Sashe 37
Ban Saketa Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tashin hankali kam, Dan yanzu babu mai kulasu agidan, sunzama tamkar mujiyoyi, yaya ma dayake mutumne mai zuciya, haryau baicema Aunty komaiba, ammafa yadaina Shiga d'akinta, baya amsa gaisuwarta, ko kallo bata isheshiba dama yagaji da mugun halinta, idan yashiga 6angarensa yaganta afalo zaune d'auke kai yake kamar bai gantaba, idan tashiga d'akinsa ya korota. (Tashiga tashin hankali, gara ace yazaunar da ita yay mata masifa akan shareta d'in dayakeyi yanzu). Suna zaune itada Raihan sun zabga tagumi. Raihan tashare hawayen dasuka cika mata idanu, aunty yanzu yakike ganin zamuyi, nifa wlhy har yanzu inason ya Isma'il, gashi yanzu yace ko shigowa yayi yaganni afalo wlhy saina gane kurena, kina ganin yanzu andaina cin abinci damu, babu mai mana magana agidanan, aunty kinsakamu amatsala munshiga uku mukam, munzama mujiyoyi. Aunty ta ce, "humm Raihan kenan, nifa d'azu marwan marina yayi wlhy,. Marifa kikace?, marwan d'in?. Wlhy kuwa Raihan, kuma babu damar ramawa bare nad'au wani mataki, nifa sonake kawai Mansur yasakeni. Kai aunty kidaina manager fatan saki wlhy, k'ila nangaba su hak'uri, kinsandai zaman sokoto d'innan bawani dad'i bane, ko abincin arzik'i babu. Nima abinda nake hangowa kenan Raihan shiyyasa d'azu na k'yale marwan. Mucigaba da hak'uri akan duk abinda ZAMU gani watarana sai labari aii. Shikenan ALLAH yabamu ikin jurewa. *(ni bilyn Abdul na ce, " humm, jurewar nan dakamar wuya, musamman idan Deexerh tadawo, ah ah ah,)* Marwan ya Sanar da deexerh komai Dan haka tak'agara su gama Exam ta taho gida, ita kad'ai tasan muguntar data shirayama k'ananan 'yan iskannan, gashi takira wayarsa Iman akashe, Dan haka ta hak'uri tabar komai saitazo gidan. Iman kam tanajin gyara wajen ummansu Xoxo, aunty Salma tana aikawa da nata agefe, itamadai gwaggo tana bada gudummawa sirrinsu na manya, Xoxo da iman ma suna 'yar tasu fasahar dasuka sani, _(nace humm zafa Ku haukata Dr Isma'il)._ Shi hankalinsama atashe yake, Dan saikiran wayarta yake akashe, arikice yazo gidansu gwaggo ta ce, "aii batanan, d'aukar Musayeef yayi suka yafi gidan aunty Salma, nanma akace MASA batanan,. Aunty pls.... Karku haukatar dani Dan ALLAH tana ina?. A'a k'anina bazaka haukaceba, iman sunyi tafiya da hafsat, amma insha ALLAHU zasu dawo nanda kwana hud'u. Aunty nanda kwana hud'ufa kikace, randa iman zata koma gidana. Hakane insha ALLAHU. Kai Dr Isma'il yadafe, yana fad'in wayyoni ALLAH na. Aunty tayi dariya, to kwana hud'u aii kamar yaune insha ALLAHU, daga nan ba kayarka za'a maida makaba. Dariya ya Majeed yayi, kai abokina kadafa kayimana kuka wlhy, irin wanan damuwa haka, idan sak'one kawo nabata. Dr Isma'il ya hararesa, aii nama lura hardakai aka kulla 6oyeta. Hhhhhh yanzu kuma kaina zaka dawo, to bazadai mu bayarba sainan da kwana hud'u. Tashi Dr Isma'il yayi yasa6i musayeef dayayi barci akafad'a, aii shikenan zan rama Nima, nabarku lfy. Dariya sosai aunty Salma da ya majeed suke masa, shima Fita yayi yana dariyar. *RANA BATA K'ARYA* yaune wa'adi yacika, tunda sassafe akadawo da iman gidansu, gwaggo sai latsa jikin iman takeyi cike da mamaki, iman kin canja mi umman hafsat d'in tarink'a bakine haka?, kai ALLAH yasakama wanan baiwa da Alkairi, ALLAH yasa munada Rabon ganin bikin hafsat haka. ( Na ce, "amin gwaggo). Dukda Dr ya ce, " kar a kaita da komai, saida aka k'ara siya mata kayan kicin Nagani na fad'a, ga d'inkuna sababbi cike da akwati da aunty Salma da ya majeed sukai mata, ummansu Xoxo ta had'a mata turarirrika masu sirrin k'amshi, najiki na d'aki nagashi na kaya, kai lamarinfa sai godiya. *_8:00pm_*................ *luv u oll my fan's* *(((S)))...........2017* [8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *miya kamata nayi?.* _kizama mai kamunkai, wlhy 'yammata iskanci baida wata riba, babu abinda yakai budurci daraja ajikin 'ya mace, shin miye ribarki idan kin rabama guys naki a titi?._ _randa kikayi aurefa akwai Matsala wlhy, duk d'an isaka baya son auren 'yar uwarsa 'yar iska, burinsa yasamu nitsatstsiyar mace kamila ya aura, kinga wanan kawai ya Isa ya nuna miki kin fad'i babu nauyi, idan aure kikeso karkiji kunya kisanar da iyayenki, idan bazaki iyaba samu wani a 'yan uwanki kisanar masa yasanar da iyayenki, wanan rashin kunyar tafi sauk'i akan kizubar da darajarki awajen wani sakarai Wanda baisan muhimmancin budurcinkiba, 'yar uwa tattali abinki kikaima mijinki domin yasaka ranar farkonku acikin muhimman kundin tarihinsa, duk mijin da matarsa takai masa budurcinta bazai ta6a mantawa da wannan k'yautarba har k'arshen rayuwarsa._ _wallhy 'yar uwa gsky nake gayamiki budurci mutunci, kuma, nagarta, donk'on so, tattalin so, k'auna ta musamman yake jawowa gadukkan macan data kaima mijinta._ *ALLAH yasa mugane* *(page 32)* *_8:00pm_* kowa yagama shiri za'akai iman, gayyace guda y'an rakiyya, Dan Matan anguwar dayawa sunshigo Dan rakiya abin kamar wasa. Xoxo dake kusada iman zaune sun gama waya da Reefat sun bata labarin komai tanata murna, kira yashigo wayar Xoxo, takalli wayar tana murmushi Dan wringing na musamman tasaka masa, itadai iman sai binta take da kallo kawai, ga zuciyarta taf da fargaba. Assalamu alaiki gimbiyata. Wa'alaikassalam sarkina. Dr Nabeel yay murmushi tamkar yana gabanta, ngd sosai dasamun sarauta, amma haryau baku maida mana amaryarmu bane? Tab aii wanan amaryar ta gskce, saikunzo da motama, 'yan rakiya fal gida. Kai haba?. ALLAH kuwa. Ku sauraremu gamu nan zuwa, kafin tace wani abu ya yanke wayar. Iman ta ce, "karfa ya d'auka gskne sisi. Oh keda wasa kika d'auka, kina ganin idan basuzoba saidai wasu mutanan suhau keke napep fa. Iman ta ta6e Baki, kenifa daza'a fasa zanyi murna. Dariya sosai Xoxo takeyi, haba 'yammata babu fashi yau saimun kaiki, ak'irjin Daddyn Musayeef zakiyi barci. Duka iman takai mata ta kauce tana dariya, wlhy hafsy ke 'yar sikace, amma Dr Nabeel zaimana maganinki, kamar yanda yaa usman yay maganen Reefat. Xoxo tamik'e tana fad'in Ashe za'a dad'e ba'ayi maganin nawaba....... Sallamar aunty salmace ta k'atse Xoxo, tamik'ama iman kaya, kinga tashi ki shirya abbah sai fad'a yakeyi. Iman takar6a tana turo Baki haba nikam naga takaina yau. Bakiga takankibama sai anjima aunty Salma tafad'a tana Fita. Dariya Xoxo tasaka, harda yima iman gwalo gsky ne auntyn mu, sai anjima zataga takanta. Iman tamik'e tanufi Xoxo, itakuma tafita da gudu, zan kamaki aii humyim. Xoxo tak'arasa inda aunty Salma take, saitin kunnanta ta gwargwad'a mata magana. Aunty Salma tayi dariya dgsk hafsat?. Wlhy kuwa aunty suna k'ofar gida, hannu aunty tabata suka ta6a, shiyyasa nakesanku 'yan k'annena kanku akwai kawo haske Xoxo tayi dariya, aunty aigara muje musu ashirye su tabbatar wa mak'iya da gsk mukeyi. Tafawa suka sakeyi, ALLAH yamiki albarka k'anwata, yakaimu naki da Dr Nabeel. Da Sauri Xoxo tafita tana dariya, dansu ummanta suna gurin, itama taxo za'a raka iman da ita. Aunty Salma ta ce, "to jama'a ga motoci ankawo yakamata muyi harama. Kowa yamik'e akayi waje, aunty Salma tashiga ta Tatar Xoxo ta