← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 38

Sashe 8

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tin da ta shige gidan duk wani abu da za'ayi ta na ciki ta ƙi fitowa, ta na kallon mutane har zuwa ake ana leƙota ana ɗan nunata, ita dai ba ta ce komai ba sai dai in abin ya yi mata ciwo ta ɗan matse hawaye, jiran tafiyar su Umma take yi su kuwa sai Goman dare sannan su ka tashi tafiya, lokacin da su ka iso gida Sha Ɗaya sauran Ƴan Mintina, ta ji daɗin hakan don kuwa duk Fitinannun yaran layinsu sun shige gida har shi kanshi Gogan, tinda ta yi siff ta shige gidan makonci kawai ta nema don anan ne za ta samu damar yin kukanta ba tare da kowa ya sani ba.

Yau Abdulkareem ya na zaune shi kaɗai sauran Yaran kowa ya tafi uzurinsa wasu makaranta, Walid ne ya tawo ya na taku a ƙasaice kamar wani Yaron Giwa shi a dole babban Mutum, sai da ya kalli Abdulkareem sannan ya watsar ya wuce, Abdulkareem ya miƙe ya riƙe hannunsa kam sannan ya ce "Kai daga ina kake??" "Ina ruwanka? ka aike ni ne? ba na son shishshigi ba kwarjini" Wani kyakkyawan Mari Abdulkareem ya tsinka masa sannan ya ce "Da ni kake gaba ko?? sabi da na doki ƙanwata da ba daga gidanku ta fito ba, ni za ka nunawa rashin hankali?? ashe kasan abin da ciwo? ranar nan da ka dokawa YaYa Aaminat Ƙwallo don ban nuna ɓacin raina ba shine kai za ka yi Gaba dani sabi da na doki Ƙanwata ko??" cike da rashin kunya irin tashi ya ce "Eh an buga mata ɗin ai naga YaYata ce ko, wallahi ka ƙara dukana sai dai mu daku." wani lafiyayyen marin ya ƙara zuba masa sannan ya ce " Na ƙara maka kuma zan ja maka kunne, rashin kunyar da ku ke yiwa Aaminat ta isa haka, nima ina jin zafi bansan ba daɗi ba sai da ka fara gabani wai akan ka na son Ƙanwata, to wallahi ka shiga hankalinka da kai da ita duk ina iya karya muku ƙafafu na zauna lafiya, nima ina jin zafin da ka ji a duk lokacin da kuka wulaƙanta Aaminat kawaici kawai nake muku" Walid ya yi tsaki kafin ya ce "To wai kai me kake nufi?" "Ban damu da sai ka san me nake nufi ba inda ka fahimci akan abin da nake magana, kuma wallahi tallahi ka je ka yi min munafurci ko a gida a Layi sai na lahira ya fika jin daɗi, ni zan rabaka da farin cikin rayuwa ne har ka koma ga Allah, kuma na ƙara yi maka magana kai min banza ka ga in ban sauke maka na tauna ƙashi ba." Walid ya zumɓuri baki, yasan an fi ƙarfinsa don haka bai yi ƙoƙarin wani abu ba, ya na sakinsa ya wuce gida ya na gungunai da kumfar baki.
Mama ta bankaɗe labule ta fito ta na cewa "Wa ya taɓa ka???" "Wancan Dan Iska Abdulkareem ɗin ne har da marina ya yi ba abin da na yi masa kuma." "Kanbutar Duma???, sai na sa an ci uwar Abdulkareem ɗin nan sannan zai fita idona in rufe, Umar! Umar ! maza kira min Umar ai ya dawo" Walid ya fita kiran Umar Mama kuwa ta ci gaba da zazzaga masifa, Umar ya na zuwa ta ce "Wannan Abdulkareem ɗin nake so ka ci min Ƙanwar Tsohuwarsa, ya raina min Ƴaƴa yanzu Fati in ka ga wulaƙancin da yake sa yara su yi mata sai ka sha mamaki, yanzu ka ga ya kama min Auta ya mammara ba tare da laifin komai ba, to wallahi in ya na da ƙarfin damtse ai doka ta fishi, ni zan iya yin shari'a da shi tinda ba shi da hankali" Umar ya yi murmushin takaici kafin ya ce "Mama indai Mari ne kawai ayi haƙuri don kuwa Kinsan Waye Alhaji Aminu Mai Kasuwa, ya na da kuɗi kuma ya ɗaurewa ɗansa abun shi yasa ya ke tata iskancinsa, ba za mu iya nuna masa yatsa ba gwara ma ki yi haƙuri, Shari'ar da ki ke taƙama da ita ba za ta goyi bayanki ba bare har ki ga ribarta, ba iya ku ya ke yiwa ba ya gagari kowa a layin nan, ki na gani fa ko Ball da su ke yi a layin Matasan Layin sun yi ƙoƙarin hanawa daga nan har gaban hukuma yaron sai cewa ya yi ai idan ana so su dena sai dai a basu babban Filin Ball, kuma lokacin manya ne su ke yin wasa a a wai sai dai manya su haƙura su ba yara, ance su dinga yi da rana ya ce ai su ba cima zaune bane su na sana'a kuma suna neman ilmi ba su da lokaci sai da yamma, dole fa muna ji mu na gani mu ka ƙyalesu, Kina gani a layin nan manyan samari ƴan shekara Ishirin da Bakwai ma ba za ki gani ba bare ƴan talatin sabi da tsabar bala'in yaron nan duk sai dai su bar unguwar nan su shiga unguwar maƙota sannan su kafa Majalisa, yanzu babu samarin da za ki gani sai yara ƴan sheka Ishirin zuwa ƙasa, Mama wallahi yaron nan tantiri ne fiye da tunaninku, kaff yara masu tasowa ya lalata su ba sa ganin kowa da gashi sai shi.
Mama ta ja tsaki sannan ta ci gaba da yayyafin masifarta sai ma ta koma cewa don ba Ita ta haifi Umar ɗin ba ne ya sa ya ƙi ƙwatarwa Ɗanta haƙƙi, shi kuwa Umar sai ya bar mata gidan Umma ma ta na jinta ta yi shiru, Aaminat kuwa ta na son yin magana akan rashin kunyar Walid ɗin amma idan ta tuno waye Abdulkareem sai ta ja bakinta ta tsuke.

