← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 38

Sashe 5

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Abdulkareem tin da ta yi gaba ta barshi ya kasa gaba ya kasa baya, Haisam Cokali ne ya iso gurin cike da iyayi da kwainane irin nasa ya ce "Master Allah i sa dai lafiya don wallahi gani na yi idanunka sun kawo ruwa." Abdulkareem ya numfasa ba tare da ya ce komai ba ya koma jikin gatangar gidansu ya jingina gami da zubawa guri ɗaya ido, Haisam Cokali ya ce "Wallahi daga gani yau Maza sun sha fama don kuwa gabaki ɗaya rauninka ya gama baiyana Oga" tsaki Abdulkareem ya ja kafin ya ce "Cokali zan Ɗauraye hannuna in kikkifa maka Mari wallahi". cikin sauri ya riƙe haɓa gami da cewa "Ni Ɗan nan rufani ka saya ni, abin ai bai yi zafin haka ba, maida wuƙar Allah i bada haƙuri ni tafiya ma zan yi." Abdulkareem ya ce "Haisam wai don Allah ka lura akwai wata cuta da take damuna?? ni ina ganin kamar lafiyata ƙalau ko ina alamun hauka?" Haisam ya tuntsire da dariya ya yi shewa ya tafa hannuwa sannan ya ce "Master namu Allah ya barka, to ai ni duk layin nan a Samari dai har ƴan shekara Talatin banga me hankali kamarka ba, kumw lafiyarka ƙalau tinda ba zazzaɓi ba ciwon kai." girgiza kai ya yi a sanyaye ya ce "Ta na da gaskiya sai dai na kasa gane kowane irin ciwo ne, nima kaina na san ba ni da lafiya". "Allah Sarki Master, don Allah sa ranka a inuwa ka je ka yi Sallah, ba ka jin Masallacin gidanku ma anyi kira??" Gyaɗa kai ya yi ba tare da ya ce komai ba, ya nufi cikin gidan.
bai bi takan kowa ba ya yi Alwala ya bi Jam'in Sallar bayan an Idar ya shige cikin gida. ba shi ya fito ba sai yamma liƙis lokacin har an gama kasa Ƙwallo shi ake jira, ya na fitowa kuwa su ka fara.
Sun yi nisa cikin wasan Nana Kadija ta tawo tsogal-tsogal ta sha ado cikin wando ja Da baƙar Riga iya guiwa wadda aka yiwa adon duwatsu ta yi Rolling da ɗan ƙaramin Mayafi Ja, sai Glass No Respect baƙi ta haɗe girar sama da ta ƙasa, tsaki ta ja ganin sun cika layin su na Ƙwallo kamar mallakinsu, Walid ne ya kula da zuwanta ya ɗaga murya ya na cewa "Ku tsaya a wuce!" Banza su ka yi masa har sai da Abdulkareem ya ce "Dalla ku dakata mana ko bakwa gani ne?" su ka tsaya su na kallonta, ita kuwa ta girgiza sannan ta ci gaba da takawa kamar me tsoron Ƙasa, sai da ta zo saitin Abdulkareem sannan ta ja wani dogon tsaki ta tsartar da yawu ta bashi wani banzan kallo sannan ta yi gaba. cike da mamaki ya bi ta da kallo ya na cewa "Kaii!!?? ke zo nan, ni za ki kalla ki yiwa tsaki harda tsartar da yawu?" ta juyo a fitsare ta ƙare masa kallo sannan ta kuma wani tsakin, Muktar ya ce "Haba Master ba da kai take ba da mu take fa, ƙyaleta kawai." Fuska ya haɗe ya ce "Ku tara min ita in ji in ni sa'anta ne." Walid ya ce "Me za ka yi mata to? ka ƙyaleta mana ai ba da kai take ba." "Wallahi in ta bar sashin nan ba ku tare ta ba sai ran kowa ya ɓaci" ya na rufe baki su ka bi bayanta su ka sa ta a tsakiya, ya yi tsalle ya tsinko ƙaramin reshen bishiyar da suke ƙarƙashinta ya gyarata sannan ya nufi inda suke, Sai tsiwa take zuba musu bakinta ya ƙi mutuwa gashi sai keɓe baki take yi ita a dole ƙyamarsu take. buɗa masa su ka yi ya shigo tsakiyar ganinsa da bulala ya sa ta zaro ido ta na cewa "Wai meye hakan??" bulalar ya shiga sauke mata a gadon bayanta, tin ta na mazewa har ta fara kuka ta na roƙonsa, sai da ya daka iya son ransa sannan ya ce su bata guri, su ka buɗa mata hanya, Abdulkareem ya ƙara zuba mata ɗaya gami da cewa "Ƙetare Ƴar Bantan Uba ta Danƙi Harawa." Nana Kadija ta tsallake da gudu, duk ta watsar da iyayin nata ta fara gudu, ba ta tsaya ba sai da ta shige gida, ta je da kuka yare-yare.
Abdulkareem kuwa ko a jikinsa ya ce su ci gaba da Ƙwallon.

