Sashe 28
Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tuni hawaye sun wanke mata fuska, da sauri ta ɗauki waya ta kara akunne bugu ɗaya aka ɗauka, cikin muryar kuka da tashin hankali, ta ce "me...meyasa zaka barni alokacin da nake tsaka da buƙatar rayuwa da kai wallahi ina sonka" ƙit ya katse kiran sai a lokacin zafafan hawayen da suka cika ƙwarmin idon sa, suka sami damar sakkowa, ƙasa yayi da kai yana ambaton sunan Allah don samawa kansa sauki.
zuwa yanzu Aaminat ta gama fita hayyacinta kuka take mai tsuma zuciya Umma da Umaima kuwa sai faman rarrashin ta suke, Umma tace "kiyi haƙuri ki ɗauki ƙaddara haka Allah yaso daku" haka suka cigaba da rarrashin ta,
Mama da Fati kuwa ransu fafess sai nishaɗi suke suna ɓaɓɓaka dariya Mama ta kalli Fati kana ta ce "ni dama banaso ahaɗa bikinki da na Bazawarar can wallhi, sai gashi saurayin ma ya fece" dariya suka sa hada shewa,
Abi ne zaune a Falon Anti Zainab, Yarima ya shigo kai aƙasa, zama yayi kusa da Anti Zainab gami da cewa "barkan ku da dare " Abi ya ce "yauwa" Anti Zainab ta muskuta gami da cewa "Abi dama tun ɗazu nakeso zamuyi magana da kai" ya ce "to ina jinki" "dama batu ne akan Abdulkareem" Abi ya murmusa sannan ya ce "Abdulkareem yayi mini bayanin komai gaskiya abinda Aminina yayi bai kyauta ba, banji daɗi ba," Anti ta ce "to ya za'ayi sai haƙuri nima ya bani tausayi wallhi" tashi Yarima yayi, Abi ya dakatar dashi ta hanyar cewa "zo mana Abubakar" dawowa yayi ya zauna, Abi ya ce "Abdul ya roƙeni na taimaka masa na nema maka Auren Aaminat domin yana ganin zaka iya maye gurbin sa arayuwarta" ƙasa yayi da kai, Abi ya ƙara da cewa "kuma na yanke hukunci zuwa jibi iyayanka su Alhaji Kabiru zasuje gidan su yarinyar saika faɗa mata ta sanar da mahaifin ta" cikin rawar murya ya ce "to"
ya tashi ya nufi sashin Ammi,
Washegari da safe
ahankali Dadda yake sakkowa daga benen dake tsakiyar Falon gaban sa ne yayi wata muguwar faɗuwa ganin hawaye shaɓe-shaɓe afuskarta, da sauri ya ƙarasa inda take sai alokacin ya lura da takardar dake riƙe ahannun ta, hannu yasa ya karɓi takardar sannan ya zauna kan kujera ya fara karantawa,
kamar haka
"Salam Daddana da Ummina, tabbas ban taɓa zaton haka daga gareku ba, nayi tunanin zaku iya cika duk wani buri na ɗanku ashe ba haka bane, dama ƙaunar da kukemin ba har cikin zuciyar ku bace???? Uhmmm ban taɓa tsammanin hakan ba, nayanke hukuncin nesan ta kaina daku, nabar ku lafiya" wata zazzafar iska Dadda ya furzar cikin dakakkiyar muryar sa ta jajirtaccen Uban da ya amsa suna Uba, ya ce "kar hakan ya dameki kuma hakan ba zaisa na sauya ra'ayi na ba" yana gama faɗin haka ya juya zuciyarsa na wani mugun tar tsatsin azaba tabbass a zahiri bazaka taɓa iya gane iya tashin hankalin da Dadda ya shiga ba, a baɗini kuwa zaka iya cewa yafi kowa shiga tashin hankali dan kuwa tafiya yake a harabar gidan amma baisan inda yake jefa ƙafarsa ba,
*Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta*
*Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.*
*HALY-JASHERU venture's*
*munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.*
*prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA*
su Abdussalam suma suna ɗaki suna nasu zaman makokin, babu mai iya cewa ɗan uwan sa ƙala saidai kallon kallo su Farida kuwa sunyi kuka mai isarsu sun gaji, Kadija kam tun daren jiya ta haɗa kayan ta tsaf ta koma gidan Uncle Rabi'u,
"Aaminat ki daure kici abincin nan, ki fauwala wa Allah komai" Umma ta faÉ—a cike da damuwa,
Umaima kuwa tana gefen Aaminat ita da Siyama sun zabga tagumi sai muzurai suke,
haka kowa ne gida suka wuni cikin baƙinciki,
Bayan kwana biyu su Alhaji Kabiru da Baba Usman sukaje gidan su Aaminat suka gana da mahaifinta da ƙaninsa Baba Auwalu, cikin kamala suka bawa Yarima Auren Aaminat,
Haka rayuwa ta cigaba da garawa a kowane ɓangare.
