Sashe 6
Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau su na zaune su na hira Abdulkareem ya ke cewa, "Wai Kwanan nan naga Walid ba ya yi min magana, ko wasa ake yi da shi idan na shigo sai ya fita, me yasa haka???" Kowa ya ja bakinsa ya yi har sai da Abdulkareem ya ƙara maimaita tambayarsa sannan Amiyo ya ce "Ni fa ba zan ɓoye maka ba wallahi, munafukan ba sa son gaya maka gaskiya shi ya sa ka ji sun yi shiru." Abdulkareem ya ce "Yauwa Mutumina zo ka zauna kusa da ni." Amiyo ya furmutsa tsakiya ya zauna sannan ya ci gaba da cewa "In gaya maka, ba ramar nan ka zane ƙanwarka ba? to ai shine ya ke jin haushinka wai shi sonta yake". Abdulkareem ya yi dariya kafin ya ce "Ita Ƙanwar tawa ya ke so??" Amiyo ya ce "Ƙwarai da gaske, kar ka ƙara kar ka raga hakan ne ya sa ya ke ta jin haushinka." Abdulkareem ya ce "Lallai ma yaron nan, bar ni da shi zan ji da lamarinsa." Muktar ya ce "Kai kuma da tsinin bakinka ya gaya muku sirri amma ka zo ka kwashe ka faɗa." "To zaman munafurci da cin Amana kake so ayi da ni? aa ba zan iya ba" Abdulkareem ya ce "Kar ka damu Amiyo gwara da ka faɗa min ai, wai ni kam Ya akai naga Chokali yau ba iyayin nan?
"Cokali Cokali!" wai lafiya ka zabga ta gumi?" Bilal ya tambaye shi, kallon shi kawai ya yi ya ƙara maida kai ƙasa, Amiyo ne ya ɗanyi ƙasa da kai yace "Babarsu ce ba ta da lafiya" da sauri Abdulkareem ya dafa Abokin na shi cike da damuwa ya ce "Haba Haisam mene amfanin zaman mu waje ɗaya in har ba za mu magance matsalarmu ba? kamata yayi ka sanar min tun wuri mu kaita asibiti" tashi yayi ya run gume Abdul yana kuka "nagode Allah ya ƙara arziƙi " Abdulkareem ya murmusa "karka ƙara yi min godiya, babu godiya tsakaninmu maza kaje ka ce su shirya za mu tafi Asubiti" da ' to" ya amsa sannan ya nufi gidan nasu, ɗaki ya shiga ya tarar da Sumayya ƙanwarsa se faman kuka take tana shafa mata ruwa cikin rawar murya ya ce "ki kintsa Inna za a kaita asibiti" to tace tana tashi.
tuni Abdulkareem ya fito da mota yana jiran fitowarsu Sumayya ce ta rungumo ta suka fito
murfin motar ya buÉ—e suka shiga da Inna, Haisam ya shiga gaba
shima ya shiga ya tada motar ya fara tafiya cikin nutsuwa duk da sauri yake amma hakan be hana shi bin hanya a hankali ba
se faman jerawa Inna sannu ya ke har suka isa A.I HOSPITAL Asibitin Daddansa duk da babu wanda ya sani cikin Abokan na shi.
danda nan aka bawa Inna gado likitoci guda uku ke kanta suna ƙoƙarin ceto ranta.
"Ummi ki ƙara kiran shi na kira ba a ɗauka inaga baya kusa ne" Nana Kadija ta faɗa cike da damuwa,
wayar ta ta É—auka kai tsaye ta danna wa shalelenta kira
dede lokacin Abdul ya buɗe ƙofar motar ze ɗauki waya
ganin sunan Ummi ya baiya na akan fukar wayar yasa yayi saurin ɗauka ya kara a kunne, Muryar Ummi ce ta daki dodan kannan shi tana cewa "ɗana kana ina? ina ka shiga?" "Ummi ina Asibiti Maman Cokali ce bata da lafiya" "ayya Allah ya bata lafiya waye kuma Cokali?" "Haisam Aboki na Ummi" "to jikin da sauƙi ko?" "eh Ummi mun ma kusa tahowa in sha Allah" "to Allah ya ƙara lafiya se kun dawo kakula ka ji?" "to Ummi.
daga haka su ka yi sallama ya koma ciki
Cike da fustara da rashin kunya Fati ta ke cewa "wallahi sekin biya ni kuɗina wa yace ki ɗaukar mini?" Aaminat ta ce "dan Allah kiyi haƙiuri ranta nayi in na samu zan baki" "taɓ baki isa ba yanzu zaki biya ni kuɗina ko mu daku" jin Fati ta kira dakuwa yasa Aaminat zaro ido ta sani zata aikata,
Umaima ce ta shigo dakin tana cewa "ke ƙaramar Bazawara zaki biya ko se mun fara salawaitun bala'i ne" "kuyi haƙuri zan baku in anjima" "wallahi yanzu zaki bani kuɗina ko na faɗawa Abba kin satar min kuɗi" "Haba Fati kin sani bana sata kar kiyi min ƙazafi zan biyaki kuɗinki, yanzu ba ni da su ne in da akwai ai da ban kai ga ɗaukar nakin ba" "to biyani" rausayar da kai tayi tana tunanin inda zata samu kuɗi ta biya Fati
tunawa tayi da Siyama ta yi saurin miƙewa ta na faɗin Alhamdulillah.
