← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 38

Sashe 16

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

danda nan Mama ta sauya fuska ta koma kalar tausayi ta ce "yanzu nikike faɗawa haka daga cewa kizo ki tayani wanki???" dafe ƙirji Aaminat tayi tare da zaro ido tabbas Mama azzaluma ce tafaɗa cikin ranta, wata tsawa Hamza ya daka mata gami da ce wa "mahaifiyar tamu kikewa rashin kunya dan ubanki kodan ba uwar ki bace" murya na rawa ta fara magana "wallhi ya Hamza banyi mata rashin kunya ba yanzu ma nafito daga ɗaki" Mama kuwa jin Hamza yana sauke ƙwandon bala'i ya sa ta fara matse hawayen makirci, Abba ne ya shigo da sallama da sauri Mama ta ce "yawwa Alhaji nagaji ka zaɓa koni ko ƴarka dan kuwa na gaji da futsarar da Amina take mini" ran Hamza kuwa in yayi dubu ya ɓaci jiyake kamar ya nakasa Aaminat yahuta Abba kuwa haƙuri ya shiga bawa Mama,
Umma kam kuka me ƙarfine ya kufce mata, ta rasa meyasa Mama ta tsaneta ita da ƴaƴanta kodan ita bata da ƴaƴa da yawa, itama ta gaji da cutarsu da ake agidan dan kuwa yanzu Abba ko ta ita bayayi,
jikake tassssss Abba ya wanke Aaminat da mari ya na ce wa "ke wace irin yarinya ce??!! mara tarbiya kin ƙi zaman aure sabida Uwarki da ta ɓataki kullum baki da aiki se tayar da masifa da bala'i to kinyi na farko kinyi na ƙarshe daga yau se yau na rabaki da duk wata alaƙa da zata haɗaki da iyalina kuje can ku ƙare keda Uwarki!!! Ni dai ban taɓa haifar Ɗa na yi nadama ba sai ke, a gidan Miji ma ba ki fasa iskanci ba Aaminat ina ki ke so ki kai Alhakin mutane? Da Mijinki fa ki ka dinga neman Mazan wasu kuma ya sake ki kin dawo ki na tayar min da hankali a Gidana Aaminat ki je don kanki, na yi bakin ƙoƙarina don naga na nema miki wani mijin kin yi Aure kin gyara rayuwarki amma duk kin Fatalar sabi da idonki a tsakar kai ya ke, Ba komai ki je don kanki" yana gama faɗin haka yajuya fuuuuuu ya fice daga gidan don kuwa in ya zauna ba abinda zai tsintsa sai ɓacin rai. durƙushewa tayi awajen tana wani kuka metsuma zuciya tayi da nasanin rayuwar ta a duniya wani juyi take ganin gidan yana yi.
Hamza kuwa har yanzu ranshi aɓace yake ganin yadda Mama take matsar hawaye "shikenan haka zamu zuba ido ta dinga yiwa Mama rashin kunya to wallahi haƙurinmu ya ƙare" Fati ta faɗa tana goge hawaye A hassale Aaminat ta ce "mukuma tamu uwar fa ta mutu sabida baƙin cikin da kuke ƙunsa mata???!!! ko a tunaninku bata jin zafin abinda kuke wa ƴarta kodan kunga tana kauda kai tana bawa uwarku girmanta?????!!!" "ke dan uwarki mu kike faɗawa haka??!" cike da ɓacin rai da baƙin ciki Aaminat ta ce na faɗa sede kakasheni nagaji da wulaƙancin ku yau sede ayi duk wadda za'ayi" wani zazzafan mari ya kifa mata ya ɗaga hannu zeƙara mata yaji an riƙeshi da sauri ya juya dan ganin waye idon shi yayi tozali da Omar, rai a tsananin ɓace ya ce "kayi kuskuren marinta da farko amma yanzu na iso wajen ba za ka ƙara ba, Zawarci fa ba hauka bane, Idan ita ƴar iska ce ƴan iskan nawa ku ke tare da su kuma ba kwa nuna musu ƙyama sai ita da take jininku sabi da Asararru ne ku? Kun lalata mata ƙaunar da ke tsakaninta da Mahaifiyarta har ma da mu ƴan uwanta, Ba Uwar kwabo sama da taku uwar kai ma ka sani." Hamza da yake wani huci kamar yunwataccen Zaki ya fizge hannunsa daga riƙon da Umar ya yi masa ya cafki kwalar Umar ɗin ya na cewa "Uwarka itace Uwar Kwabo domin ita ta ɗora yarinya a turbar Karuwanci, kuma ƙarya ka ke ka ce mu muka ɗora Uwarka akan tsanar ƴarta ai ta na da hankali ko mahaukaciya ce da za mu faɗa ta yarda?" Fati ta ce "Ƙila dai Mahaukaciyar ce." Wani lafiyayyen Mari Aaminat ta saukewa Fati a kumatunta, Fati ta ƙwalla ƙara gami da rintse ido sabi da azabar da ta risketa lokaci ɗaya; Aaminat da jikinta ya ke kakkarwa ta ce "Wallahi tallahi ki ka ƙara zagar min Uwa sai na lahanta rayuwarki, Kai kuma Hamza na dawo kanka, Ni Karuwa ce na faɗa na ƙara Idan akwai wanda nake bautawa sai ya hanani Karuwanci, Miji ɗaya ya yi min kaɗan don hakan na ke neman wasu ka gane?? Ƴan Iska Ƴaƴan Baƙar mace!" yuuuuuu Yaɓar!!!! Mama ta yi zaman Ƴan Bori a gurin ta na cewa ''Na shiga uku na Lalace wannan Ƴa ta zageni ta zage Mutuncina, ni ki ke kira Baƙar Mace duk baƙina ai ban kai baƙin Halin Hasiya ba, Allah zai min sakayya Azzaluma Hasiya kin haifi bala'i da Masifa Allah ya isa Tsakanina da ku." jin haka ya ƙara ta'azzara Fusatar Hamza ya yiwa Umar wata Muguwar Shaƙa wadda ta sa numfashinsa ya fara rikirkicewa.
Umma da Umaima su ka ƙara ɓarke baki su ka ci gaba da kuka, Aaminat kuwa idanunta sun ƙeƙashe hawayen ma babu, tsananin Fusatar da ta yi ya sa take jin kamar ta kama su ta yi musu mugun dukan ko Mutuwa ko Rayuwa, Fati Sai zubo Maganganu ta ke yi amma Aaminat ta yi mata banza don kuwa Hamza ta ke Hari.

