Sashe 7
Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
firgita ta yi sabi da jin muryar Abdulkareen a dodon kunnenta "Haba YaYa Aaminat don Girman Allah ki koma ki canja kayan nan, wallahi sun yi miki ƙanƙanta kamata ya yi ki dena saka su ma.
Bakinta har rawa ya ke wajen cewa "Bab.. ba.. bazan canja ba, ina ruwanka da ni?" ya ɗan yi dariya kafin ya ce "Ba ruwana da ke kawai karambani ne, ina za ki je ma??" Ta ɗan murguɗe baki ta ce "Bikin Ƴar Ƙanwar Abbanmu ake yi" Idanu ya zuba mata ya na binta da wani sihirtaccen kallo, sai murmushi ya ke wanda bai ma san ya na yinsa ba "Kin iya murguɗa baki YaYa Aaminat" tsaki ta yi gami da ci gaba da tafiya ta na tuhumar kanta ma dalilin da ya sa ta tsaya saurarensa. cikin sauri ya tare hanyar ta fuska a haɗe ba alamun wasa ya ce "Aaminat bar ɗaukar zancena a wasa fa, idan ƙanwata ce ke ba zan bari ki fita da kayan nan ba bare ke YaYata, don Allah ki koma ki canja sai ki tafi." "Ba fa zan canja ba" "Ni kuma indai ba za ki canja ba nima ba zan barki ki wuce ba wallahi sai dai ki fasa zuwa bikin, kin ji har na rantse"
"Wai ina kake so in sa kaina Abdo..." ɗaga mata hannu ya yi cike da manyance ya ce "Na gama magana Aaminat, ki yi haƙuri ki dinga sitirta min kanki." ya na rufe baki ta ɗauki hanyar komawa gidan zaizaizai ta na tafiya ta na haɗa hanya bakinta ɗauke da Addu'a a cewarta neman tsari take da sharrin Abdulkareem, duk ilahirin jikinta ya ɗauki tsuma, ai kuwa indai gaskiya ne abin da Zuciyarta ta ke gaya mata akansa ai kuwa Kamal ya sa ta tafka babbar asara a rayuwa, ya yi mata tozarcin da ba lallai a samu tozartacciyar mace irinta ba....
Â©ï¸ INDO & AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin HaÉ—aka ne💪ðŸ¾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S
Shafi 6
Bismillahirrahmanirrahim
Sabi da takaici sai ta ji kamar kar ta je Bikin ma, Doguwar riga Abaya ta ɗakko ta ƙare mata kallo aranta ta ce Wannan dai duk jarabarsa ai ba za ta kama jikina ba, Sakawa ta yi sannan ta Ɗakko Hijab ta saka a cewarta ta ma fasa saka mayafin, ta ƙara fesa turare sannan ta fito cikin sanyi jikinta duk ya mutu, ta cikin mirror ya hangota, ganin yadda ta zuba Hijab ya sa shi sakin murmushi, kwata kwata ba ta lura shine a Motar ba sai da ta zo wuce ya yi Hon da ƙarfi, ta maruƙar razana da artawa za ta yi da gudu sai ta cije, ya fito ya na dariyar shakiyanci, har ya je ya yi shirinsa cikin Ƙananun Kaya Baƙin Wando da Farar riga me ɗan ƙaramin hannu, "YaYa Aaminat zan je gidan mai shiga in rage miki hanya" ya yi maganar ya na murmushi gami da kasheta da fararen idanunsa, cikin sauri ta girgiza kai ta ce "Ba zan shiga ba" Takawa ya yi cikin nutsuwa ya matsa kusa da ita idan ya matso sai ta matsa har sai da su ka kai bango sannan ta tsaya ta zuba masa ido don ganin ƙarshen tsagerancin nasa, asalin ƙwayar idanunta ya ke kalla wanda yake iya karantar abubuwa da dama daga cikinsu, cikin wata kasalalliyar murya ya ce "Allah Aaminat idan ki na yawan yi min gardama zan nuna miki bambancin Wa da Ƙanwarsa, ki shiga ko na sa ki da kaina, ki ka tsaya kina kallona." cike da takaici ta ce "Wai kai ko kunyar faɗen sunana kai tsaye ba ka ji? aƙalla fa na yi ƙani na biyar ko shida da kai, amma don rashin kunya kake min abu kamar wani Babana don wannan isar taka ta fi ƙarfin YaYa, ba fa zan shiga Motar nan ba sai dai ka yi duk abin da za ka yi, akan na bi ka gwara
