← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 38

Sashe 11

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aaminat kuwa jiri ne ya ɗebeta ta yi luuuu zuwa ƙasa, ta faɗa jikin bango sannan ta zame ta yi zaman ɗaɓaro, kukan da take ma ta dena ta zubawa guri ɗaya ido ita ba a sume ba ita ba a daidai ba.
Hankali tashe Siyama ta yo kanta ta na cewa "Aaminat!! lafiyarki ƙalau kuwa?? ki rufa min asiri ki tashi." jijjigata ta shiga yi ta na cewa "Aaminat! Aaminat don Allah ki tashi ai ya tafi." Wasu zafafan hawaye ne su ka samu nasarar gangarowa gefen idanunta, cikin disashshiyar murya ta ce "Siyama Abdulkareem shine ajalina, nasan dama ba zai taɓa ƙyale ni ba har sai ya gama yi min illah." Siyama ta girgiza kai ta na sharar ƙwallah ta ce "Ba haka bane Aaminat, kinsan a rayuwa kowa da irin fahimtarsa wani ba ya ganewa amma nasan wata rana zai fahimce ki zai dena shiga rayuwarki." Aaminat ta yi shiru sai kuka mara sauti da ta ke yi. Siyama ta tashi da sauri ta nufi Firji ta ɗakko mata Fiyowata duk da ba wani sanyi gareshi sosai ba, miƙa mata ta yi gami da cewa "Ki sha ruwan nan nasan Zuciyarki za ta ɗan yi sanyi, don Allah ki yi shiru ki dena kuka, wallahi ita damuwa ba yin kanta take ba sai dai in mutum ne ya so yinta, ki cire shi daga tunaninki bai isa ya yi miki abin da Allah bai yi ba, mu yi ta addu'a Allah zai kawo mana ƙarshen matsalarmu, ki yarda da ni Aaminat ni fa Aminiyarki ce." ruwan ta karɓa ta sha ba da yawa ba ta ajiye sannan ta ce "Temaka min in koma gidanmu Siyama." Siyama ta tashi ta miƙo mata takalmanta ta gyara mata zaman hijab ɗinta sannan ta temaka mata zuwa gida.

©️ INDO & AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)

Littafin Haɗaka ne💪🏾

Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S

Tare da

Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S

Shafi 9

Ya na kwance Kan Gado ya ɗora Filo ya rufe fuskarsa kamar me bacci, Nana Kadija ce ta shigo ta na ƙwala masa kira, "Auta kai Auta! Auta!!" tsaki ya yi yace "Ki tafi bana son takura" "babu inda za ni se ka tashi" "nace ki tashi ko?"
"haba kai kuwa wata gulma nazo in ɗan gutsura maka" "Nana ki fita kar na mareki" cikin tsiwa tace "Mari? ka daɗe baka mareni ba kawai daga magana se mari ɗan halak ka fasa, Don ka ga ma ina lallaɓaka" banza ya yi mata ya toshe kunnensa da hannun shi yana cije leɓe, masifa ta ci gaba da yi tana tafe tafe wai dole ma ya tashi ko su daku, ganin be ce komai ba yasa ta saduda ta fara tunanin ko bashi da lafiya, fita tayi da gudu ba ta daɗe ba ta dawo da magani a hannunta, ta zauna kusa da shi sannan tace "Ya Abdulkareem ga magani" ta shi ya yi ya zauna sannan ya kamo hannun ta yace "lafiya ta lau, ina son hutawa ne yau shiya sa, kinji zuwa anjima in na tashi se mu dakun"
murguɗa baki tayi tace "oho de ruwa ya daki babban zakara" murmusawa yayi gami da cewa "to koma mene ki je zuwa anjima ma yi shi" jiki a sanyaye ta ce "Amma Ya Audu gaskiya fa ko lafiyarka ƙalau akwai abin da ke damunka, ranar nan su YaYa Abdulmajid sun tambaya na hau bayanka na yi ɗare-ɗare amma yanzu na ga abin ya yi yawa wallahi." "Na rantse da Allah Kadija kawaici kawai na ke miki, idan ki ka ji Biyar ɗina a kumatunki inaga za ki fi fahimta ta, na ce miki ba na son hayaniya. ba ta ce komai ba ta fita saƙol jikinta ya yi matuƙar sanyi dan ba haka ta saba ganin shi ba,
kai tsaye ta nufi É—akinsu tana tafiya tana tunane tunane.

Aaminat
ta yi kukan har ta gaji sai dai na zuci, sabi da bakin ciki da damuwa Zuciyarta a koda yaushe zafi ta ke yi, don kuwa kalaman Abdul sunyi matuƙar tsaya mata Aaminat I LOVE YOU in ta tuna wannan furucin se ta ji kamar ta haɗiyi Zuciya ta mutu, zuwa yanzu ji take duk duniya babu wanda ta tsana sai su biyu Daga Kamal sai shi, a cewarta Kamal ne ya yi mata silar da har Ƙanin Ƙaninta ya dubi tsabar idon ya ke gaya mata Kalmar So.
kuka ne ya kufce mata yayin da take riƙe da carbi tana Azkhar, ta shiga rera shi tana roƙon Allah i yanke mata wahala ta huta koda sauƙinta shine Mutuwarta ta zaɓi hakan"

