← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 38

Sashe 22

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Marin da ta yi masa ne ya bawa hawayen da suka cika kwarmin idonsa damar zubowa ya dafe kumatunsa ya na binta da idanunsa wanda su ke masa suya tamkar an watsa masa gaurashi. sai da ta gama magana sannan ya samu damar motsa bakinsa ya fara cewa "Idan ki ka ce haka kin butulcewa Allah gami da ni'imominsa gareki, ke zawarci kawai ki ka yi amma wata tin tana ƴar ƙarama aka keta mata haddi aka yi mata illar da ba wanda zai yi sha'awar aurenta, wata kuma sai da ta girma ta na burin samun miji na gari aka keta mata haddi ƙarshe ki ganta har da Ɗa bayan ba ta taɓa aure ba, wata kuma ta na so ta yi Auren amma har shekarunta su wuce ƴan-matanci ta koma babbar mace Allah bai kawo mata mijin Aure ko da sau ɗaya ba, amma duk da haka Aaminat ki ce taki ƙaddarar ta fi ta kowace mace muni?? shin kinsan adadin dubban Matan da suke jiran zuwan Namijin gaske irin Abdulkareem cikin rayuwarsu? tabbas Aamimat samun miji nagari kamar Abdulkareem a zamanin nan sai an tona, shine me sonki da gaskiya me son farin cikinki ko da kuwa shi zai kwana da baƙin ciki, ya na son ganin dariyarki ko da shi zai kasance ya na kuka a koda yaushe;, Aaminat wallahi ni kaina da na shigo rayuwarki ba don ni shaida ne akan irin son da yake miki ba da ban fara aikata hakan ba, ya so share miki hawaye da tafukan hannunsa amma kin ƙi amincewa kuma ya san kina buƙatar temako hakan ne ya sa ya turo ni gareki, idan ba ki manta ba a ranar da ki ka fara ganina na gaya Hajiya Maimuma cewar na zo ganin wani Patient ne , ba kowa bane face ke, Asibitin Aminu Abdallah mallakin Abdulkareem ne da sunansa aka gina shi kuma ya zaɓe ni a matsayin Babba me kula masa da Asibitin,, shi ɗin Ogana ne kuma Abokina, Babana Abokin Babansa ne; ya gujewa Abinci ya sa kansa a damuwa ya jawowa kansa Cuta duk sabi da ke, yana bala'in tausayinki; Aaminat na roƙe ki ke ma ki tausaya masa ki jiƙansa ko da sau ɗaya ne ki nuna masa Halacci, ki ƙaunace shi ko da Zuciyarki ba ta so, shi ɗin mutum ne me sauƙin kai kuma ya na sonki, za ki yi farin ciki indai har ki ka zaɓi rayuwa da shi, amma in ki ka bari kika rasa shi tabbas kin tafka asarar da ba za a iya kwatanta ta ba, wannan shine saƙona na ƙarshe a gareki Aaminat!,, ni kuma da na zo miki a matsayin ɗan yaudara ki yi haƙuri ki yafe min ba don halina ba." ya ƙarasa maganar ya na shashshekar kuka kamar ba namiji ba namijin ma Garƙeƙen saurayi.

Ba iya suma ko mutuwar tsaye ba in da gaba da nan Aaminat ta gama kaiwa, idanunta ne kawai ke zubda hawaye yayin da ta kafe su akan Yarima, gangar jikinta kuwa sun dena aiki don in ba ka saurari bugun Zuciyarta ba ba za ka ce mutum ce me rai da lafiya a tsaye ba.

*©️INDO Tare da SALMA AUTA*
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)

Littafin Haɗaka ne💪🏾

Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

Tare da

Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION

Shafi 18

Yarima ya ƙara da cewa "Ki kasance me ɗaukar ƙaddara a duk yadda ta zo miki, ba komai ne ake so kuma a samu ba, ita rayuwa ta gaji haka, ina yi muku fatan Alkairi." ya na gama faɗen haka ya juya ya shiga Motarsa ya ci gaba da tafiya ya nufi gidan su Abdulkareem.

Umar ne ya ƙaraso kusa da Aaminat da ke tsaye cokam ta ƙi gaba ta ƙi baya, "Wuce ciki!" ya faɗa cikin sigar umarni, sai a lokacin ta ja dogon numfashi ta sauke tare da fashewa da kuka ta fara tafiya a hankali a hankali kamar karyayya.
a gefen Katifarsu ta zauna ta haɗe kai da guiwa ta ci gaba da rero baitin kuka, ba abin da take tunowa sai Abdul sama da ƙasa ya mamaye tunaninta a wannan lokacin.