©️INDO & AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: https://chat.whatsapp.com/DkGGck6Es6l4w7KMwiaGVZ

*AAMEENAT*
(Bazawara)

Littafin Haɗaka ne💪🏾

Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S

Tare da

Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S

Shafi 7

Bismillahirrahmanirrahim

Fati ce ta fito daga ɗaki ta na cewa "wallahi Mama karki yarda, ai ɗa befi ɗa ba haifar shi ki ka yi shima haifar shi akai" cikin baƙin ciki da takaici Mama ta ce "kina gani fa na kira Umar ya je ya rama masa sabi da ba ni na haife shi ba yaƙi ya kama ƙalabusan banza, shima yaron ai ɗan iska ne dama ƴaƴan masu kuɗi haka suke iskanci iri-iri"
Aaminat ta kasa jurewa sai da ta shiga zancen, "Haba Mama shi fa yaron nan anan gurin babu ruwan shi Walid ne da shegiyar tsokana, na san halinsa ba kunya ce da shi ba" "to? lamarin hada zawarawa dama?" Fati ta faɗa tana riƙe baki kafin ta ƙara cewa "ai dole ki ce haka tun da yana ce miki Anti kuna sheƙe ayar ku" dole tasa Aaminat ta fito daga ɗaki tana dafe kirji Umaima ta ce "ko bahaka bane kike ɗafe ƙirji?" wata shewa Fati tayi kafin ta ce "Hee!! ni naga abun mamaki Mama Ranar bikin Bilkisun Umma Sa'a fa Abdulkareem ne yakai ta a Mota"
Mama ta yi salati tana tafa hannu tana cewa "innalillahi wa'inna'ilaihirajiun Aamina dama haka kike?" Fati tace tafi ma haka ku ne baku sani ba, ai wallahi Allah ne kaɗai ya san abin da su ke aikatawa ita da Abdulkareem ɗinnan" Umma da ke jin maganar su kamar ana zuba mata wuta ajiki bata san lokacin da kuka ya kufce mata ba tana cewa "Aaminatu da abinda zaki saka min kenan? kin san dai na baki tarbiya shine za ki dinga biyewa wannan Ɗan iskan Yaron da kowa ya san bai da kyakkyawar Ɗabi'a?, na gaji da baƙin cikin da ake sa ni a gidan nan, wallahi na gaji" jiri ne ya ɗebeta luuu tayi ƙasa cikin hanzari da tashin hankali Aaminat ta sa hannu ta tallafo Umma ta na cewa "Wallahi Tallahi Umma ni ban taɓa aikata komai ba, babu wani abu tsakanina da Abdulkareem, hasalima ni na tsane shi kawai sharri ne aka son yi min" Umaima ta fashe da kuka tana cewa "wallahi baza mu yarda ba in ta mutu ke ki ka kasheta macuciya muguwa, ba wani sharri da akai miki ai kowa ya ganki, indai da ke mutuniyar kirki ce ai ba za ki kashe Aurenki ba" cikin tashin hankali take faɗin haka
Aaminat kuwa ta shiga matsanancin hali, Temakawa Umman ta yi ta shigar da ita Ɗaki ta kwantar da ita saman Gado, cikin kuka ta ci gaba da cewa "Don Allah Umma ki yarda da ni, in banda Ƙaddara ba abin da zai rabani da Mijina, ba son raina bane kamar yadda kowa ke faɗa, Umma ni ba zan aikata kuskure ina ji ina gani ba." cike da takaici Umma ta ce "Ba ni da baƙin ciki da damuwa sai naki, tin da ki ka dawo gidan nan ba ni da kwanciyar hankali, komai akaina ya ke ƙarewa, Ko me aka faɗa akanki ba zan ƙi yarda ba, Aaminat abin naki ya yi yawa, ba zan iya jura ba baƙin cikinki zai kashe ni." wani sabon kukan ya ƙara sillewa Aaminat cikin rawar murya ta ce "Wallahi ba sa ƙaunata ne kawai sabi da baƙar Ƙaddarata, ki dena yarda da su abin da suke faɗa ba gaskiya bane." Umma ta ce "Aaminat tashi ki bani guri, ki fita kawai ki barni, ni ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba har sai kin bar gidan nan kin tafi gidan Miji." Aaminat za ta yi magana Umma ta katse ta da cewa "Ba na son jin komai, ki tashi ki bani guri." Aaminat ta tashi jiki a sanyaye, sabuwar Ƙiyayyar Abdulkareem ta na ƙara ɗarsuwa a Zuciyarta, dama tasan sai ya ƙara jawo mata wani bala'in sannan hankalinsa zai kwanta, ɗakinsu ta koma ta tsakure a gefe ta shiga rera baitin kuka.
Chapter 8 · 0% Book details