Gidan su Abdulkareem kuwa har zuwa yanzu
babu wanda yasan inda Abdul yake agidan sai Kadija ita kuma tayi musu ƙaura daga gidan Alhaji Aminu kuwa yayi cigiyar yayi neman amma shuru,
Yau ta kasance ranar lahadi saura sati É—aya bikin Aaminat da Abubakar (Yarima)
Ammi tana zaune a falon ta ta zabga ta gumi, Yarima yayi sallma, zama yayi kusa da ita gami da cewa "Ammi lafiya kuwa???, naga kwana biyu bakya walwala" hawaye ne suka fara shatata tayi saurin kauda kai, "Ammi meke faruwa haka dan Allah ki daina kuka banason ganin kukan ki," cikin muryar kuka ta ce "mahaifinka ya juya min baya sam ya daina saurara ta ko magana nayi masa baya kulani rabon da yazo sashina har na manta kullum sainayi kuka mai isa ta" ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kama hannunta ya ce "Abi yace mini ba zai iya zama da wadda bata ƙaunar iyayansa ba, shine dalilinsa na juya miki baya" hawaye ta sharen gami da cewa "Allah natuba kayafeni wallhi duk zigar su Hajiya Bilki ce suka ce karna bi iyayan mijina wai E'iya ta fiye tsugudidi da munafurci ga masifa, sun cuceni gashi sun rabani da miji na" ta ƙarasa maganar tana kuka Abubakar yasa hannu ya share mata hawayen sannan ya ce "tunda Allah ya ganar dake gaskiya ina ganin kije ki nemi yafiyar su mahaifiyar tasa daganan saiki faɗa musu abinda yake faruwa tsakanin ku da Abi ɗin zasuyi masa faɗa kuma zai ɗauka, banda abinki dama Amma kema fa uwa ce idan na yi Aure matata ta tsaneki kamar yadda ki ka tsani su E'iya nasan ke ba ma za ki iya haƙura ba"
rausayar da kai tayi ta ce "Ai Ƙaddara ce yaro, ni bansan hakan kuskure bane, kana ganin su Hajiya E'iye zasu yafemin abinda nayi musu harfa kiransu nake da mayu, kaicona nayi asara" ta ƙarasa maganar tana kuka mai ƙarfi, cikin ƙwarin guiwa Abubakar ya ce "zasu yafe miki in sha Allah, ki shirya na kaiki gidan" "to" tace cike da tararradin zasu karɓeta ko kuwa,
bata ɓata lokaci ba ta shirya tsaf suka ɗauki hanyar gidan su E'iye
cikin mintina ƙalilan suka ƙarasa gidan Yarima yayi gaba Ammi na biye da bayan sa kai tsaye sashin E'iye suka nufa
E'iye da Inni suna zaune a Falo sukaji sallama, fuska babu yabo babu fallasa Inni ta amsa, Abubakar ya ce "yadai Budurwas naga kin wani haɗe fuska" zumɓura baki tayi ta ce "naga ka shigo mana da baƙuwar fuska ne" murmusawa yayi ya ce "Ammi ce tazo ta naimi yafiyar ku" Ammi kuwa kanta yana ƙasa sai sharar ƙwalla take, Abubakar ya ce "ni bari naje wajen su Huzaifa" Ammi ta zauna murya na rawa tace "dan Allah ku yafe mini na tafka babban kuskure da ban ɗaukeku da daraja ba, dan Allah ku gafarce ni badanni ba dan Allah na roƙeku" ajiyar zuciya E'iye ta sauke a ranta ta ce Alhamdulillah Allah kaine abin godiya, Inni kuwa tashi tayi zata bar wajen, Ammi tayi saurin durƙushewa agaban ta ce "dan Allah ba danni ba ku yafemin dan girman Allah" E'iye ta ce "nayafe miki Allah ya yafe mana baki ɗaya" Inni ta sake ajiyar zciya ta ce "nima na yafe miki kinji ai ɗa na kowa ne, ina fatan Allah i shiryi duk masu irin halinki" Ammi bata san lokacin da ta fara murmushin farin ciki ba, ta ce "Na gode Allah i saka da Alkairi....
Indo and Autar Jarumai
[8/1, 1:28 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin HaÉ—aka ne💪ðŸ¾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION
Shafi 24
E'iye ta ce "ya zaman gidan naku komai lafiya ko!???" da sauri Ammi ta girgiza kai ta ce "da sauki dai, Abi ya juyamin baya yanzu ko magana bata haɗani da shi sai kallo amma karku ga laifinsa nice da laifi dan kuwa mugun halina ne ya ja mini" E'iye ta ce "sabhanallahi mekikayi masa har haka!??" murya ƙasa-ƙasa ta ce "rashinyi muku biyayya ne kuma yanzu na gane kuskure na wallhi nayi nadamar abinda na aikata, duk nice silar rabuwar Abubakar da ƴar uwarsa, nidai banyi dacan hali ba" cike da manyance E'iye ta ce "kinga dama haka duniya take abinda ka shuka shi zaka girba, ko akan Abubakar zaki gane Allah ɗaya ne, tun yana goye yake ƙaunar mu har ya girma kinsha jifanmu da munanan kalamai, amma yanzu komai ya wuce, zankira Alhaji Saadiƙ ɗin" ta ƙarasa maganar tana ɗaukar wayar ta ta dannawa kira Abi bugu biyu ya ɗauka, cike da girmamawa yayi sallama, ko amsawa batayi ba ta ce "ka hanzarta zuwa ina nemanka" rasss gaban sa ya faɗi cikin rawar murya ya ce "lafiya kuwa" "inkazo kaji" ta faɗa tana sauke wayar,