Sashe 10
Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Aaminat ta ce "Ni fa ban tambayeki sunan Maru buciya ba." Siyama ta yi dariya sannan ta ce "Eh na sani, amma ai labarin sai ya fi daɗi, ki na ji, Sunansa Muftahul-jannah ya na da yayye da yawa amma Ba Mamansu ɗaya ba, shi ƙanwarsa ɗaya mace Jannatiee, duk yawan yayyen nasa ba sa ƙaunarshi kamar mujiya haka su ka tsane shi, sai dai Babansa ya na son shi sosai itama Ummanshi haka, kullum ƙiyayyar da suke masa ta na ƙara yawa, gasu da son Zuciya da son abin Duniya, su na mugun jin haushin Babansu ya dinga nunawa Jannah Ƙauna amma ba yadda za su yi sabi da komai na baban nasu Jannah ne akan gaba, a kasuwancinsa ma Jannah ya ɗora duk da shine ƙaramin cikinsu, wai kin san abin Tsoron?" Aaminat ta girgiza kai, Siyama ta ce ''Wai sabi da Jahilai ne da su da iyayensi Mata su ka haɗa kai su ka kashe Mahaifinsu sannan su ka sa aka yiwa Ƙanwarsu Jannatiee fyaɗe, sannan su ka ɗorawa Jannah laifin, yanzun haka a halin da ake ciki kenan, sun jefa shi cikin gararin rayuwa, sun rabashi da Babanshi kuma sun yi masa sharri, sun haɗa masa azabu iri-iri shiyasa na ji kawai na fara kuka, yanzu anje sai Shari'a ake yi, sun ce ba za su yarda ba sai an ƙwatar musu haƙƙinsu a gurin Jannah, ki ji fa wani zalumci? ni cewa ma na yi anya kuwa Ƴaƴansa ne?? Yanzu Jannah ba shi da kowa sai Allah sai Ummanshi, Ƙanwarsa ma ta rasa tunaninta, ban san waye zai cece shi daga wannan Ƙangin Wahalar ba." jikin Aaminat ya yi sanyi, sai da ta ɗan yi gyaran murya sannan ta ce "Kai!! rayuwar nan fa akwai abin tsoro a cikinta, kasan yau ba ka san gobe ba, yanzu sabi da son Zuciya aka kashe masa Babansa, shi kuma tashi ƙaddarar kenan, ni kuma Allah ya haɗani da Kamal duk ya bi ya tarwatsa min farin cikina." Siyama ta yi dariya kafin ta ce "Allah Sarki Ƙawata, wato har labarin ya tsuma miki Zuciya, gaskiya akwai abubuwa da yawa a cikin Littafin, abin akwai ruɗani, ga ban tausayi, masifu iri-iri ya na ganinta Dogon Yaro, sun sha kai masa hari za su kashe shi Allah ya temake shi ya rayu, ƙila ma sai sun kashe shi ɗin don ko a Kotun nan nasan sai sun Yarda shine ya kashe Mahaifinsa kuma ya yiwa Ƙanwarsa Fyaɗe." Aaminat ta ce "Haba Siyama ta ya za ki ce haka bayan kinsan Allah ya na tare da me gaskiya?, ai tinda ya riƙe gaskiyarsa ba za su yi nasara akansa ba in sha Allahu." Siyama za ta yi magana Amiyo ya yi sallama, amsawa ta yi gami da binsa da ido don jin abin da ya kawo shi. ya ce "Siyama wai Master ya na son yin magana da ke." ido a zare ta ce "Master??? fa ya na nufin Abdulkareem." ya ɗaga gira ɗaya gami da cewa "Yessss!!" da mamaki ta ce "Amiyo zan ci ubanka ni kake ɗagawa gira?, to wai me zai ce min ne? ni fa ban yi masa komai ba bana son salawaitun Bala'i irin na Abdulkareem." Aaminat ta ce "Don Allah Siyama dena ambaton sunansa a gabana, ba na so." Miƙewa Siyama ta yi ta wawushi mayafinta ta yafa ta nufi hanyar fita ta na cewa "Allah i sa ba munafurci ku ka haɗa min ba, bansan