← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 38

Sashe 29

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

bayan ɗan wani lokaci Abi ya ƙaraso gidan kai tsaye yayi ɓangaren E'iye, sallama yayi a Falon turusss yayi ganin Hajiya Hafsa tayi muzu-muzu gaida su Inni, yayi rai a ɓace ya kalli Ammi ya ce "meya kawoki gidanmu kokinzo ki haddasa mana fitina agida???? to kisani makircinki babu inda zaije"...
numfashi yaja ya cigaba da cewa "idan kin manta ni ban manta ba, lokacin da sukaje gidanki kikasa akayi musu korar kaji kikace ke baki sansu ba, dama zama kawai nakeyi dake amma yanzu zamanki yaƙare agi...." "ka dakata karka yanke hukunci cikin fushi" muryar Inni ta dakatar dashi
E'iye ta ce "bawai nakiraka bane dan ka dawoda bara bana ba, nakirakane domin inaso ka daina abinda kake ka ka koma ga iyalinka, indai akanmune ka fita shirgin matarka to kakoma, ta nemi yafiyarmu kuma munyafe mata, saura kai" ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "tinda kun yafe mata nima na yafe mata Allah ya yafe mana baki ɗaya, kuma darajarku da ta ɗanta ta ci" suka amsa da amin, shurune ya ɗan ratsa na wani lokaci kafin Abi ya ce "nizan koma sai anjima zan dawo" Inni ta ce "to Allah ya kaimu anjiman, nima zan fita nayo siye-siye kar naje Amarya tafini kyau" dariya sukayi Abi ya tashi E'iye ta ce "ai bamu gama magana ba" komawa yayi ya zauna, ta ce "inason da kaida Hafsa ku haɗa kan ƴaƴanku da yarabe" Inni ta ce "gaskiya dai yakamata wannan gabar da take tsakanin su tazo ƙarshe" "to in sha Allahu zamuyi hakan, Allah ya saka da alkairi," kallon Hajiya Hafsa yayi ya ce kikira Rahina kice ina nemanta yau ɗinnan," cikin jin daɗi Ammi ta ce "to" sallama yayi musu sannan ya fita,"

Yarima ne ya shigo Falon yana tafe yana haɗa hanya Inni ta ce "saurayin ya dai naga kamar bakajin daɗi" zama yayi gami da cewa "kin fiya ƙaga min cuta banace muku Dr baya rashin lafiya ba???" E'iye ta maka masa harara gami da cewa "shiyasa naga ai Dr kullum sai yayi kuka," dariya yayi ya ce "to su E'iye kinshin ya motsa" badole ya motsa ba zakayi mini kishiya kuma kace dagani ka gama Aure" Haba uwar gida nimafa ba ason raina zan miki kishiya ba" dariya suka sa, Ammi cikin raita ta ce "dama haka suke gudanar da rayuwarsu nake ƙoƙarin shiga tsakanin su???" Inni ta muskuta gami da cewa "ai tare zaka Aure mu nagaji da zaman budurci" dariya sukayi suka cigaba da hirarsu cin farinciki,

"Wai a haka za'a kaiki gidan mijin ko gyara babu" Siyama ta faɗa Aaminat ta ce "gyaranme zanyi" "Au bazakiyi ba kenan" Aaminat ta murmusa ta ce aini agyare nake koda yaushe" dariya Siyama tayi ta ce "kyajidashi dai" Umaima ta ce "Siyama gobe fa zamuje rabon katin gaiyata" "Allah ya kaimu kowa a layinnan sai mun bashi," "kedai bari har maƙiya sai mun gaiyata wallhi ɗazu ma naje fagge wajen mai ɗinki na karɓo" Aaminat ta ce wai ku baku da aiki saina zancan wani biki can" "iyeeee lallai to kokina so ko bakya so sai mun cashee" Siyama ta faɗa tana murguɗa baki Aaminat ta bita da kallo, "Siyama nifa da sosamu ne wallhi da gobe zan fara shagali" Siyama ta ce "to uwar zumuɗi" dariya sukayi, Aaminat ta ce "dan Allah ku bani katin nan na bawa su Bilal" Siyama ta ce "taɓ ai'dasu ake komai suma zasuyi tasu gaiyatar, sune ƴan shigo da Amarya fa" ɗigimi wai shigo da Amarya saikace wata mage" "kinga sai wani babbasarwa kike munfa san komai wallhi" "mekuka sani???, ƴar rainin hankali kawai" Umaima ta ce "ba saikinji ba" "to karku faɗa" dariya sukasa, Aaminat ta ce "wallhi ko kwana biyu tinanin Abdulkareem kawai nake" "Allah sarki rayuwa ɗazu naga ƙanwarsa Farida" Aaminat ta tayi murmushi mai tafe da hawaye, "kinga matsalata dake komai kuka saikace wata kaza" Aaminat ta ce "ina tunanin halinda Abdulkareem yake ciki ko yana ina???" Umaima ta rausayar da kai gami da cewa "haba yaya Aaminat ki daina damuwa na san yasan ankusa bikinku kuma inaga yana nan yana farinciki dan kuwa shi rayuwarda kike ce baya so kuma ai Amininsa ne zai Aureki kuma shiya nemi haka" ƙwalla ta share ta ce "Allah ya bamu haƙuri da dangana," suka amsa da Ameen,,