sai bayan sun tashi ya koma gida ya tarar da ita har lokacin kumburi take, ta yi murjai-murjai. Ummi ta ce "Babban Mutum me ya haɗaka da Nana Kadija??" "Au wai zuwa ta yi ta ce na daketa??, to me yasa ba ta gaya miki abin da ta yi min ba?" Ummi ta ce "Ba tambayarka na yi ba?? ka kama Budurwar Ƴa a gaban Yara ka zaneta haka ake yi??" "To Ummi tin da ba ta da kunya ai wallahi fin haka ma za ta samu, wai fa kallona ta yi ta min tsaki ta tsartar da yawu, ƙarshe dai kinsan cewa za ta yi wai ina wasa da ƳaƳan Talakawa, to ina ruwanta? ki ga ta na yawo a layi kamar figaggiyar tantabara ita a dole Ƴar Masu kuɗi, na bi kuɗin da gudu ba Silifas, sai na karya mata ƙafa idan ta ƙara yi min irin wannan iskancin" Cike da tsiwa ta ce "Eh ɗin ni na fi figaggiyar tantabarar ma, aikin kawai ba dole ma ka sa a dinga raina mutane ba ka na shiga cikin ƙazaman can kuna wasa, wai Ummi ba za ki hana shi wasa da su ba? Kuma wallahi Ummi indai ya ƙara dukana sai na rama ai jiki bai fi jiki ba, kwata-kwata shekara uku fa ko huɗu ka bani shine za ka maidani kamar ƴar cikinka, to wallahi ba ka isa ba." "Idan kin gama surutun sai ki tashi ki rama yanzu ai ga jiki ga tsoka, ko da minti Ɗaya na girmeki ai na girmeki dai, kuma ni Namiji ne a Matsayin Ubanki nake ɗaukar kaina." rasa abin cewa ta yi don haka ta ƙara fashewa da kuka, Ummi ta ce "A gaskiya Auta ni kaina raina ya ɓaci, abin ya isa haka Nana Kadija fa ta girma, Sakuwarka ce fa, ka dena Dukanta don Allah musamman dai a waje gwara ma a cikin gida ya fi rufin asiri, ba ka san ma idan mace ta girma dena dukanta ake ba?" "Wannan ƴar Ummi tinda ba ta yi hankali ba ai kuwa ba ta girmi duka ba." ya faɗa gami da yin gaba ya basu guri don ya gaji da jin gunjin kukan nata.
Ummi ta ce "Allah i shiryeka to" Nana Kadija ta ce "Wallahi Ummi bakwa son yi masa faÉ—a ne shi yasa duk ya bi ya addabi kowa." Murmusawa Ummi ta yi kafin ta ce...

© INDO & AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)

Littafin Haɗaka ne💪🏾

Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S

Tare da

Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S

Shafi 5

"Ba ya aikata abu mara kyau, shi yasa za ki ga kamar ba a son yi masa faÉ—an ne, ba za ki gane hakan ba sai kin sawa kanki nutsuwa.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya a kowane ɓangare ba wani sauyi.
Aaminat Kullum jiya i yau ne ba ta da lokacin farin ciki, ko da ba ayi mata komai ba idan ta yi tunanin rayuwarta ita kaÉ—ai sai ta kama kuka.
Chapter 5 · 0% Book details