hawa ba bansan sauka ba, nasan ba mutunci ne da shi ba." ya na raguɓe a jikin bango a ƙofar gidan ya yi wani sumul kamar ba shi ba. Siyama ta na fara'a ta ce "Guda ba Tsagi ba, Allah i sa lafiya ce ta sa kake nemana." murya a cunkushe ya ce "Ta ɓangarenki lafiya amma a gurina zan iya cewa ba lafiya ba." "To fa me ya faru??" ta faɗa cikin mamaki, "Siyama Aaminat! wallahi na yi mata laifi, tin daga ranar ban ƙara ganinta ba shi yasa duk na firgice wallahi, ta dena fitowa amma nasan idan ki ka ce ta zo gidanku za ta zo hakan zai bani damar ganinta." Siyama ta na shirin jirga masa Ƙarya Amiyo ya tari numfashinta da cewa "Master ai YaYa Aaminat ta na gidan su Siyaman, yanzu na ganta." Siyama ta kifa masa wata shegiyar harara, ya buntsire baki alamar ko a jikinsa. a marairaice Abdulkareem ya ce "Siyama don Allah don Darajar Ma'aikinsa ki yi min Izini in ga Aaminat, wallahi akwai damuwa idan ban ganta ba." ganin ya na neman fashe mata da kuka ya sa ta cewa "A'ahh ni fa ba na ƙi bane, kasan ni Ƙawarta ce ta yarda da ni, ka ga bai dace na yaudareta ba." "Ba za ta ga laifinki ba laifina za ta gani, ni kuma duk na yarda da hakan, idan ba za ta fito ba ki ba ni dama in shiga ciki don Allah." Siyama ta rausayar da kai kana ta ce "Zan jarraba kiranta idan ba ta zo ba sai ka shiga, amma ba da yawuna ba." "Na ji daɗi Siyam's , hankalina duk ya bi ya ɗaga na kasa control na kaina Laifi na yi mata kuma ina son bata haƙuri." Siyama ta juya ba tare da ta ce masa komai ba, a ƙasan Zuciyarta kuwa mamakin ƙarfin halinsa take, ba shakka yanzu ta fahimci mugun son ƙawar tata yake, a gefe guda ta na murna da hakan don kuwa za ta so Ƙawarta ta kauce daga Cikin Uƙubar da take, a gefe guda kuwa tsoro da fargabar rigima take don ta san Abdulkareem bai wuce Shekara ishirin da Ɗaya ba bai zama lallai iyayensa su amince ya yi aure a yanzu ba bare ma ya Auri Bazawara a matsayinsa na ɗan masu kuɗin nan. da wannan tunanin ta shiga cikin gidan ko zama ba ta yi ba ta isar da saƙonsa don tasan ƙarshe ma ko ta zauna sai ta tashi ta koma don Aaminat ba za ta amince ba, wani mugun kallo Aaminat ta watsa mata kafin ta ja tsaki ta ce "Siyama ba na son ki shiga sahun masu son lalata min rayuwa, ni kaina na kasa gane meye Manufar Yaron nan a kaina, ya na yi min wasu irin abubuwa da su ke bala'in rikita tunanina, ina tsoron ya bi Sahun Kamal don ba shakka Abdulkareem ba shi da burin da ya wuce ganin ya jefani cikin iftila'i da Azaba, indai har don gaskiya ki ke ƙawance da ni kuma ki na tausaya min to kar na ƙara jin sunansa a bakinki bare ma wani saƙo daga gareshi." Siyama ta numfasa sannan ta juya, ya na tsaye ya zubawa ƙofar gidan ido da alamu jiran fitowarsu yake ko ita ko Aaminat, Siyama ta ce "Guda Wallahi dogon Sharaɗi Aaminat ta ja min don haka ka temaka ka fitar da ni daga cikin zancen nan ba zan iya ba." bai ce uffan ba ya kutsa kai hanyar shiga gidan Siyama ta bashi hanya ya wuce gudun kar ya mazgeta don har ga Allah tsoronsa ta ke ji.
