← Book details Ban Saketa Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 49

Sashe 44

Ban Saketa Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kwantaina da mutane dayawa ke cikin, tsirara duk jikin su wani iri babu k'yawun gani, su tsoroma suke basu, Dan haka suka raku6e waje d'aya suna rabzar kuka. (Nace duniya makaranta, Wanda baizobama jiransa takeyi). Kowa yagina Ramin mugunta........ **************************** Iman da Dr kam ansha soyayya, daren nan zir a angwaci suka cinyeshi, iman ta murzu, Dan Daren jiya Sabon Daren farko Yakoma musu. Wanan karan dai babu kuka amma yasha shagwa6a da ta6arar iman, da k'yar suka tashi sukayi sallar asubar, suka sake bud'e sabon babin barci. Sai shabiyu dawani Abu suka tashi, alokacin tuni musayeef ya tashi yay tafiyarsa 6angaren su yaya. Imam ta tashi da k'yar, fuskar Dr ta tsurama idanu, barcinsa yake amma tamkar yana murmushi, fuskarnan fayau sai hasken angwaci yakeyi, talumshe idanu tasake bud'ewa akansa, tana k'aunar Dr harma batasan iya adadin k'aunar datake masaba, tana fata ALLAH ya sa babu wata k'addara dazata sake raba rayuwarsu anan gaba. Ahankali tamik'e tanufi bayi danyin wanka, Dan jikinta sai ciwo yakeyi wlhy. Ruwa mai zafi ta had'a ta gasa ko INA najikinta hartaji d'an k'arfi. Tafito d'aure da tawul tana goge jikinta da k'arami, Dr dake kwance yatsura mata idanu jiyake tamkar ya had'iyeta saboda so, tunda yake baita6a tunanin yaso wani Abu bayan iyayensa da mama da ya'yaba bayan IMAN, yanajinta sosai azuciyarsa, fatansa ALLAH ya tsawaita rayuwarsu suci amfanin juna. Iman dabatasan yanayiba ta k'arasa jikin madubi tayi kwalliya mai sauk'i, durowa tanufa, tad'akko wata dakakkiyar shadda zani dariga, ta d'aura zanin, tana k'ok'arin saika riga suka had'a ido da Dr da idonsa yake tsaye kam a k'irjinta ko k'yaftawa bayayi, da sauri tasaka rigar tana fad'in daddy katashi?. Bai amsataba baikuma daina kallontaba, d'ankwalin kayan tad'auka tak'araso Inda yake tareda rankwafowa ta hura MASA iska a idonsa. Ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya. Ta ce, ''kallonfa?, aii saika karemin muni Dr. Murmushi yayi tareda ziro k'afafunsa k'asa, yakafeta da idanunsa yana fad'in, aii kozan shekara dubu INA kallonki bazanga muninkiba. A'a daddyn musayeef banda zigadai. Tasowa yayi yarungumeta tabaya, yad'ora Kansa saman kafad'arta suna kallon juna tamadubi, ahankali ya CE da gsk nakeyi Ni'imatullah. Cike da mamaki take kallonsa ta ce, "wanan sunanfa daga ina?. Saitin kunnenta yamatsar da bakinsa ahankali yarad'a mata maganar danima banjiba masu karatu. Ta zaro ido waje saikuma tasa hannu tarufe fuska tana fad'in nidai babu ruwana kaje kayi wankanka. Dariya yayi yana k'ara matseta ajikinsa, nikam da ruwana harda d'an tsaki tsaki. Dariya tayi, nidai kaje wanka Kasan musayeef zai iya shigowa d'akinnan akowane lokaci. Da sauri yakalli gadon, o, wai yana INA?. Hummm sai yanzu kalura baya nan?. ALLAH nazata yana barcine. Tab wanan yaronne zaikai sha biyu dawani Abu yana barci?, Nima tunda natashi ban ganshiba. Musayeef sarkin wayo kenan, shiyyasa dole NASA agyara MASA d'akinsa azuba komaiba Yakoma da kwana can. Aiigara dakayi wanan tunanin da anka, Dama INA niyar yin magana. Dariya yayi yanufi bayi yana fad'in to an hutash sheki. Bayan Dr yafito daga masallaci yanufi 6angaren mama Dan iman tanacan suna shan hirarsu itadai deexerh. Deexerh nabata labarin Umar farukh, iman ta ce, " amma dee.... Miyasa bazaki bashi Dama yazo gidaba Dan asan dashi. Wlhy aunty inajin tsoro, shima kullum nacinsa kenan, sau biyu yana kaimin ziyara amakaranta, yanzu haka yana fushi dani akan nak'i had'ashi