Sashe 38
Ban Saketa Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Ledar da Dr Nabeel yabasa yad'auka yanufi d'akin iman. Wasu hawaye suka wanke kumatun Raihan dake bakin k'ofa tana kallonsa, takoma cikin d'akinta dagudu tana kuka. Shikam dama baisan tanayiba yatura k'ofar iman ahankali yashiga, bakinsa d'auke da sallama. Wani k'amshin dad'ine yabugi hancinsa, yashak'a ya lumshe idanunsa, ahankali yabud'e ya saukesu akan iman dake kwance tana kuka, Dan shigowarsa saita k'arajin sabon kuka. Cikin takun nutsuwa yak'arasa gaban gadon, ya ajiye ledar ak'asa sanan yahaye saman gadon shima. Gabanta yaje ya kwanta yana fusakantar ta, da Sauri tamik'e zaune tana hararsa. Wani murmushin gefen baki yasaki, Wanda ya kashe zuciyar iman, taisaurin duk'ar da kanta k'asa Dan murmushinsa ya tsayar da hawayenta cak. Hannunta yakamo yarumtse anasa, Amincin ALLAH ya tabbata agareki my life. Bata tankashiba saima k'ok'arin zare hannunta takeyi. Bai bata damar hakanba, yakuma damk'e hannunta sosai Wanda yakejinsa kamar auduga dan laushi. Muryar iman can k'asa ta ce, "INA musayeef?. Murmushi yak'ara yimata yana murza hannunta, lallenta yaymasa k'yau sosai, muryarsa cike da salo ya ce, " gadai daddyn musayeef atare dake, musayeef kuma yana wajen mom d'in Deexerh. Shiru tayi babu amsa. Yatsunsa biyu yasa yad'ago ha6arta, sai kawai tamatso hawaye. Yad'an rintse ido yabud'e, ahankali ya ce, "har yau bakibar kukan rabuwa dasu gwaggonba ne?, yakamata kiyi shiru haka nan, tun amota kike kukafa. Aii kamar ya zugata saima ta fashe masa da kuka. Jawota yayi yarungume yana lallashi, my life please ya Isa haka, inko bakiyi shiruba nima zan fara miki kukan, yafad'a yana d'ago fuskarta. Yanda ya yamutse fusaka kamar yaro saiya bata dariya. Ta murmusa. Shima yasaki lallausan murmushi yana kallonta. Matsawa tayi baya tana turo baki gaba. Yagyara zamansa wauni gudunama akeyi kenan?, duk'ar dakai iman tayi tana wasa da zoben hannunta. Yakuma matsowa daf da ita ta matsa baya, ya matso tamatsa, suka dangane da jikin gado, murmushi yayi ya ce, " to munzo k'arshe sai Yaya kuma?. Kallonsa tayi da runannun idanunta datasha kuka, ta ce, "saina barmaka d'akin. Hhhhh duk Inda kikaje yau zan bikine aii. Mik'ewa tayi danufin barin gadon, yajawota tafad'o jikinsa, zobe yaymata da hannunsa yarungumeta tsam ajikinsa. Tafara mutsu mutsun kwace kanta, yakuma matseta, cikin kunnenta ya ce, " yaufa babu wata hanyar ku6ta Dan mak'ogwarona abushe yake da k'ishirwa. Tad'an kalli fuskarsa akaro na farko, wani shek'in angwanci taga fuskarsa tanayi, takawar da kanta daga kallonsa, jitayi zuciyarta tana wani zafi saboda kishi, aranta ta ce, "namiji munafiki. Yalura da canjin fuskarta, ya sumbaci yuyanta dake wani tashin k'amshi mai rikitashi, my life baki yarda da maganata bane?. Baki ta ta6e tana k'ok'arin tashi, yazanyi na yarda bayan kaima Kasan ba haka bane, harma mai amarya yayi k'ishirwa. Hannunta yaruk'o Dan harta mik'e daga jikinsa, ta kauda fusakarta data jik'e da hawaye. Dawo da ita yayi saman cinyarsa, yajuyo da fuskarta suna fuskantar juna, saita rintse ido tana k'ara zubo da hawaye. " aransa ya ce, "kishi". Afili kuma saiya huro iska daga bakinsa, yana hura mata akan idonta, nan take hawayen suka tsaya, kafin ta bud'e ido ya had'e bakinsa maicike da k'amshi danata, sannan yaymata k'yak'yk'yawar runguma wadda babu maganar kwacewa................... *_hummmm masu karatu........... Baridai na shiru kawai *luv u oll my fan's* *(((S)))..........2017* [8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *_"wanga page nakine k'anwa Marak'isiyya alkairin ALLAH yakaimiki, nayi missing naki sosai, yakamata kidawo haka nan"._* *(page 33 & 34)*