gama d'aurama iman d'ankwali, kwalliya sosai Xoxo tamata dukda bataso amma Xoxo ta dage saida tayi mata, tayi k'yau kamar wata aljana, _(nikaina mace saida na k'yasa )_.. Kamar wasa saiga iman tana rabzar kuka, gwaggoma kukan takeyi, ahakadai aka lalla6a akyo waje da iman. Dr Nabeel ya kalli Dr isma'il dake cikin mota zaune, bayaso agansa, ya ce, " Alhaji aii yau kad'auka sabuwar amarya za'a kaimaka. Murmushi Dr isma'il yayi yashafa sumar kansa datasha aski da gyaran fuska, "o, kaida mika d'auka za'a kaimin?. To kamabar wani tunani amarya gal aleda za'a kaimin. Nabeel yay dariya, cikin musayeef kuma aruwa tasha ko?. Rankwashi yabashi akai, to d'ansa ido koma ya akayi ina ruwanka...... Kafin Dr Nabeel yay magana su Xoxo suka iso rik'e da hannun iman daketa shashshekar kuka. Nabeel yabud'e musu suka Shiga, shima yashiga yatada motar, shiru Dr isma'il yayi Dan bayaso agane dashi akazo, amma tuni k'amshin turarensa yacikama Iman hanci. Bata kawo yana motarba, azatonta motarsace shiyya turaren Yakama motar, har lokacin shashshekar kukanta takeyi. Dr Nabeel ne gaba, mota biyar ta 'yan rakiya suna binsa abaya. Tunda suka shiga cikin gidan suke rangad'a gud'a kamar ankawo sabuwar amarya, ananma gidan cike yake Da makwafta, Dan tarba tamusamman mama da mom suka shirya musu. Yauma tarihi ya maimaita Kansa, saida aka fara kaita 6angaren mama, mama ta rungume iman tana hawayen dad'i, itama iman kukan takeyi,, an dank'a amanar iman a hannun mama akaro na biyu, wanan karonma mama ta kar6i Amanna tareda addu'ar fatan alkairi ga iman, sannan tabada k'yauta abama iman wadda babu Wanda yasan komiye aciki. d'aukarta akayi daganan har 6angarensu mom, itama dai amanar iman aka bata itada Yaya, suma sun kar6a. Su aunty dai anzama 'yan kallo, bak'inciki fall ransu saidai babu damar koda tarine mai k'arfi Daga nan 6angarenta aka kaita, tofa anafa kallo yakoma sama. Jar ubancan kai, kai masu karatu, kunga wani sabon salon gyara da akayima 6angaren kuwa?, hu'ummm nabaku dama kutambayi Xoxo labarin tsaruwan da 6angaren yayi 'Yan rakiyadai sunata tofa albarkacin bakinsu, har tsakkiyar gadonta aka kaita, gadone na alfarma, mai musalta muku tsaruwarsa sai Xoxo dasuka kasance amara kirjin biki, lol. Bayan 'yar nasiha da aka k'arayima iman, 'yan rakiya sukayo waje, umman su Xoxo kawai aka bari ad'akin da aunty Salma, Umma ta koro Xoxo waje, fitowa tayi tana zum6ura Baki, mumadai ankusa daina korarmu idan za'ayi wanga zance, shiyasa Zarah Bukar ta ce, "bata zuwa rakkiyar amarya da manya, Ashe da gskyarta. Tana tsaye tana kunkunai Dr Nabeel ya iso gareta, humm wanan bayajin kunyar gamo da Umma ne. Abubuwa su Umma sukabama iman, wasuma suna d'akin tashiga bayi tayi amfani dasu, aka bata wasu tasha, sanan suka fito, itakuma taja filo tarungume tana kuka. ALLAH yasa Musayeef yazo yanzu, Dan ita rabonta dashi tunkafin taje gidansu Xoxo, yau data dawo akace yana nan gidan. Bayan kamar minti15 gidan yay tsit, kowa Yakama gabansa, taso Xoxo tashigo su k'ara yin magana, amma Umma ta korata. ************************* Har k'arfe goma Dr isma'il bai shigoba, itakam bata daina kukanba, Dan ita azatonta yana wajen Raihan, datayi shiru ta kalli agogo saita k'ara fashewa da kuka. Dr Isma'il kam yana d'akinsa kwance, yama rasa irin murnar dazaiyi, tashi yayi yay wanka yashiga gyaracan goge can tamkar wani mace. Yarasa kayan barcin dazaisa, candai idonsa yatsaya akan wasu fararen kayan barci masu taushi, wandone iya gwuywa da riga mai bud'ad'd'en k'irji, yabaza turare na d'aukar hankali.