da uncle. Kai amma dee.... Bakida kai, ke Matan na Neman mijin aure ido rufe ke kina zillewa bayan kin samu, kobak'ya sonsane?. Wlhy aunty INA sonsa kawai inajin tsoron kamar yanda nafad'a miki. Tsoron kuma?, tomiye abin tsoron anan?. Kinsandai uncle yanada sauk'in kai amma bazan iya tunkararsa da wanga batuba, shiyyasa na CE, "farukh yatsahirta harna kammala makaranta. Cabd'i Jan, tsaya kallon ruwa kwad'o yaymiki k'afa 'yammata, yanzu idan ansamu tattali ake. Ni kibar komaiba ahannuna zan Sanar da daddyn musayeef, shima Umar d'in kisanar dashi yashirya zuwa bayan na Sanar da Dr saiya saka MASA ranar zuwa. Waye kuma? Dr dake shigowa yafad'a. Atare suka kalleshi, yazauna kusada iman, dee.... Tai saurin tsungunin iman wai kada tafad'a yanzu. Dariya iman tayi ta ce, " zan Sanar maka amma ba yanzuba. Okey ko yaushene INA saurarenki. Daga nan suka d'ora hira, har marwan yadawo daga makaranta mom ma tashigo akacigaba da hira mai dad'i irin ta 'yan family d'in dasuka shak'u da juna sosai............... *_kuyi hak'uri, wlhy nayi typing sosai, Nazo zanyi posting na danna delete, bakuji iron haushin danakejiba yanzu wlhy *luv u oll my fan's* *(((S)))........2017* [8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_* *_NA Bilyn Abdul_* _sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)* https://mrsbilkisa.blogspot.com *(page 41 & 42)* Dr kishingid'e gefen gado, kan musayeef na kan k'irjinsa yayi filo dashi, barcincisa yakeyi ajikin babansa, ahakali Dr ke shafa sumar yaron data kwanta luf luf, yakai dubansa ga iman dake tsaye tana shirin barci. My life wai wace maganace zaki fad'amin d'azu ne?. d'ago idonta tayi tad'an kalleshi tana murmushi, saida ta d'aure igiyar rigar barcinta sanan taja kujerar madubi tazauna suna kallon juna. Uhmm damafa akan d'iyarkane deexerh, deexerh kuma?, mike faruwa da ita?. Babu komai sai alkairi. Yaushene kuke ganin zakubar dee.... Tafara kula samari harta sami mijin aure?. Kallonta yake cike da mamaki, yad'an k'an k'ance idanunsa, miya kawo wanan maganar?. Iman ta juya kwayar idonta tana gyara zama, bafa wani Abu bane, ni kawai ina ganin lokaci yayi dazaka bata dama tafito da miji. Ajiyar zuciya Dr ya sauke, yad'an tashi zaune tareda gyarama musayeef Kwanciya, hakene my life, saidai ina ganin abarta ta kammala karatun shiyyafi a'ala, kinsanfa yarannan dasun fara soyayya saisu zubar da komai mai muhimmanci arayuwarsu. Murmushi iman tayi, hummm Dr kenan, zan iya yarda dabatunka tawani 6angaren, amma tawani gefen zand'an musaka, musamman Idan na kalli rayuwata. Karka manta ina ss 2 secondary aka cireni aka baka, miyasa iyayena basuyi wanan tunaninba. Kai ya girgiza yana murmushi, kema asanan akwai abinda yakawo dalili, amma dukda haka na fahimceki, yanzu ita khadijan tanada Wanda takesone?. Ajiyar zuciya iman ta sauke, tareda fad'in abinda nakeso ka tambaya kenan. Yasake murmusawa amma baice komaiba. Dee..... Tanada Wanda takeso, sun had'une alokacin dakayi wata jiyya a asibiti, 'yarka tanason guy d'in sosai domin na fahimci haka a zancenta, shima kuma yana Sonta bil'hak'i da gsky, Dan har yana buk'atar ganinka daga nan yaturo iyayensa, kaga bayan kammala makaranta saimusha biki. Dariya Dr yayi, Dan ganin yanda ta k'arasa maganar cike da d'oki, yashafa kansa yana kallonta, my life nima nakusa zama kaka ko?, yak'are maganar da d'aga gira. Jinjina masa kai tayi tana d'an zaro ido, fuskarta d'auke da murmushi, ta sara masa alamar girmamawa. Dariya yayi sosai, my life kodai kema zaki zama soja ne?. Kagako damun kafa tarihi miji soja mata soja, d'ansuma zaizama soja, lamarin so nice. Dr yalek'a fuskar musayeef