Ba zato sai jin muryar Omar ta yi ya na cewa "Ke fa duk yadda ki ka ɗauki Duniya ba haka take ba, abin kuka ba ya yi miki wahala kamar wadda ba ta san ciwon kanta ba, ki na da dama amma kin ƙi amfani da ita ga ci gaba kina maida kanki baya tsabar kin san takan shiririta, duk fa ƙarancin shekarun mutum indai Namiji ne kawai ki sa a ranki Namiji ne, domin in azzalumi ne komai yawan shekarunki ko da kin yi sa'ar mamarsa ba zai yi duba da ƙarancin shekarunsa ba hakan zai zalumce ki kuma ya nuna miki ya isa ya kai a kira shi Namiji, babban kuskure ne Mata suke tafkawa na Raina ajin Maza da faɗa musu cewa ba su kai ba hakan ya na tunzura yara ƙananu su aikata abin da ba shikenan ba ƙarshe su barku da mugun tabo, amma ya rage naki ki yi shawara da Zuciyarki sai ki yanke hukunci."
Ya na kaiwa nan ya fice ya bata guri, ta bi bayansa da ido tsaiii, ta daɗe ta na kallon ƙofa ta na tunani iri-iri kukan ma ba ta san lokacin da ya ɗauke ba, gajiyar da ta yi da zama ya sa ta zamewa ta kwanta ta ci gaba da tufka da warwara.

Yarima
a harabar gidan ya tsaya ya turawa Abdulkareem kira, ya na ɗauka ya ce "Likita Bokan Turai." murya a cunkushe Yarima ya ce "Abdul ina Parking Space ɗinku ka zo ka sameni in kana gida." rasss gaban Abdul ya faɗi sabi da jin muryar Yarima sak irin ta wanda ya ci kuka ya ƙoshi.
Tashi ya yi ba tare da ya ce ƙala ba ya zabari silifas ɗinsa ya na jin Nana Khadija ta na tambayar inda zai je ya yi mata banza.

Yarima ya na tsaye jikin Motarsa ya jingina hannunsa ɗaya harɗe a ƙirjinsa ɗayan kuma ya na kan ɗayan ya tallafo haɓa da shi.
Abdul har shirin tuntuɓe yake wajen ƙarasowa inda Yarima yake, ko tsayawa bai ba ya ce "Lafiya kuwa Yarima?" ya girgiza kai gami da sauke nannauyar ajiyar Zuciya Sannan ya ce "Ba zan ce lafiya ba, Mahaifin Aaminat ya na buƙatar Aurar da ita cikin wata ɗaya ya nemi iyayen Masoyinta, ni kuma ban yi ƙasa a guiwa ba na gaya mata gaskiya domin rufewar shine kuskuren." tamkar Mutum ya yi gware da Babbar Mota Gingimari haka maganar Yarima ta zo wa Abdulkareem, cikin rawar baki da rashin sanin abin yi ya ce "Yanzu kana nufin ta san ni na turaka gurinta??, kuma a wata ɗaya Abba yake son aurar da ita? anya baya shan wani abu kuwa? ko an ce masa haka ake auren sama taka?" Yarima ya ce "Ya yi bazata kuwa, amma a shawarce wannan dama ce ta sameka ka san yadda za ka yi ka aureta don ba na so ka rasata, idan aka ƙara kawo min kai ba lafiya Allurar Dogon bacci zan yi maka ka yi shekara baka farka ba kowa ya huta da rigimarka." ya ƙarasa maganar cikin sigar zolaya, Abdul ya ce "I'm seriously, ban san wanda zan tinkara da maganar ba, to amma zan yi tunani sosai, na gode da temakonka."
Yarima ya jinjina kai kafin ya ce "Ni zan wuce, ka kula sosai."
Ya na gama faÉ—en haka ya shiga motarsa ya fice.

Abdulkareem ya shiga zagaye a gurin a matuƙar rikice, ba zato ya ji an cafki kwalarsa, ya juyo da zafinsa don ganin wanda ya yi masa hakan, karaf su ka yi IDO HUƊU da Abdulmajeed fuskarsa a murtuke ba alamun wasa, cikin kakkausar murya ya ce "Mu je ciki dan ubanka yau ka yi mana bayani da bakinka." bai saurari maganar da Abdulkareem yake ba ya ja shi zuwa babban falo, har Dadda ma ya na zaune. a tsakiyarsu ya ja dinga kafin ya fara magana a mugun fusace, "Ashe munafukin yaron nan tayar mana da hankalin da yake wai aure yake so, amma shine ya ke ta ƙumi-ƙumi, yanzu banda tsaurin ido i na Abdulkareem ina shi ina aure yaron da ko gama iya sa riga bai yi ba?" tsananin mamaki ya cika kowa da yake gurin musamman Dadda da bai taɓa zaton ɗan da yake wa kallon me hankali zai iya yin hakan ba.
Cikin sigar tambaya ya ce "Aure!??"
*Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta*
*Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.*

*HALY-JASHERU venture's*
*munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.*
*prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA*
Chapter 22 · 0% Book details