← Book details Ban Saketa Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 49

Sashe 47

Ban Saketa Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan d'aurin aure hidimomi suka cigaba da gudana, Dan 'Yar bidi'ar nan saida aka d'ana, muntaka rawar ak'ame k'am, munci rangam da ruwan roba, harda lemon gwangwani, kai munfa Shana abikinga wallah.
Bayan hidimomi da 'yan bidi'oi aka mik'a amarya Xoxo d'akinta cikin tangamemen gidanta na alfarma, tasha kukan rabuwa da ummanta da Abba harda 'yan k'annenta.
Zuwa k'arfe tara kowa Yakama gabansa sai k'awayen amarya mafi kusanci aka bari, zuwa k'arfe tara da rabi gayyan anguna suka shigo akasha shafta da nasiha ga ango da amarya kowa Yakama gabansa aka barsu cikin aminci.
Dr Isma'il yad'auki iman d'insa sukai gida harda Reefat, Dan sai jibi zata wuce.
Gida tsit kamar bai tara mutaneba daga Ango sai amaryarsa.
Dr Nabeel yana gaban Xoxo yak'ura mata idanu kamar za'a kwace masa ita, itakam tayi k'asa da kai cike dajin kunya dakuma kewar gida da fargabar sabuwar rayuwa.
Yasa hannunsa yad'ago fuskarta datasha kwalliya sai k'yalli take.
Ta lumshe idanu Dan bazata iya had'a ido dashiba, yay murmushi mai sauti yana cigaba daraba ido afuskarta, 'yammata yau babu tsiwa ko, anrufe bakin magana ruf.
Itadai Xoxo ko motsi batayiba, ahankali yamatsar da bakinsa Kusada NATA, sunajin saukar numfashin juna, magana k'asa2 yace tunda bakin arufe yake bayan su isma'il sun siya, nima bari nayi nawa siyen bakin, kafin tayi wani yunk'uri ya......... Hum baridai nayi shiru, (Tawan saida safe nabarku lafiya asha amarci k'alau
*_Washe gari_*
Na ce, "bari nad'an lek'a muku amarya, wajen misalin k'arfe 12 nashiga gidan, a get nagamu da gayyar mutane sun fito daga gidan, da'alama bak'ine masu tafiya sukaga d'akin amarya.
Nidai bayan mun gaisa na ra6a nashige, afalo na iske mutanen gidan, Xoxo kwance tayi fillo da cinyar Dr Nabeel, hannunsa na shafa gashinta ahankali, itakam ta shagwa6e fuska wai barci takeji.
Ya sumbaci goshinta yana murmushi, aidole kiji barci my hafsat Dan jiya kin....... Da Sauri tarufe masa baki da lallusan hannunta plzz nidai karka fad'a ga bilyn Abdul nan tsaye, yanzu saita iya sambad'awa ashafin littafi nikam gsky banaso.
Yacire hannun yana 'Yar dariya to shikenan nafasa fad'a aii, yamik'e tareda d'aukarta kamar wata baby yay bedroom yana fad'in ALLAH yasa kada wani bak'o yasake zuwa subarmu musha barcinmu.
Tsuru nayi tamkar munafuka, to masu karatu tunda sungudu Nina aii saina kama gabana (nimafa soyayyarna inada gwarzona agida, to aii gwara na lalla6a gurin kayanaba
Yauda gobe kayan ALLAH, su Xoxo anashan amarci kamar babu gobe, tayi k'yau bul bul da ita, alamomin jin dad'i sun k'ara bayyana sosai atareda ita, wanan kad'ai ya Isa yanuna Dr Nabeel yana kula mana da ita sosai.
Suna shan amarci kam,
yayinda iman taketa fama da laulayin ciki, Wanda tunda oga Isma'il yagane yaketa faman murna, jiyake tamkar ya had'iyeta Dan dad'i, sai kaf kaf yake da ita.
Hummm xoxo mafa kamar ansamu, Dan naje gidan daga fara gaisuwa naga tayi bayi da gudu sainajiyo yunk'urin amai, lallai Dr Nabeel mai sa'a ne, lol.
A6angaren Reefat ma dai cikinta harya fito abin gwanin sha'awa, ya usman yanaji da ita, ana shan soyayya kamar babu gobe.
Ana cikin haka makarantarsu takoma daga yajin aiki, haka suka tarkata suka koma makaranta kowa da k'aramin cikin, aiiko anashan shafta, idan weekend yazo mazansu suzo su kwashesu kowa yasha soyayya da matarsa.
Agida iman tabar musayeef hannun mom, bai damuba tunda yasaba dasu dama.