Fati ce ta cakumi wuyan Aaminat ta na cewa "ina za ki je baki biya ni b? wallahi babu inda zakije se kin biya ni!!" ta ƙarasa maganar cike da bala'i. cikin muryar kuka tace "zanje gidan su Siyama na aro na biya ki" "koma ina ne muje tare" kibari na kawo miki karki bini dan Allah" murgu ɗa baki tayi tace "maza ina jira ki da wo"
Umaima tace "kuÉ—i ne de se kin biya shi ehhe"
Aaminat ta ce "To sakar min wuya sai in tafi." "Abin ya ci tira ma bayan takura har da sata Alawadai da wannan zawarci, azo a damu iyaye a damu ƙanne yanzu ma an fara sata, Ba dan Allah ya tona miki asiri ba da tuni shi kenan kin sha ni na warke" Fati ce ta ke zazzaga masifa hannunta riƙe da ƙugunta har wani ɗan girgiza take yi, Aaminat ta share hawaye kafin ta ce "Kar ki fitar da ran kema Allah zai jarrabeki Fati, nima ban taɓa tunanin hakan ba gashi ta faru da ni." "Allah i kyauta ya kare hawala, ai wallahi ni nafi ƙarfin zawarci na riga na bashi baya, ke dai da baki da daraja ke Allah ya ɗorawa amma ni wallahi ko tawo mu gama ba zan taɓa yi da shi ba, ya ƙare dai akanki. Umaima ta ce "Ato wallahi fa" Aaminat ba ta ƙara ce musu komai ba ta fita domin samo rancen ta biyata ta huta.
Fati da Umaima kuwa zancenta su ka dasa Umaima ta ke cewa "Ni fa wallahi har ba na so ma ta ƙara yin Aure yanzu kinsan sabi da me?" Fati ta ce "Sai kin faɗa, ni dai na fi so naga ta kauce ta bamu guri don wallahi wannan kashe mana kasuwa za ta yi, ba dan ita ba ma ai da yanzu batun Aurenmu ake yi, amma komai sai dai ace Aurenta ita kuma na lura Tafi son me Ido a tsakiyarka (Duniya)" Umaima ta ce "Ke baki kwashe ba dalla, ni aikin da take yi mana ne ya sa ba na son Auren nata, kinga ba ruwanmu da wanke-wanken safe ba na Yamma, girki ma ba kullum ba, share-share kullum sai dai ta yi mu ɓata, shi yasa fa ba na son ta tafi." Fati ta yi dariya gami da ɗakawa Umaima duka a cinya ta ce "Shegiya ke kin gano laƙabin ashe, wallahi fa haka ne, nima sai yanzu na gane amma fa kamata ya yi mu muna da samarinmu Aurenmu za mu yi ita kuma ta na yi mana aiki, kin ga sai ta ƙare a Aikin wanke-wanke, kinga wannan Bikin da za ayi na Ƴar Umma Sa'a? wallahi dagewa Za mu yi mu samo Samari masu aji da kuɗi a Wajen Dinner nan kin ga ai mijin Umma Sa'a ya na da Ƴan Kuɗaɗensa, nasan shima wanda Bilkin za ta Aura hakane, to a ciki za mu ƙure wanka mu zaɓi santalele mu yi wuf da shi" Su ka yi shewa su ka tafa kafin Umaimai ta ce "Wallahi kanki ya na kawo wuta My Sister, ayyiriri!!! ai sai dai ki ji ana mana buɗa, ni kuwa za ta iya zuwa bikin nan ma?" "Sabi da me ki ka ce haka?" "To ai naga ba ta ƙaunar shiga jama'a itama kanta kunyar kanta take. Fati ta ce ''Ba lallai ta je ba kuwa, musamman Dinner ɗinnan, yo mutum ne kamar mujiya ba farin jini." Umaima ta ce "Allah i sittira to" Shigowarta ce ta katse musu hirar, ta miƙawa Fati kuɗin gami da cewa "Ga shi nan ai ba a rasa masu tausayi, tin da ku ƴan uwana ba ku tausaya min ba na samu me tausayina." Fati ta yi mata kallon tara saura kwata ta ɗiba ta watsar ba tare da tace uffan ba, Umaima ta ce "An dai ji, tinda kin biya kin huta da kin yo aman su a gurin nan" cike da takaici ta ce "Umaima uwa ɗaya uba ɗaya mu ke ni dake amma kin ɗauki Tsana kin ɗora min sabi da jarrabawa ta same ni, wai ba ku san ƙaddara ba?" Umaima ta buntsira baki gaba ta murguɗe ɗankwalinta ta ce "Ai ba wani ne ya ce ki kaso Auren ki zo ki dame mu ba." "Wallahi da kunsan waye Kamal da ba za ku dinga cewa na kashe Aurena ba" ta yi maganar ta na sharar ƙwallah, cike da rainin hankali Fati ta ce "Allah sarki!"
shiru ta yi musu su ka ci gaba da Æ´an maganganunsu.
Yau ta kama ranar Wunin Bikin Bilkin Umma Sa'a, sai yamma liƙis ta shirya kowa ya tafi ya barta don babu ma wanda ya ce ta shirya kawai dai ta yi ra'ayin zuwan ne duk da ba a gaiyaceta ba. Riga da Sket na Atamfa ta saka sun kama jikinta sosai, ta yi ɗaurin ture ka ga tsiya ta yafa mayafinta akan kafaɗarta, kamar ko da yaushe iya Kwalli ta saka sannan ta zura Plat Shoe ɗinta, kayan duk sun takure ta kamar ta cire har ta koma za ta canja wata Zuciyar ta ce kibar kayanki, ta ɗauki mukullin gidan ta rufe sannan ta fito.
a hankali ta ke tafiya kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki, tunanin Kamal take yi, ko shakka babu ya taka rawar gani wajen tarwatsa mata farin cikinta, indai ana samun maza irinsu to fa kowace mace ma za ta iya fuskantar rayuwa ta garari kamar yadda itama ta fuskanta.