Fati ce ta kalleta ta tuntsire da dariya ta ce "Haba Zawar dariya ma wahala ce bare kuka, za ki gaji ki dena ne" dariya suka sa ita da Umaima kafin Umaima ta ƙwace carbin gami da cewa, "Dalla tashi ki ɗora mana girki kin wani zauna kamar wata Malama se jan carbin munafurci ki ke yi" Aaminat ta kalleta cikin muryar kuka ta ce "meyasa kike min haka?? karki manta ni fa yayarki ce Uwa ɗaya Uba ɗaya ko wani ya gujeni sabi da ƙaddara ai ke be kamata ki gujeni ba, kuma ƙaddara ta na kan kowa!!"
shewa suka saki kafin Fati tace "ai muda ƙaddara se kallo daga nesa dan kuwa zaran ba Kalar Yadin bane na gaba yayi gaba wallahi mu ai babu lissafin ƙaddara cikin rayuwar mu" Umaima ta ce "Wallahi ni banga wata ƙaddara a tare da ke ba, kashe Aure ki ka yi don ki dinga tara samari masu kuɗi kuma sai aka yi sa'a ba a gamu ba, in da ba son zawarcin ki ke ba ai da kin yarda da waɗanda Abba ya ke nemo miki." wani kallo Fati tayi mata na kinyi asara gami da taɓe baki ta ce "Wallahi fa kin yi gaskiya Umai." wani kukan ta saki sabo tana da nasanin zuwanta duniya.
jin Sallamar ya Umar ce tasa su tashi dan kuwa yana jin motsin su ze fara faÉ—a meyasa ba suje makaranta ba,
fitarsu ta bata damar ci gaba da kuka me taɓa zuciyar me saurare.

Tin tana hawaye har sun ƙafe idanuwanta duk sun kumbura sunyi jawur sai ya ji su ke mata kamar an watsa musu dakakken barkono, ga matsanan cin ciwon kai.

Su na zazzaune kan Babban Carpet wanda suke shimfiÉ—awa su zauna, Salim ya lura da tunda suka zauna hankalin Guda baya jikinsa sai ya ji shima jikinsa ya yi sanyi, "ÆŠan Ummi ya dai?? tunanin me kake kai da ka Tara an Tara maka, kuma tunanin me zakayi??" murmusawa yayi ba tare da yace komai ba ya bisu da kallo.
Cokali ne ya ɗan matso kusa da shi sannan yace "wato ainahin me yake faruwa ne kwana biyu ka dena walwala ɗan abincin da kake fito mana da shi ba kullum ba yanzu" "kai de kamar maye haka kake kaje kaci na gidanku mana" Jabir ya faɗa yana tallewa Haisam ƙeya ganin Abdulkareem ba shi da niyar yin magana ya sa suka fara musu wasu suce bashi da lafiya wasu suce muskilan cin shi ne ya motsa, jin hayaniyar ta su tayi yawa yasa ya tashi yana cewa "ni zan shiga cikin gida in na fito to in kuma se gobe to" gabaki ɗaya suka tsaya da surutun cakkk suka bishi da ido suna mamakin canzawar Master ɗin su lokaci ɗaya, cikin sanyin jiki Haisam yace "wai laifi mu ka yi maka ne?? kwana biyu kadena zama cikin mu kullum kana gida ko baka da lafiya ne??" gargiza musu kai yayi alamar lafiyar shi lau,
"to se munji ka nima gida zan tafi" Jabir ya faɗa cike da damuwa, marmushin yaƙe yayi ya ɗaga gira ɗaya sannan ya juya, Walid ne ya dakatar da shi ta hanyar cewa "Guda ko de rabuwa zakayi ne damu??" cakkk ya tsaya shi bai tafi ba shi ba dawo ba kuma bai bashi amsa ba, Walid ya ƙaraso inda yake, ya na shirin yin magana Abdul ya riga shi, ya na murmushin karfin hali yace "Ba haka bane Ɗannan me ya yi zafi da zan rabu da ku bayan ku sashi ne na rayuwata? wai ni kam ina yayarka ne??" Walid ya ɗan ya mutse fuska kafin yace " tana gida bata da lafiya, kuka ne aikinta kullum, duk ta bi ta damu ni bansan me akai mata ba, gashi su kuma ƴan gidanmu kowa harkar gabansa ya ke yi an rasa me kaita Asibiti ma ba wanda ya damu da ita, ni wallahi duk jikina ya yi sanyi bansan me ta yi musu me tsanani haka ba, wai ko Abba babu ruwansa da tambayar ya ta kwana ya ta tashi" rassss gaban Abdukareem ya faɗi har ƙasa, ya wararo ido ya na kallon Walid, ci gaba ya yi da cewa '' Wai kowa ya zare hannushi daga kanta, ni fa Da na zata laifi ta yi musu ashe kawai sabi da Ta rabu da Mijinta ne, ƙila ma ba ta da laifin komai." cikin dauriya Abdulkareem yace "to kace ina mata sannu kaji? to yanzu idan ka ce za ka rakata wajen likita ba za ta yarda ba?" Walid ya ce "Hmm! ba za ta yarda da ni ba don na riga na ɓata wasana tin farko sabi da rashin kunyar da nake mata, kuma gani na yi su Umaima na yi, ni kuma na zata abin kirki ne, tin daga ranar da ka yi min magana akanta na gane kuskurena." Abdulkareem ya ce "Okay Ƙyaleta kawai, Allah i bata lafiya." yana gama faɗin haka ya ci gaba da tafiya zuwa cikin gida.
Chapter 11 · 0% Book details