Bikin deexerh yanata matsowa Dan haka aka fara shirye shirye yanda yakamata.
####################.
Su aunty madai yau cikin hikimar ALLAH suka samu ku6ta daga hannun su zuby, anzubasune amota za'a kaisu legos Inda tushen k'ungiyar take, sukai had'ari ahanya, dayawan 'yan k'ungiyar sun mutu yayinda masu taimakon gaggawa suka ku6tar dasu Raihan, babu 6ata lokaci aka kaisu asibiti, yayinda hukumar 'yansanda tayi bincike aka gane 'yan ta addane abakin d'aya daga cinsu zuby Wanda bai mutuba, ram akayi dasu zuby dasauran 'yan k'ungiyarsu dake Legos, dama k'aramar k'ungiyace basuda wani fawa yanzu suke kafata shiyya suka baza group ta WhatsApp, to ALLAH ya kiyaye gaba.
Bayan su aunty sunsha jiyya a asibiti harna tsawon watanni biyu aka sallamesu tareda damk'asu hannun iyayensu.
Sunsha kuka da nadamar rayuwarsu, sun k'ara gane zancennan na hausawa dakance idan zaka Gina Ramin mugunta ka ginashi gajere Dan bakasan wazai afkaba.
Sud'inan da da suka Shana ga k'yau ga dama amma yanzu sune suka koma jemai jemai duk kamaninsu sun canja sunyi bak'i sun kod'e kai babu gashi, ALLAH ya yafe musu suma suzama mutanen kirki kamar kowa haka suke fata.
Lokaci ya shura sosai, gasu iman sun sami nasarar mammala karatunsu, zuwa yanzu cikinsu duk sunfito suduka ukun, Reefat ma tana gangarar haihuwa, Dan cikinta ya tsufa sosai haihuwa koyau ko gobe, dak'yarma ta iya kammala exam d'in.
Sunsha kuka lokacin rabuwa, su iman sukayo kano Reefat tayi Adamawa da alk'awarin data haihu zasu zo.
Sumadai akanon kowa gidanta mijinta yawuce da it a cike da farinciki.
Musayeef yayi murnar ganin aunty maa d'insa, yak'ara girma shima yayi tsawo sosai babu laifi, walima sosai Dr isma'il da Dr Nabeel suka shiryawa Matan Nasu na murnar kammala karatu lfy, to ranarmadai mun karya k'ashi aradu.
Bikin dee.... Ya kankama su iman duk sunzama busy, ga cikin ga hidima, hakadai tadaure tanata kai da kawo saboda mom Tanama iman kara, komai aka nema irin na uwa saitace aje wajen iman, hakama yaya ya mik'a ragamar komai ga Dr isma'il, shiyyasa bikin yazama Nasu iman.
Ina k'ok'arin shiga 6angaren iman Inda amarya da k'awayen ta suke, bayan mun gaisa da iman da Xoxo dake tsaye suna shawara akan walimar gobe idan ALLAH ya kaimu, saiga wasu mata su biyu.
Daga iman har Xoxo dani bilyn Abdul tsayawa mukayi muna binsu da kallonta mamaki...........
Tofa masu karatu kosu waye wad'an nan mata oho, muhad'u a page nagaba danjin su wanene??????..............
*luv u oll my fan's*
*(((S)))........2017*
[8/6, 6:04 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*
*_NA Bilyn Abdul_*
_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*
https://mrsbilkisa.blogspot.com
*_gaisuwa da fatan Al'kairi gareki Ayusha muh'd, ya mura?, kisaurari zuwan gasassun kaji Dan sune maganin murarki, masu yaji za'a kawo miki
*```{zuciya, kowa da irin tasa}*```
Acigaba da gashi
*_(page 47 & 48)_*
Ba wasu bane face Raihan da aunty, kallo d'aya zaka musu kagane sun fita hayyacinsu, wai sund'anyi k'yauma akan sanda aka kwatosu.
Xoxo tayi k'arfin halin cewa wad'annan kuma daga INA?.
Iman ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsu, idonta tuni yacika da kwallah, muryarta ad'an sark'e ta ce, "su Raihan ne.
Raihan kuma?, wai kina nufin kishiyarki?.
Kai iman tad'aga mata tana share hawaye.
6angaren mama suka nufa Dan basu kula dasu imanba.
Xoxo tad'an tallafe cikinta daya fito sosai.
Kai iman yunwafa nakeji.
Iman tayi 'Yar dariya, sisi gsky Nabeel fa, babynmu nasaki cin abinci dayawa.
Hummm kifita batun hayatee shi bai iya komaiba sai sheri wlhy, amma zan ramane saina haihu.