na fasa zuwa, ba za ka jaza min bala'i ba yanzu ace kuma bin maza na koma yi" Ido rufe take maganar cike da son nuna iyakar gaskiyarta, shi kuwa ya yi shiru ya zuba mata ido ya na wani Sassanyan murmushi, sai da ta gama surutun ta ƙara kallonsa ta ga ko gezau bai yi ba, ta ƙara jan dogon tsaki ta ratsa ta kusa da shi za ta wuce ya yi saurin riƙo hannunta gami da cewa "Ohh Aaminaathhh!!" yadda ya kira sunanta ya mugun taɓa Zuciyarta ta tsaya cakk gami da rintse idanunta ta cije gefen leɓenta, zagayowa ya yi gabanta ya na ƴar dariya ya ce "Me yasa ki ke son ɓata min lokaci har ma da ke kanki, Aaminat tin da ki ka fito sai kin je kuma ni zan kai ki" shiru ya ɗan yi kafin ya saki wani malalacin murmushi ya ce "Komai naki har Zuciyata! kina bala'in girgizani a duk motsinki Aaminathh!!" "Kai Master hannun YaYa Aaminat ɗin ne a cikin hannunka???" Bilal ya jefo masa tambaya cike da mamaki, cikin sauri ta fizge hannunta cike fa baƙin ciki da takaici, ji take inama za ta iya ta kikkifa masa mari ko zai gane ba sa'arsa bace, shi kuwa da ta fizge hannunta sai ya saki murmushi ya shafi sumar kansa sannan ya ce "Bilal wai unguwa zan je shine ba zan rage mata hanya ba." Bilal ya ce "Yaya Aaminat ki yi haƙuri ki shiga mana, kin san shi kin san gidansu ai ba zai sayar da ke ba, ni bari inzo in raka ku ma." tsaki ta ja kafin ta shiga gidan baya don ta lura sabi da naci za su iya cinyeta, Abdulkareem ya dafa kafaɗar Bilal cikin muryar raɗa ya ce "Ba za ka je ba munafuki" Bilal ya yi dariya ya ce "Na ji , wallahi sai in ce kar ta bi ka ma" talle masa ƙeya Abdul ya yi ya na dariya sannan ya shige gidan direba ya fige motar. Tasan dama ba gidan man zai je ba don haka ko da ta ga ya ƙi tsayawa ba ta ce masa komai ba, shi kuwa ya na tafiya ya na waiwayenta daga baya ma sai ya saita Mirrorn cikin motar zuwa kanta. "Wace unguwa za ki je??" "Ba na so fa ka kaini inda dangina za su ganni tare da kai su dinga zagina, gwara ka ajiye ni in tafi a Napep" "Tin ina ɗan shekara goma sha biyar na iya Driving kawai ba a bani mota ne, sannan a gidanmu akwai motoci sai wadda naso nake hawa, kuma duk bayan wannan sai na barki ki tafi a Napep bayan gani ba aikin da nake yi? kema kinsan ai a tsarina babu haka, kawai neman ɓata bakinki ki ke yi, tin da nace zan yi kinsan sai na yi." Dogon tsaki ta rafka gami da zuba tagumi ta ɓoye fuskarta a cikin hijab, ya yi murmushi kafin ya ce "Ya Aaminat! Wallahi in kina murmushi har kusan suma nake yi," cikin sauri ta ɗago kai ta na cewa "Iye???? Abdul me ya ke damunka ne??" dariya ya yi kafin ya ce "Kin ga dai na sa kin ɗago duk da kin ɓuya, kinga bambancin babba da yaro kenan" "Ni kake kira yarinya??" "A haka nake ɗaukarki Aaminat domin ina da muradin zamo miki bango a Rayuwarki" baki na rawa ta ce "Abdulkareem