kad'an kai batareda tayi maganaba. Shikuma yadaka musu tsawa, wlhy koku fitarmin ad'aki kokuma kufuskanci mummunan 6acin rai daga gareni, wlhy na tsaneku banason ganinku, shaid'anu kawai. Sum sum aunty da Raihan suka fice, kowa zuciyarsa tana zafi. Suna Fita suka kalli juna sukai murmushi, aunty ta ce, " sakarkaru sunfa zata da gsk Neman yafiyar mukazo. Raihan tayi 'yar dariya bar kidahumai aunty. Aunty ta ce, "ina fata kin saka?, kinsan malam ya ce, " bayaso asamu Marsala ana farko. Nasaka aunty saura kuma nagobe, ai zasuci ubansune agidanan, sai sunyi Dana Sanin barinmu, aunty da Raihan suka ta6a tamkar wasu k'awaye. (Ni Bilyn Abdul na ce, "hummmm Dr Isma'il da iman kam rakasu sukai da ido, iman har zuciyarta ta yarda sunyi nadama, Amma Dr yanaji ajikinsa akwai abinda suke shiryawa, badaicema iman komaiba akan hakan saiyayi bincike. *bayan kwana uku* Bayan kwana uku da dawowar iman, kullum tana zubama Dr k'arya tana fashin Sallah, saiya Fita saitayi sallarta, shikam ko kad'an baikawo k'arya takeba a ransa. Yauma suna gama break yay shiri cikin watad'anyar shadda jaa yamurza bak'ar hula, iman natsaye tana kallonsa, saida yagama saka hular sannan yajuyo yana kallonta, murmushi sukaima juna, yamatsa daf da ita, my life nafa fara gazawa gsky. Kallonsa tayi tana murmushi ta CE, ''akan mi ka Gaza?. Akanki yafad'a yana rungumeta. Ajiyar zuciya ta saki batareda tace komaiba. Yad'agota daga jikinsa yana kallon fuskarta, ya ce, " bakice komaiba. Mikakeso nace to?.. Kicemin bak'onki ya tafi....... Kafin tabashi amsa musayeef da 'yan biyu suka shigo da gudu hannunsu d'auke da kayan sweet. Dr Isma'il yasaki iman yana kallon su musayeef. iye 'yan yara yara waya Baku?. Cikin tsalle sukace aunty deexerh ce. Kai ina aunty dee.... d'in?, tana wajen mama suka fad'a suna tsalle. Iman ta ce, "lallai dee.... Tana fushi damu, harta dawo babuko waya. Dariya Dr Isma'il yayi, ina bayanta tayi fushi sosai, kin dawo gidan uncle d'inta bata saniba, dama tagayamin kin shareta. aii laifi tamin shiyyasa na shareta. A to bari nayi shiru da bakina saikun had'u kenan. Dariya iman tayi. Ya ce, " bari nawuce ana jirana. Iman tad'an ta6e fuska towaima wanan kwalliyar ina ta dosane?. Gira yad'aga mata ya ce, "tad'i mana, kisan nasamo ta uku, iman ta had'e fuska sosai ta ce, to na mamajo saura ta hud'u. Dariya yayi danganin yanda ta had'e fuska, ya shafa fuskar tata yana d'aga mata gira, karki damu itama tana hanya uwargidana, baijira cewartaba yafice da Sauri Dan Dr Nabeel yana jiransa. Wasu hawaye suka zubo a kumatun imam itafa azaton da gsk yakeyi, bakin gado ta zauna zuciyarta na zafi. Deexerh dake tsaye tun d'azu tayi murmushi Dan taji zancensu na k'arshe, ahankali tak'arasa Inda iman take ta zauna. Imam tajuyo catake shine yadawo saitaga deexerh, Harar deexerh tayi tayunk'ura zata mik'e. Dasauri deexerh tarik'o hannunta sorry my aunty Dan ALLAH ki saurareni mana. Komawa imam yayi ta zauna, deexerh ta ce, " haba aunty na laifin mi nayi ake fushi dani. Hawaye imam tashare Dan haryanzu maganar Dr yana cizon zuciyarta, ta ce, "a'a deexerh Niba auntyki bace tunda har kika iya 6oyemin uncle d'inki yayi aure. Nasan dama komai dad'ewa kikaji labarinnan zakiyi fushi dani amma wlhy ban 