Iman tayi dariya, Ashe zaki dad'e baki ramaba, idan kika cika mana Baki, bayan sati uku da haihuwa saimu Baki wani babyn.
Ido Xoxo tazaro kai wanan fatan tsiyarfa daga INA?, aii tunda kikace haka gida zani wanka.
Dariya sosai iman take mata, suka koma ciki Inda k'awayen dee.... Suke anata shafta, amarya dai tana gefe ana mata k'unshi, duk bakinnan na dee.... Yau yayi tsit, na ce, lallai aure manya.
Xoxo ta d'an ta6a dee.... Datayi shiru tana kallon mai k'unshi kawai, haba amarya lfy dai ko?, naji yau duk kinyi wani sanyi mike faruwa?.
Numfashi ta sauke tareda yamutse fuska, ALLAH ni jinake kamarma afasa, nifa dukma auren yafita raina.
Dariya iman da Xoxo sukayi, iman ta ce, " haba my dee.... Ina son umari ya mak'alene?.
Wlhy aunty yana nan, ammafa ni duk tsoronma auren nakeyi.
Teema ta shek'e da dariya, 'Yar iska deexerh Ashe zakiji tsoron aure, sanda akayi bikina babu irin sherin dabakiminba, kema gashi yau yazo kanki, su Ikilee ma baki yamutu.
Harara dee.... Ta sakar mata, amma batace komaiba saidai idonta yacika taf da kwallah.
Iman ta rungume kanta tana lallashi damata magana mai dad'i.
(Ni bilyn Abdul na ce, "dee.... Yau ina zumud'in??)
Haka biki yacigaba da gudana cikin far in ciki, su aunty sai 6oyewa sukeyi dankar mutane su gansu, amma sun makaro Dan dayawa angansu sai kallonsu ake da zind'ensu.
Kai iman wlhy nagaji sosai, anya zan iya zuwa dawuri gobe idan ALLAH ya kaimu?.
Haba sisi na zaki iya wlhy, kinsandai kece abokiyar shawarar tawa, karki damu dakunje gida Dr zai k'ara gasa miki jikin da ruwan zafi, harma da tausa, tak'are maganar da d'aga gira.
Xoxo ta ce, "hummm kokuma yak'ara taramin gajiya ba.
Dariya iman takeyi, cikin dariya ta ce, " toya muka iya tunda ALLAH yabamu masu hali d'aya.
Kibari kawai iman, keni wlhy idan nagaji kuka nake saka masa, ga wanan kayan anlik'a mana, amma baza'a barka ka hutaba, danma momy ta turomin su maimuna da Ayeesh sunad'an ragemin wasu aiyukan, aidanaga banu, wlhy dayaga shagwa6a salo salo.
Hhhhhh nasan zaki iya sisina aii da wanan shagwa6ar kike k'ara rikita mana Dr Nabeel.......
Sallamar Dr isma'il ce tasa iman yin shiru, ya ce, "nashigo?.
A'a karka shigo iman tafad'a cikin tsokana.
Yad'aga labulen yashigo yana murmushi, aii saina koma cikin k'awayen amaryarnan naza6i d'aya, kinga gobe idan ALLAH yakaimu sai a d'aura auren baba da 'yarsa.
Cikin dariya Xoxo ta ce, " dakun kafa tarihi kuwa.
A'a hafsat kadafa ayi kuzo keda k'awarki kuna zanemin mata, yafad'a yana kallon iman data had'e fuska.
Kasan kuwa tsaf zamu iya.
Tokin gani, aii gwara na hak'ura na lalla6a da 'Yar saudat d'ina.
Iman ta harareshi.
A'a yi hak'uri gimbiya.
Xoxo dai dariya take musu, yamik'e yana fad'in hafsat Nabeel fa yazo d'aukarki.
Yauwa wlhy dama shi nake jirafa.
Har k'ofar gida suka rakata Inda Dr Nabeel yake tsaye yana jiranta, suna fitowa yanufosu, hannun Xoxo Yakama tareda rungumota jikinsa, wayyo ALLAH my Angel nasan kin gaji sosai ga babyna.
Xoxo ta wani narke masa jiki, ALLAH bakaji yanda nakejiba hayatee.
Tokodai na d'aukekine kawai..
A'a.
Dr Isma'il yay dariya, abokina kaimafa bakada dama.
Awajenka na koya aii, ko iman?.
Dariya iman tayi batareda ta ce, "komaiba.
Sukuma suka Shiga mota iman nak'ara rok'on Xoxo akan tazo da wuri Dan ALLAH gobe, tunda daga gobe shikenan.
Chapter 47 · 0% Book details