Aaminat ta na zaune a inda Siyama ta barta ta ji sallamarsa, cikin sauri ta miƙe ta na binsa da idanu cike da mamakin ganinsa, lallai rashin kunyar tashi ta ƙara yawa, abin har ya kai ya shigarwa mutane gida, katse mata tunanin ya yi da cewa "Aaminat ki yi haƙuri kuskurena ne amma ba zan ƙara ba..." dakatar da shi ta yi cike ɓacin rai ta ce ''Ya isheka Abdulkareem!! yanzu me ka yi? ka biyoni har cikin gidan mutane ka ga an samu shaidar cewa binbininka nake yi, ka fita kafin ranka ya ɓaci" "Ai raina ya gama ɓaci Aaminat tin da har na ɓata miki naki ran." fassss ta wanke shi da wani lafiyayyen mari, ta na kuka ta fara cewa "Na gaya maka na tsaneka, ka nacewa rayuwata sai kace ni kaɗai ce mace a layin nan? idan da gaske ka na tausayina ne me yasa ba ka tausayawa sauran Matan? Azzalumin yaro ka sa Umma sai fushi take da ni, ka ƙara min wata jarabar yanzu ance bin maza nake duk sabi da kai, na ce ka fita daga rayuwata iya zalumcin da ka yi min ya isa haka kar ka ƙara da wani, na tsaneka na tsani ganinka ko da sunanka na tsani ji." Sai da ta gama magana sannan ya sauke hannunsa daga kan kumatunsa da ta mara, idanunsa sun kaɗa sun yi jawur sun wani ƙanƙance, Zuciyarsa bugawa take yi a fusace tamkar za ta ɓalla ƙirjinsa ta fito, "Aaminat ba ki ji ba daɗi ba da ki ka saka hannu ki ka mareni?? Meye laifina don na shigo rayuwarki? shin na taɓa nuna miki halin banza ne? me na aikata da na cancanci wannan hukuncin daga gareki Aaminat?? kenan don sun yi miki Ƙazafi sai ya zama ni na sa su ko kina zaton zan iya aikata abin da su ke tunani ne? Aaminat na gaya miki gaskiyata ba zan iya fita daga rayuwarki ba kuma na zamo Ƙaddararki ba yadda za ki yi dani." shiru ya yi sabi da wani marin da ta ƙara zabga masa, jikinta sai rawa ya ke yau ta kai maƙurar fusata, cikin rawar murya ta ce "Ƙaddarata ma ta fi ƙarfinka balle ni, mugun nufi gareka a kaina ba alkairi ba, kuma ba za ka taɓa yin nasara ba, ko ina bin maza ma banga abin da zan bi a jikinka ba ba ka isa ba ka yi kaɗan, na gaya maka ka ƙyale ni tin kafin ka kai ni maƙura ka ƙi ji, yanzu na kai ƙarshe wallahi in baka bar gidan nan ba ko me na samu sai na buga maka na illata maka rayuwa ko ma na kashe ka!!." "I LOVE YOU Aaminat komai zafin azabar da za ki yi min har Abada ina sonki, Soyayya itace manufata akanki kuma na yi ɗamara da ita ba zan fasa ba, in kin so kar ki dena marina don ba na jin zafinsa ma kan yadda nake jin zafin kalmar ƙiyayyar da ki ke tofa min, kuma ko da za ki mutu ko ki kashe ni Ina Sonki, akanki idanuna sun riga sun rufe ba abin da ba zan iya aikatawa ba ki sa wannan a tunaninki." ya na kaiwa nan ya juya ya fice, Siyama da Amiyo su ka bashi hanya.
tafiya yake amma bai san inda ya ke tsomala ƙafarsa ba sabi da ɓacin rai, ya na da haƙuri kuma ya na da Zuciya sannan ya na da zafin rai, hakan ne yasa idan ya burkice ya ke fita daga haiyacinsa, kai tsaye Bedroom ɗinsa ya nufa ya faɗa kan gado.