6oye miki Dan wani abuba, danni ban d'auki Auren waccan sakaran a komaiba, amma kiyi hak'uri Dan ALLAH. Murmushi iman tayi, shike nan na hak'ura. Yauwa aunty na dee..... Tafad'a tana dariya, amma aunty nayi bak'inciki da ban nan randa kika dawo, amma marwan Duk yabani labari, nadad'e banyi farincikin dawowa gidan nanba kamar wanan karon. Dariya imam tayi kai dee..... Banda k'aryafa?, ALLAH kuwa aunty, saidai nadawo da d'ammarar cin uban shegunayennan, sai sunbar gidannan kwanannan. Imam ta zaro ido, kai dee.... A'a Dan ALLAH karkiyi musu komai, wlhy sunyi nadama ranarma saida sukazo Harnan suka bamu hak'uri. Humm aunty kenan ke har kin yarda da tubansu?, ni nace miki k'arya suke, nasan halinsu sosai Dan aunty dakike gani ba k'aramar shaid'aniya baceba, kemafa kin zauna da ita kinga wasu daga cikin halayenta basai nabaki labariba, ke ganauce ba jiyauba.. Hakane kuma imam tafad'a, haka dai iman da deexerh sukaita hira har aka kira sallah suka tashi sukayi. Bayan sun idar suka nufo fallo daniyar tafiya 6angaren mama, a fallo suka iske Raihan zaune tana kallo Dan yau takeso ta ida cika aikin malam so take kawai imam tafita ad'akinta taje ta aiwatar. Deexerh tasaki wani wawan tsaki tanabin Raihan da kallon banza, aunty yanzunan har kinyarda kowanne datti yazauna miki afalo?. Da Sauri Raihan ta kalleta dantasan da ita take, imandai batace komaiba, Raihan har zatayi magana saikuma tayi shiru, dee.... Tayi dariya mai bakin ja6a yakuma kika kasafad'a, fad'i maganarki karta kasheki. Iman taja hannun dee... Suka fice, kai dee.... Kibari Dan ALLAH matar uncle d'inkicefa kuma 'yar uwarki. Hummm wannan duk ada ne, ayanzu kam babu wata alak'a atsakaninmu, yanzuma tafara gaini Indai nice. Suna fita Raihan ta share hawaye, zanyi maganinki kema, baridai nagama da wad'annan sakar Karun, hankalinta kwance tanufi d'akin iman, katifarta tad'a tasaka wasu layu ko k'yan gani babu, tatsaya gaban gadon tana wani sirkulle. tana gamawa tajuyo zata Fita saifaman murmushi take Dan tasan daga yau imam tagama yawo. Turus tatsaya baki bud'e tanabin Dr dake tsaye da kallo atsorace. Takowa yayi cikin d'akin batareda yace komaiba, saida yaje gaban gadon sanan ya ce, "zoki cire abinda kikasamata agado. Jikin raihansai rawa yake tazo tad'aga tacire layun data ajiye, ya ce, " nasan bayau kika fara saka mataba d'ebo sauran ma, da Sauri taduk'a k'ark'ashin gado saiga wani kasko da da tsokar nama an cacccaka k'ayoyi ajiki. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Dr yaketa ambata, gaba d'aya zufa ta jik'e MASA jiki, waya ya d'auka yakira yayansa. Yaya kana kasuwane?. A'a isma'il INA gida yanzu babu dad'ewa nashigo. Yaya Dan ALLAH ka tattaro 'yan gidanan kuzo kuga abinda Nagani INA d'akin imam. Kagani kuma, minenen kagani??. Yaya saidai kunzo kawai. Raihan dai tana duk'e ak'asa da 'yan kayan surkullenta sai hawaye takeyi, shikenan aunty tak'ara sakata amatsala itakam tashiga uku, wlhy batason rasa Dr Isma'il Dan tana bala'in sonsa. Babu dad'ewa saiga gayyar 'yan gidan duka, kowa yashigo saiya rik'e baki, iman ta ce, "na Shiga uku ni saudatu wanan kuma daga INA Doctor?. Baiyi maganaba saidai nuna mata Raihan yayi. Jikake tauuuuu deexerh ta d'auke Raihan da wani wawan mari, shima