Sashe 15
Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Aaminat ta doka tsaki kafin ta ce "To sai me? ko a bakina ka ji baƙaƙen labaran? ina da asara ne ni ko sun yi ma ko ba su yi ba?" Ya yi murmushin takaici gami da cewa "Hmm!!! Aaminat! a tunanina kinsan martabar SO kuma kina sauraren Huɗubar Manya na cewar ka so me sonka, a bakin kowa za ki iya jin wannan furucin me yasa ba za ki ɗauki wannan Nasihar ba? Wallahi ba na wasa da soyayyarki tsakanina ga Allah ina sonki kuma ina son Aurenki; ko da a yau ki ka Amince a Ɗaura a shirye nake, kinsan na riga na mutu akan sonki amma ki ke saurarar wani gaja da bai son inda ke masa ciwo ba?" a fusace Aaminat ta nuna shi da yatsanta manuniya gami da cewa "Kaii!!! ka shiga taitayinka wallahi ka kama kanka tin kafin ka tsinci Juma'arka a Laraba, banda ba ka da kunya wai ka kalli tsabar idanuna ka ce ka na sona? kai ba dan nasan daga gidan Daraja ka fito ba da ka sha wankin Rashin Mutunci a gurina, duk haƙurina ka fara kaini ƙarshe zan rufe ido in yanka maka tikitin rashin Mutunci" ta ƙarasa maganar ta na raka shi da wani mugun kallo wanda ya ke ƙara murtsika Zuciyar Abdulkareem, a take idanunsa su ka sauya kamanni, ya girgiza kai alamar a'a sannan ya ce "Aaminat Ko a yau nace zan Aureki zan iya sai dai ba na so na Aureki ta hanyar tilastawa domin ina matuƙar Tausayinki kuma ina darajaki in banda haka da ko ta wane hali sai na Aureki." "Sabi da Auren abin banza ne? me ka ɗauke ni ne? ka yi kuskuren raina Ƙarfin Ƴa mace wallahi, ina fa da Ƴanci Abdulkareem!" ya yi murmushi gami da shafar ƙeyarsa ya ce "Hmm!! Aaminatu tawa, kin yi kuskuren raina Hatsabibancin Ɗa Namiji musamman akan abin da ya ke so; Ta sigar lumana na ke so komai ya faru don haka na ara miki lokaci ki gama sha'aninki ki dawo gareni." Mewtch!! ta buga tsaki ta yi gaba ta na cewa "Saurararka ma ɓatawa kai lokaci ne." "Aaminath I Love U!"ya faɗa tare da raka bayanta da ido, duk da ta ji furucin nasa har cikin ranta amma ta ƙi juyowa ta ci gaba da tafiya gabanta na wata muguwar faɗuwa a kai a kai. a diririce ta shige gida dan kuwa zuwa yanzu jikinta har rawa yake bata bi takan kowa ba tashige ɗaki,
"Aaminat! Aaminat!!" Mama ta ƙwala mata kira tana ce wa kina ina zonan ki karɓi wankinnan da su fati suke dama ke ya kamata kiyi dan kuwa su yanzu su ke zamaninsu" "Yasalam" ta furta tana dafe kanta wata sarawa yake mata jitake kamar ta mutu ta huta sede babu yadda zatayi haka zataje tayi wankin, ta shi tayi tana haɗa hanya labulan ta bankaɗa zata fita taji sallamar yaya Hamza da sauri ta tsaya tana zazzaro ido danda nan bugun zuciyarta ya ƙara tsananta.
"Ummi ya kamata ki ɗauki mataki akan ya Abdul dan kuwa komai ƙara ta'azzara yake dan ɗazu kuka natarar ya nayi" Nana kadija ta faɗa fuskarta cike da tsagwaron damuwa, numfasawa tayi kafin ta ce "nima nalura kullum lamarin nashi ƙara taɓarɓarewa yake ya dena cin abinci kuma na rasa meke da mun shi" shuru suka ɗanyi na wani lokaci kafin Hauwa'u ta ce "Ummi nakira Anti Maryam ta ce suna hanya" tsaki kadija tayi tare da cewa "wai ke kina hauka ne yanzu se kija tazo itama ta biyemai mukasa gane kansu" Ummi kuwa ta faɗa duniyar tunane tunane, Abdulkareem Abdussalam Abdurrahim Abdulmajid suka shigo tare da sallama cikin shiga iri ɗaya riga da wando baƙaƙe sunyi bala'in kyau sosai yayin da tsantsar kamarsu ta ƙara bayyana, zama sukayi kusa da Ummi Abdulkareem ya tada kai da cinyar Ummi Abdulmajid kuwa gefenta ya kashingiɗa Murmusawa Ummi tayi tare da ce wa Allah yayi muku albarka ya shirya mini ku Allah ya karemin ku a duk inda kuke Allah ya kauda idon maƙiya daga kanku" da Ameen suka Amsa baki ɗaya shuru ne ya ratsa na ɗan lokaci kafin Kadija ta ce "Na ga ka yi jan Ido Mutumina, wallahi ka rame." Cikin takaici da baƙin ciki ya zuba mata harara aransa ya na tunanin tsawwalawa irin ta ta duk ta bi ta dame shi a memakon ta barshi da Iyo a Kogin azabar da Aaminat ta jefa shi.. ya fara tunanin Kalmar da zai bata martani Abdussalam ya riga shi da cewa "Ke kuma Jar Munafuka ko? ba ki da magana sai can na yi masa ciwo sai ka ce jikinki." cikin sauri Abdulkareem ya ce "You're Right, I Like You Wallahi." Nana Kadija ta cika baki da iska gami da ɗauke musu kai cike da takaici, a ranta tana cewa "Ai gaskiya na faɗa kuma na damu da damuwarsa ne ba wai takura masa na ke yi ba." Abdulmajid ya ce "Zaginmu ki ke ne??" Zaro ido ta yi cikin sauri ta ce "Ni na isa?" Abdulkareem ya yi ƙwafa kafin ya ce "In Mutum ya isa ya gwada mana." ta raka shi da hararar ƙasan ido ba tare da ta ce ƙala ba. Hira su ka ci gaba da yi ana yi Abdulkareem da Nana Kadija su na faɗa kamar tagwayen Kaji.