Sashe 26
Ban Saketa Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
marwan yad'auka yabashi, akunne yakara yana murmushi, Nabeel ykk?. Lfy lau abokina, gani a k'ofar asibiti. " kai haba da gsk?." "Wlhy kuwa Kasan bazan iya hak'uriba sainazo na ganka." Tom ga marwan nan zai shigo dakai. Marwan jeka shigo da Dr Nabeel. Okey uncle, marwan yafad'a yana mik'ewa. Bayan kamar minti hud'u suka shigo da sallama, su deexerh suka amsa, Dr Nabeel yak'araso gaban gadon, ayya abokina karame sosai wlhy, ya jikinka?. Dr Isma'il yay murmushi, Alhmdllh Nabeel. Su deexerh suka gaidashi, shi saima yanzu ya lura dasu, bakinshi nad'an rawa yanuna Xoxo, nikam a INA nasanki Xoxo tayi murmushi, amakarantar su jman, lokacin dakaje d'aukar daddyn Musayeef. Yes hakanefa. Murmushi Dr Isma'il yayi, danganin yanda abokisa ya waske, tunfa ranar yake damunsa akan yana son Xoxo, ya musalta masa kamanninta, shiyyasa randa ya d'akkosu kallo d'aya yaymata yaganeta, amma yanzu jiba yanda yanuna yama manta Inda yasanta. Daga nan fira suka farayi sosai, Xoxo data d'ago saisu had'a ido da Dr Nabeel, ita kunyarma kallon dayake mata takeyi, duk ya wani tsareta da mayun idanunsa. Xoxo takalli agogon hannunta, kai deexerh bari nawuce dare yafara yi, daddyn Musayeef ALLAH yak'ara lafya. Amin hafsat ngd sosai, Dan ALLAH kigaidamin 'yan gidan. Zasuji insha ALLAHU ngd Nima. Dr Nabeel ya mik'e, abokina bari nayi rakkiya ko, yafad'a yana kanne ido Dariya Dr Isma'il yay yana jinjina kai. Suna fita wayar deexerh tahau wringing, kallon Number tatsayayi Dan bata ganeba. Har wayar ta yanke aka k'ara kira sanan ta d'aga da sallama. Assalamu alaiki gimbiya, muryarsa ta daki dodon kunnenta, ajiyar zuciya tasauke, tareda fad'in wa'alaikassalam. Humm kin manta dani ko?. Aiini bamma ganekaba deexerh tafad'a tana d'an murmushi. Oh God sorry, Sunana Umar farukh, Wanda muka had'u a asibiti. Okey nagane. Yauwa to ykk?. Ina lfy. Masha ALLAH. Dan ALLAH idan bazaki damuba inason kawomiki ziyara gidanku gobe idan ALLAH ya kaimu. Kai Haba malam daga had'uwa sau d'aya saikuma zuwa gida.......katseta tayi da fad'in pls gimbiyata, ke mai ajice bakidace da afad'amiki ana sonkiba awaya, dole sai anbaki girmanki zuwa gida. Murmushi deexerh tayi, shikenan gwanin dad'in Baki, zan turomaka address d'in. Babu dad'in baki komai nafad'a akanki gsky ne, ngd sosai saina jiki. A6an garden su Xoxo ma kusan hakan take, kiran deexerh da akayi awaya yayma Dr Nabeel dad'i, Dan gani yake yasamu damane. Yakalleta cike daso da k'auna, 'yammata nifa kinmun sata wlhy. Ido Xoxo tazaro sata kuma malam?. Yes yafad'a yana wani lumshe idanu, Xoxo ta had'e fuska kai malam banason sherifa, wanan idan wanima yaji aisai yazata gskyne? To aii gaskyar CE kedama kin zata wasa nakeyi. Mtsowwww malam bani hanya na wuce kaji, humm aii bakida damar tafiya saikin bani madadin abinda kika satar min, kokuma namiki ihu. Harararsa tayi, tokayi ihun mana, ya ce, "kin yarda kenan?. Banza tayi masa Dan yafara bata haushi, wayarta tad'akko tafara danna Kiran iman, fisge wayar yayi ya yanke kiran, 'yammata saifa kin saurareni. To tunda ana dole basai muganiba. Dariya yayi sosai, zan kar6i number ki wajen khadija zan gaya miki satar dakikamin, sanan kijira zuwan rundunar sojoji gidanku kar6ar madadin satar dakikamin.. Daidainan deexerh ta k'araso, yamik'a mata wayarta tareda fad'in sai kinjini, kud'i yad'akko yabama deexerh, khadija ga wanan kibama bak'uwarmu tahau mota. Deexerh ta rissina