Abi Ammi Anti zaina Rahina Abubakar zaune suke a babban Falo.
Cikin nasiha Abi ya ce "ke Rahina na kira ki ne akan tsakaninki da ɗan uwanki daga yau sai yau karki kuskura na ƙara ganin kina nunawa ɗan uwanki ƙiyayya, idan baki riƙeshi da daraja ba wazai riƙe miki ɗan uwa kin kuwa san irin baƙin cikin da nakeji idan naga kina nunawa ɗan uwanki ƙiyayya????! babu dare babu rana addu'a nake Allah ya haɗa min kanku Amma ke ce babba kuma kece babbar banza ciki ɗaya amma ace baki da maƙiyi sai wanda kuke uwa ɗaya uba ɗaya anya kuwa kina da hankali????!" Yarima kuwa banda sharar hawaye babu abinda yake, kansa na ƙasa, Ammi ta ce "duniya abin tsoro wata rana in mune wata ranar bamu bane, yanzu itace damarki ki gyara kusakuren ki" "kin kuwa san waye yayi nasarar ceto rayuwarki lokacinda kikayi hatsari???, to ɗan uwanki ne wanda kika ɗauka maƙiyinki, shi ko da yaushe ƙaunarki yake, amma kallon da kike masa daban, sau da yawa ba tare da kin sani ba shi ke temaka miki, wai me ya yi miki ne haka?" da sauri ta ɗago suka haɗa ido da Abubakar yayi saurin yin ƙasa da kai yana goge ƙwalla,
itama maida kai ta yi ƙasa ta kasa cewa komai, jikinta ya yi mugun sanyi,
Ammi ta ce "Wallahi Rahina da ni da ke duk duniya ce take ruɗarmu, amma ko iya abinda ki ka yiwa Abubakar ba ki yi nasara akansa ba su kaɗai sun isa ishara, bai yi miki laifin komai ba, kuma duk nice na fara nuna miki hakan sabida shi yana nunawa kakanninsa ƙauna ki nemi yafiyarsa don Allah" ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka, Anti ta ce "rashin sanine, ki godewa Allah da ya ganar dake tin yanzu" cikin kuka Rahina ta ce "Abubakar ka yafemin dan Allah wallahi sharrin shaiɗan ne" cikin muryar kuka ya ce "yaya wallahi ni ban taɓa ƙullatarki ba kullum burina naga mun zauna inuwa ɗaya muna zumunci da juna" tashi tayi taje gaf dashi sannan ta durƙusa ta ce "ina neman yafiyar ka kayafe min duk abinda nayi maka" hannu yasa ya share mata hawayen sannan ya kalle ta ya ce "na yafe miki nima ki yafe min" cikin kuka ta ce "na yafe maka dukda bakayimin komai ba" Abi ya ce "Alhamdulillah Allah kaine abin godiya" Ammi kuwa murna take sosai sai sharar hawayen farin ciki take, Abi ya miƙe gami da cewa "lokacin sallah yayi"
tashi suma sukayi kowa ya nufi inda zai É—aura Alwala"

INDO TARE DA AUTA
[8/1, 1:28 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)

Littafin Haɗaka ne💪🏾

Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

Tare da

Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION

Shafi 25

Yarima yana dawowa daga masallaci ya nufi ɗakin sa, zama yayi gefen gado ya zabga tagumi, wayar sa ce ta fara ruri da sauri ya ɗauka ya kara akunne, "salamu'alaikum" "likita bokan turai bakaso a mutu bakaso a zauna lafiya" dariya yayi ya ce "mai gaiya mai aiki sai dakai uban gida" dariya sukasa Abdulkareem ya ce "ya shirye-shirye???" "shiri kuma saikace wasu mata" "Au sannu maza" Yarima ya ce "sai yaushe zaka dawo ne, nifa nagaji da zuwa duba mutan gidanku" "dawowa kuma ai sai abinda Allah yayi idan kana son ganina ka zo inda nake" "kana nufin bazaka halacci wajen ɗaurin Auren ba!??" "eh bazan zoba idan nazo ai nadawo gida kenan kuma nasan Dadda zai halacci wajen" "dan Allah ka daure kazo wallahi bazanji daɗi ba in bakazo ba" "kana ruwa nace fa bazan zoba" Yarima ya rausayar da kai ya ce "wallahi mutan gidanku duk sun rame yaufa kwana uku Dadda baya fita bashi da lafiya" dariya Abdul yayi gami da cewa "zuwana ba zaisa Dad yaji sauƙi ba, dan ba danni ya kwanta rashin lafiya ba" "dan kaine kuwa Dadda babu inda baya neman ka amma ya kasa gano inda kake" Abdul yayi murmushi mai ciwo ya ce "Allah ya bashi lafiya kawai, ni yanzu Allah ya taimakeni na dawo cikin nutsuwa ta, kullum ai'kina karatun Alƙur'ani mai girma" "to Allah ya taya mana" daga haka sukayi sallama,

Abdul ya ajiye wayar yana murmushi yanzu abu É—aya ne ya rage masa, yaga Æ´ar uwarsa Kadija,

"Fati wallahi ko banso Auren ki da waccan banzar yazo ɗaya ba" wani banzan murmushi Fati tayi ta kalli ƙawar ta Nafisa ta ce "kinsan kodame kurna tafi magarya ƴaƴa," "kuma kinsan wazata Aura??" Fati ta girgiza kai ta ce "koma waye nasan sai dai ya biyo bayan Ahmad, dan kuwa idan kuɗi ne Ahmad ya tara an tara masa," dariya suka yi gami da tafawa, "inaga ma bazawari ne ko mai mata" "to dama ai bazawara sai bazawari," "hahahaha" Nafisa tayi wata dariya kamar wata mahaukaciya, Fati ce ta tashi gami da cewa "zoki rakani gidan su ruma" "to" tace suka tashi suka nufi hanyar fita,
Chapter 29 · 0% Book details