← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 38

Sashe 18

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Yaya Aaminat kin karya kuwa?" Umaima ta faɗa tana zubawa Aaminat ido "Umaima meyasa yau kike tambaya ta na ci abinci??" murmusawa tayi sannan ta ce "da da yanzu ai ba ɗaya bane" murmushin ita ma tayi kafin ta ce "to na karya Umma ta zuba mini abin kari" "ai na zaci baki karya ba shiyasa" "Umaima kina son wata abaya tawa??" ina so mana kogi ai bai ƙi daɗi ba" "sawa ɗaya nayi mata naji ta fita daga raina" "nikam ina so wallhi dama akwai wani takalmi naki ko kibani ko mudinga sawa tare" tintsirewa tayi da dariya Umaima ta zaki baki tana kallon ta ta ce "yaya Aaminat dariyar mekike??" "kece kika bani dariya wai ko na baki ko musa tare" "A'a to bazaki bani ba" Aaminat ta ce "A'a zan baki mana ai baki taɓa tambaya ta abu na hanaki ba, kin manta lokacin da ina budurwa kafin nayi aure wata ranar se na zo sa abu se naga kinyi ɗagwass-gwass a ciki" dariya sukasa Umaima ta ce "rayuwa kenan dan ma sharrin shaiɗan ya ratsa da zigar Mama da Fati suka sa na juya miki baya amma ki yi hakuri ki yafe ni don Allah, yanzu na gane kuskurena" dandanan annurin fuskar Aaminat ya ɗauke ta ce "ba na son naji kina irin wannan magan-ganun ai baya tawu ce ni na yafewa kowa" rausayar da kai Umaima tayi ta ce "ai nadena daga yau" "kyaji dashi de" Aaminat ta faɗa fuska ɗauke da murmushi dariya Umaima tayi kafin ta ce "wai kina da labarin wani sikarin guys da yace yana sona??" "A'a bani da labari se kin shaƙamini" "Ummm ai nake faɗamiki shiɗin maƙura ne wallhi gashi kyakkyawa" "Allah ƙanwata kice kin kware masa?" dariya ta ɗanyi ta ce "ai dole sabida tsabagen kyanshi gashi ɗan wanka babu ruwan shi" Aaminat ta riƙe baki ta ce "lallai Autar ɗakinmu haka kika kama da wuta??? ya fini kyau kokuwa?" dariya suka sa cike da nishaɗi Umaima ta ce "ai kowa da matsayi shi kin fishi kyau" haka suka cigaba da hira suna dariya da nishaɗi.

Misalin ƙarfe 4:30 na yammaci Yarima ya shirya cikin dakakkiyar rantsats-tsiyar shadda fara ƙal har ɗaukar ido take baƙar hula dara yasa baƙin agogo baƙin takalmi yayi kyau sosai fitowa yayi Falo a ya na taku ɗaiɗai,
Ammi na zaune ta na kallon TV dama aikinta kenan ko Abi ne yadawo bata kulawa da shi abinci ma sede ƴan aiki su kai masa ko Yarima, ɗan ƙaramin tsaki yayi sannan ya ce "Ammi ni zan fita" "Allah ya tsare kuma saura kabiya gidan kakannin ka" ya ce "Ameen" yafice zuwa harabar gidan Kai tsaye wajen ajiye Motoci ya nufa, wata tsuleliyar mota baƙa ya hau me tsadar gaske yanufi Gadon Ƙaya gidan su Aaminat.
*Ku Dakata Mana✋🏽🤸🏾‍♀️Saurin Me Kuke🤔 sai ka ce Za'a ci da Rabonku🤔😍* Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.*

*HALY-JASHERU venture's*
*munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.*
*prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA*

be ɓata lokaci ba ya ƙarasa Unguwar wayarsa ya ɗauka ya danna wa Siyama kira bugu biyu ta ɗauka tare da sallama ya sanar mata ya ƙaraso "to" kawai ta ce ta tashi ta yafa mayafinta tayi waje sai gidan su Aaminat.