ta kar6a tana fad'in to uncle angode. Xoxo kan gaba tayi bata tanka musuba. Hannu yasaka a aljihu yana binsu da kallo har suka 6ace sanan Yakoma cikin asibitin yana murmushi masifar Xoxo. Dr Isma'il ya kallesa kai abokina duk kawani rud'e wlhy. Dariya Dr Nabeel yayi, badoleba abokina soyayya aii ba k'arya bace. Hakane Dr Isma'il yafad'a yana murmushi. Deexerh ta ce, " aunty hafsat Kodai Kodai keda uncle Nabeel ne?. Kodai2 me Xoxo tafad'a tana zaro ido Dariya deexerh tayi, naga kamar sonki yakeyine?. Tab rufani ki sayani, ko d'aya tafad'a tana tare adaidaita sahu, saida tashiga sanan Deexerh tasaka mata kud'in da Dr Nabeel yabata a jaka, toga k'yautarki. Tab nifa bazan kar6aba ki maida masa kayansa. Habadai ai ba'a maida hannun k'yauta baya, ngd sosai kigaidamin mutan gidan. To zasuji mai adaidaita yaja suka wuce deexerh na d'aga mata hannu. Iman kuwa tunda suka bar asibitin tazama wata shiru2, koda suka koma gidama d'aki tashige tayi shiru, sallah kaiwai ketashinta, wajen k'arfe 6 taji wayarta tad'anyi wringing, d'auka tayi taduba, saitaga Xoxo, tayi murmushi 'yammata ni kikema flashing?. Komawa tayi takwanta, ganin xoxo bata sake kiraba yasa ta tashi, d'ari biyu ta d'auka tafice. Deeni na zaune afalo yana cin abinci tabasa, deeni idan ka gama Dan ALLAH d'an siyo min kati. To aunty, Dan ALLAH Nima d'an bani d'ari, inada d'ari nacika nasiyo katin, data nakeson saya. Hararasa iman tayi, kai Dama kud'inka aii a sayen data zasu k'are, ALLAH ya shiryeka. Amin aunty, nidai idan zaki bani aii babu matsala. Fita tayi bata tanka masaba, babu dad'ewa tadawo da d'ari biyu ahannu tabashi. Kai my aunty ngd, shiyyasa wlhy nake k'ara sonki. Iman tayi murmushi kawai takoma d'aki ta kwanta. Babu dad'ewa yakawo mata katin tasaka. Saida tafara gwada Number Reefat, har yanzudai bata Shiga, afili ta ce, "ALLAH yasadai lafiya. Xoxo takira bugu d'aya ta amsa, suka gaisa cike da kewar juna, Xoxo ta ce, " ai d'azu naso na kiraki nace miki INA wajen mijinki, saikuma aka samu matsala. Aii flashing d'inki Dana ganine ma yasa nakira da fushi nakeyi dake. Ohh my sis.... Kiyi hak'uri, wlhy zanzo gobe idan ALLAH ya kaimu insha ALLAHU, wani abunema yahana in zuwa jiya da yau. To shikenan na hak'ura, kinsan bana iya fushi dake, ALLAH ya kawoki lfy. Amindai, Wai Yaya kema har yau bakya samun Reefat?. "Wlhy bana samu, ni harma nafara tunanin ko lafiya?, wlhy Nina haka, to ALLAH yajishemu alkairi. " Ameen dai". Sukai sallama kowa ya kashe wayar. _Bayan kwana hud'u_ Jikin Dr Isma'il yayi sauk'i sosai harma an sallamesa yau. Iman dai bata sake zuwa dubashiba, bakuma takira wayarsaba, gwaggo da Abbah sunje har sau uku, hakama su aunty salma sun sake zuwa, Xoxo ma tak'ara zuwa. To Dr Isama'il ALLAH yak'ara sauk'i. *_WATA SABUWA_* Gidan su Dr isma'il yau cike yake da mutane, dangin mahaifinsu ne sukazo dubashi, ciki kuma harda baban su aunty sadiya, bayan anci ansha aka zauna ana hira. Acikin hirarne kawu Falalu yake fad'in sufa dawata magana sukazo, mama ta ce, "to falalu muna saurarenka. Kawu falalu yagyara zama yana kallon mama, ya ce, " maganace akan Sama'il, lokaci yayi daya kamata yayi aure, wanan zaman dayakeyi bazai haifar da d'a mai idoba, tunda kowa yasandai ba'a komawa saki uku, to Dan haka yama fidda rai akan matarsa, saidai idan darabon zama nan gaba zasu zauna. Hakane mama tafad'a fuskarta babu walwala, Dan tasan Dama ba alkairine yakawosuba. Kawu falalu yacigaba, to yanzu dai mun yanke shawara Nida