yana fad'in gsky zamu bada ma'ana, da maganatu idonsa biyu datuni labarinnan yakai kunnen mama da yaya da aunty. Iman tamik'e tana dariya, ta hawo gadon tazauna kusada Dr tareda d'ora kanta akafad'arsa, aii wanan d'an naka har nakan rasa inda ya koyo magana, gashi kai ba gwanin surutuba, nimadai hakan nake, amma shi magana kamar akku, tad'anja hancin musayeef daketa barcinsa. Dr yashafo fuskarta yana fad'in kin manta da deexerh, aii dukkanain surutunta musayeef yad'obo. Uhhmmm kumafa hakane habibi na. Kallonta yayi sosai, ya maimaita sunan ahankali habibi!.. Kai takad'a masa tana murmushi, rungumeta yayai yana sumbatar wuyanta daketashin k'amshin wani fitinannan turare. Yad'ago suna kallon juna, ngd sosai. Ka cancanta tafad'a cike da salo. Nima nayi dace yafad'a ahankali. Nice nadace habibi na, nima nadace my life yafad'a yana rungumeta. *++++* *++++++* *++++* Washe gari iman tabama dee..... Labarin yanda sukayi da Dr, cike da farinciki Dee.... Tarungume iman, kai aunty nayi farinciki sosai wlhy, yaushe ya ce, "yazo su had'u?. Nanda kwana biyu, Dan zaikoma wajen aiki ranar lahadi, woow! Bari na gumtsama bobo na. Tofa Dee.... Kinfa afka da yawa. Um'um aunty kefa kikace karna tsaya kallon ruwa kwad'o yamin k'afa. Haka batun yake d'iyar uncle isma'il, maza kira surikina ki gumtsa masa bayani kawai. Dariya sukayi harda tafawa...... Shigowar Xoxo yasa suka mik'e suna ihun murna, cike da farinciki suka rungume juna. Bayan sun zauna iman ta ce, " haba my sisi abin ko waya babu. Uhummm kedai bari, gidanne zasuyi bak'i shiyyasa nahad'o inawa inawa nayo nan. Bak'i kuma kamarya?. Xoxo ta harari iman, kina nufin daddyn musayeef bai fad'amiki komaiba. A'a wlhy basanar dani komaiba, k'ila ya manta. Lallai daddyn musayeef zan ramane, wai ina kishiyarki naji gidan tsit, gashi kuma kuncika gida da ihu keda dee..... Deexerh dake ajiye tire ta ce, "lah wai aunty bata baki labarin mun iza k'eyarta gidan tsohoba. Xoxo tad'an zaro ido, kamarya dee....?, Kaini 'yan ganau mana. Gilas kof dee.... Tamik'ama Xoxo cikeda lemo, hhhhh aii randa nadawo ranar suka kama hanyar sokoto da sakamako mai k'yau har uku uku. Xoxo takwashe da dariya, dee..... Wai kina nufin anshare tarihinsu saidai alabarin kundin k'addara. Wlhy kuwa, sunyanki tikitin barin kano tuni. Shegiya dee..... Shiyasa nake k'ara sonki, ammafa yau zanyi barci mai dad'i. Iman dake zaune tanajinsu ta girgiza kai kawai batareda tayi maganaba. Xoxo ta kalli iman, lallai sisi shine koki Sanar minma. Kai saikace wani abin farinciki?. Okey keda abin bak'inciki kika d'aukeshi, tab ni fishinma danake da daddyn musayeef ya wuce na huce. Iman ta ce, " kudai kula sani", ni Dan ALLAH miya faru agidan har bak'i suka koroki?. Ki tambayi mijinki shiyyafi cancanta yasanardake. Kai sisi.... Bafa ya nan suna kasuwa tareda yaya, saifa anjima zai dawo, nikam wlhy nak'agara naji. Hhhhh saiki maida kwad'ayinki Dan bazakiji mutuwar sarki abakinaba, shine abokin ango mafi kusanci. Iman tazaro ido waikina nufin komai Normal?. Xoxo ta ce, "bafa zakijiba. Da sauri iman ta tashi saigata da waya, Dr takira, bayan sund'anyi musayar kalaman soyayyarsu ta ce, " hafsat fa tazo mana yini. Woow! Kice kawai amaryarmu insha ALLAHU. ban ganeba?. Oh my life sorry Dan ALLAH, wlhy namanta nabaki labari, randa nadawo dazumud'in fad'a miki abinnan yafaru, karki damu ganinan zuwa gidan yanzu. Tom saikazo iman tafad'a tana Yanke wayar. Babu dad'ewa Dr ya iso gidan, lallai amarya saikika gudo kenan?. Dariya Xoxo tayi, bayan sun gaisa ta ce, "badole na gudoba kun cike gidan da mutane. To aii haka akeso, babban taroma yana
Chapter 44 · 0% Book details