Rijiyar Zaki za ka kaini don Allah ka dena lelewa da ni akan titi kar ka ɗauki raina kafin na je bikin nan, wallahi nayi da na sanin fitowata zamana a gida ya fi Alkairi, yanzu na tabbatar kai Mahaukaci ne, meye haɗina da kai??" "A zahirance ba alaƙa a tsakaninmu ta jini ko ta wani abun ba abin da mu ka haɗa, sai dai shi Allah babu rawansa baya damuwa da matsayin wani ko wani sai ki ga ya haɗasu Alaƙar, ni dai ina jin akwai alaƙa a tsakaninmu kece dai bakya jin haka, a gurina Ba ki da bambanci da Nana Kadija Nana Fareeda Nana Hauwa'u, dake da su duk ƙannena ne." "Ciwon Zuciya ne ajalina na tabbata, abin duniya ya yi min yawa, ka rufa min asiri ka barni na rayu da baƙin cikin da yake damuna kar ka ƙara min wani tashin hankalin, ka tausaya min ka cire ni daga sahun Ƙannen nan naka don girman Allah" murmushi me taɓa Zuciya ya yi kafin ya ce "Ba ni na sa ki da kaina ba, kuma ba ni da ikon cire ki, ki tayani da Addu'a indai cutata me warkewa ce zan warke in kuma ba zan warke ba to fa ba na jin zan iya bari ki zauna lafiya ko ina ki ka shiga, ki ɗauke ni a matsayin ƙaddararki Aaaminathh!"
"Abdulkareem Na tsaneka!!" ta faɗa tare da fashewa da kuka, Murmusawa ya yi ba tare da ya ce komai ba, Zuciyarsa banda ƙuna ba abin da take yi, a take idanunsa su ka canja launi.
ba wanda ya ƙara magana har su ka isa unguwar sannan ya ce "Idan za ki iya ki kwatanta min in ba za ki iya ba sai mu zauna tare a motar don ni ba na gajiya da kallonki ko da gaban tsana za ki yi min." ta san aikata hakan ƙaramin aikinsa ne don haka ta murje idanunta ta kwatanta masa.
har ƙofar gidan ya kaita ya na tsayawa ta buɗe ta fito, cikin sauri ya fito ya zagayo inda take ya na cewa "Aaminat don Allah in da wata damuwar ki kira ni, duk lokacin da za ki tafi ma kawai ki neme ni." girgiza kai ta yi kafin ta ce "Ina Addu'ar kar Allah ya kawo min ranar da zan nemeka don kaina." ya ɗan yi murmushi gami da cewa "Na ji Aaminat, amma ni ba zan yanke ƙauna ba , na ce wata rana za ki neme ni." Fiddausi ce ta kasa yin shiru ta ƙaraso wajen hannunta riƙe da haɓarta, "Aamina?! tabbas ba shakka, ke aka aje a wannan Motar lunƙumemiya??" Abdukareem ta zubawa ido cike da takaici take binsa da kallon ka ga abin da ka ja min, ya rausayar da kai gami da cewa "Ki yi haƙuri YaYa Aaminat na yi miki shi....." ɗaga masa hannu ta yi kafin ta yi gaba, Fiddausi ta kalle shi kafin ta ce "A kawo maka ruwa Yallaɓai??" a taƙaice ya ce "Sauri nake aikena aka yi shine naga Auntynmu na rage mata hanya." "Laaa Abdulkareem me ya kawo ka Bikinmu?? ko dama kasan ana bikin ne??" Fati ce ta yi magana cike da mamakin ganinsa.
"Ke ni wa na sani a cikinku, YaYa Aaminat na kawo, an aikeni ne shine na rage mata hanya" a take annurin fuskarta ya ɗauke ɗiff ta taɓe baki ta ja hannun Fiddausi. Zagayawa ya yi ya shiga mota ya na mamakin sa ido irin na mutane, ya na ankare da tinda ya zo ya tsaya kowa idanunsa na kansu, har ya koma gida tsaki yake ja gabaki ɗaya duniyar ta yi masa zafi, Abdulkareem Na Tsaneka idan ya tuna kalmar sai ya ji kamar ya yi hauka sabi da zafinta da yake ji.