Lurwanu da Maharazu, da Karima akan zamu k'ara k'ulla zuminci, mudai nida maharazu da Karima bamuda yara mata, sai Lurwanu, Dan haka muka Yanke shawarar aurama Sama'ila Zakiyya,(Raihan). Gaban Dr Isma'il ne yafad'i da Sauri yad'ago yana kallon kawu falalu. Kawu falalu yacigaba da fad'in, to yanzudai maganar damuke muku, ni na biya sadaki an d'aura auren tun a can, shinema dalilin dayasa kukaga mun taho da Raihan, gata nan munkawota suzauna lafiya, ga 'yar uwarta nan intayi ba daidaiba zata ringa tsawatar matane, kumadai saiku kula, intayi ba daidaiba a gyara mata Dan kunsan yarinyace karama sai hak'uri. Tunda yafara maganar falon yakarayin tsit, bakajin motsin kowa, sai aunty da Raihan Dasuke murmushi. Yaya ya bud'e baki zaiyi magana mama ta girgiza masa kai alamar yayi shiru. Shirun kuwa yayi amma idanunsa sun cika da kwallah, tu da mahaifinsu suka bar duniya, dangin mahaifinsu suka watsar dasu, basa kulawa dasu ko kad'an, basa zuwa Inda suke, har saida sukaga sun girma sun zama wani Abu, shine akazo aka k'ak'aba masa auren sadiya, zuwan sadiya baifi da wata ukuba uwar 'ya'yansa tabar gidan mamansu deexerh. To gashi kuma yanzu an mannama Isma'il Raihan, bayan abaya mahaifiyarta ta CE, "bata yarda Isma'il ya auri Raihanba baza'a tara mata 'ya 'ya agida d'ayaba........ Maganar mama ta takatse masa tunani. Shikenan falalu, mun amshi k'yautarku ALLAH yasanya alkairi, saidaifa kunyi kuskure Dan yakamata kafin kuyi Auren kukiramu asanar damu Dan aji tabakin Isma'il d'in, amma yanzu ya wuce saidai Atari gaba kawai. Baban su raihan ya katse mata zancen da fad'in, Maryama kinsandai munada iko da Sama'ila muma ko?, Dan duk duniya bashida iyayen dasuka wuce mu, ko Neman auren zashi wani waje dolene mune wakilansa, to tunda abin yazama na gida kuwa aikinga koya sani ko bai saniba, koya yarda kobai yardaba dolene yakar6i 'yar uwarsa yarik'e da hannu biyu, kuma naga dama suduka suna son juna daga sama'ilan har Raihan d'in, kawai abaya ALLAH ya rubuta bazata zama matarsa bane. Kaga Lurwanu nifa babu abinda nace maka, Dan haka maganarnan bata 6acin rai bace, aurene kun d'aura kuma nace mun kar6a, to saime?, duk wata maganarma kun Isa bata tasoba, Inda bama ku isanba aii wlhy babu mai aurama yarona aure batareda yardarsaba. Sunsan halin mama sarai Dan haka suka Shiga bata hak'uri da magana mai dad'i, anandai ka masu Dr Isma'il nasiha shida raihan. Deexerh taji zafin wanan had'in ammafa tawani 6angaren taji dad'i, Dan idan bata mantaba aranda suka Gana da bilyn Abdul tace musu inama Raihan ta Auri Uncle, da komai saiyafi saurin fitowa fili. Wanan yasa bataji haushiba sosai. Saidai ana gamawa da uncle d'inta aka dawo kanta. Kawu Maharazu ya ce, "kema hadiza mun Baki nan da wata Biyar Kodai ki fito da mijin aure kokuma muhad'aki aure da Kamilu na wajena. Ido deexerh ta zaro ta ce, " kawu Kamilufa kace?. Eh shifa nace, Dan haka saikiyi gaggawa..... Dr Isma'il ne ya katse masa zancen da fad'in a'a kawu nanfa ba huruminku baneba, domin khadija jikace agareku, mune iyayen khadija mu Muke da damar aurar da ita lokacin da mukaso, ayanzu kuma karatu takeyi, sainan da wata Tara zata kammala, saikuma ta kammala sanan zamuyi mata maganar aure, mudai damuke 'ya'yan d'an uwanku, Duk abinda kukaga dama kuyi damu, saboda darajar kun kasance jinin mahaifinmu na kusa..... Sama'ila mukake gayama haka Dan ubanka, to ai ko Mahammadu dayanada rai bazai fad'amin hakaba akan zuri'arsa...... Mama ta katseshi, Maharazu