Ta zaune tana rera karatun alƙur'ani maigirma cikin nitsats-tsiyar muryar ta me daɗin saurare. zama Siyama tayi Aaminat ta taƙaita karatun dan ganin Siyama ta yi addu'a suka shafa Siyama ta ce "kin fa yi baƙo" "nayi baƙo kuma wanene?" ta faɗa cikin sigar mamaki Siyama ta rausayar da kai ta ce "ke de kizo muje" "kinga nifa babu inda zani sekin faɗa min kowaye" "Yarima ne" rassss!!! taji gabanta ya faɗi takasa cewa komai se kallon Siyama da take to meya zo yi wajenta ta tambayi kanta Siyama ta ce "yana kira fa kihanzar ta"! taɓe baki tayi kafin ta ce "wai na hanzar ta sabida ga ubana ya zo ko??" Siyama kuwa roƙon Aaminat ta shigayi tana magiya akan tafita, Siyama ta ce "tunda bazaki ba bari na faɗawa ya Omar shiya tilastaki koma dole kije" tana shakkar ya Omar sosai dan kuwa ba shi da wasa hakan yasa ta ce "zanje base kin faɗawa Ya Omar ba amma da sharaɗi bazan daɗe ba!" Siyama ta ce kokefa harkinfi kyau yanzu" Aaminat ta kai mata duka ta ce "dani mummuna ce??!" "A'a karki kaini inda Allah be kaini ba" ta shi tayi ta zura zumbulelen hijabi ta feshe jikinta da turare meƙamshin gaske, Siyama ta ce "sekizo muje ai ko" ƴar dariya tayi gami da cewa "sekace wata babata se wani magana kekemin sama sama" Siyama taja hannuta ƙiii zuwa ɗakin Umma, cikin jin kunya Aaminat ta ce "Umma zanje nayi baƙo" Umma ta ce sekun dawo kukula kunji ko Allah yayi muku albarka" Siyama da Aaminat suka amsa da Amin.

Ɓangaren Yarima kuwa yana jikin motar sa ya jingina ya harɗe hannayen sa a ƙirjin sa kanshi a ƙasa kamar tsohon munafuki sallmar da yaji ce ta dawo dashi hayyacin sa yayi saurin ɗagowa karaff suka haɗa ido da Aaminat wani kallon kallo suka shigayi babu kiftawa dariyar da Siyama tayi ce ta dawo dasu hanyyacin su, Aaminat tayi saurin kauda kai gefe, sannan ta ce "i...ina wuni" wani tattausan murmushi ya sakar mata gami da cewa "lafiya lau" wani sihirtaccen kallo yabita da shi yana wani limshe ido wani tartsa-tsi yakeji zuciyar sa nayi sede ya ɗaura ɗamarar bayyanawa Aaminat soyayar shi.
Siyama ta ce "To ni dai sai anjimanku." Yarima ya ce "Na gode Siyama ki gaida Aunty." ta ce "To"

Maida kallonsa ya yi ga Aaminat kafin ya yi
gyaran murya sannan ya ce "Aaminat kin bani dama na bayyana soyyata agareki??" rasss-rasss!!!!!! gaban Aaminat ya faɗi tunanin Abdulkareem ne ya keto mata, Yarima ya ɗan ƙara takawa yaje gaf da ita kana ya ce " kitaimaki wannan bawan Allahn da idanunsa su ka rufe akan sonki Aaminat." shiru ya ɗan yi kafin ya ci gaba da cewa "Ina sonki!!! ba na so ki ce min a'a don Allah ki yi tunani me kyau akaina." a hankali ta ɗago kanta ta zuba masa idanu Zuciyarta na wani irin tsalle, ba shakka idan ta ce Ba ta burgeta ta yi ƙarya, haka idan ta ce ba za ta iya son shi ba ta yi babbar ƙaryar da ƙarshe ta zo ta ji kunya, sai dai akwai wani hanzari ba gudu ba, Abdulkareem kawai take tunani don ba ta san yadda za su ƙare ba, bayan haka kuma ta gaji da sanya shi ƙunci duk ta dalilinta. tattausan murmushi Yarima ya sakar mata wanda ya ratsa dukkan sassan Zuciyarta, tayi saurin yin ƙasa da kanta yayin da itama murmushin yake neman kufce mata. murmushi me sauti yayi kafin ya ce "kin amince da Soyayyata???!!!" murya a harɗe ta ce "Zan yi shawara" ya ce "shikenan kiyi shawarar amma dan Allah karki sanarmi mummanan saƙo" bata ce komai ba ta juya zata tafi taji ya ce "kitsaya muyi sallama mana ko" cakk ta tsaya batare da ta juyo ba, ya juya mota ya ɗakko wata ƴar ƙaramar leda sannan ya nufota, miƙa mata ya yi gami da cewa " ga wannan waya ce da layi aciki inna koma gida zan kiraki" ƙin karɓa tayi ta ce "A'a kariƙe kayarka nima ina da ita" "nasan kina da ita shiyasa na baki wannan" ajiyar zuciya ta sauke aranta ta ce "wannan bawan Allahn yafiya ta kura" ya ce "Don Allah ki karɓa ba don ni ba, sannan duk shawarar da ki ka yanke ki kirani da ita kar ki barni ina tunane-tunane." karɓa ta yi gami da godiya sannan ta wuce cikin gida.
seda ya ga ta shige gida sannan ya juya ya nufi motar shi cike da farin ciki da kuma zullumi kar Aaminat ta ce bata son shi....

INDO tare da Ƴar Uwa Salma Auta
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)

Littafin Haɗaka ne💪🏾

Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

Tare da

Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S

Shafi 15
Chapter 18 · 0% Book details