©Autar Jarumai & INDO
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)

Littafin Haɗaka ne💪🏾

Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA ONLINE WRITER'S

Tare da

Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S

Shafi 13

Cikin kuka Umma ta ce "Aaminat! Umar! indai kun tabbata ni Mahaifiyarku ce to na ce ku bari domin ni, ku kuma Hamza ku yi haƙuri komai ya wuce ba na son tashin hankali." a hasale Hamza ya ce "Ba zan haƙura ba har sai mun kece raini ni da Wannan Yaron." Umar ya ce "Yaro ya na bayan uwarsa don ni ba yaronka bane, kuma in ka isa ka fito waje mu yi Wallahi sai na saɓa maka kamanni kawai zan ƙyaleka ne sabi da Umma ta sa baki." ya na gama faɗen haka ya hankaɗa Hamza da ƙarfi, ya yi baya taga-taga, daidai lokacin Abba ya dawo gidan, cikin ɓacin rai ya ce "Au ku na nan ɗin dai ba ku dena ba??, kowa ya ɓace min da gani ko ranku ya ɓaci, shashashan banza da ba ku san ciwon kanku ba, don fita sai ku zo tsakiyar gidana ku kama yi min tashin hankali iye?, to ba zan ɗauka ba, idan na ƙara jin labarin wani ya taso fitina sai na saɓa masa, marasa mutunci shashashai." nan fa ya ci gaba da faɗa ta inda yake shiga ba tanan ya ke fita ba. Umar da Hamza su ka yi sum-sum su ka fice su Aaminat ma su ka gudu ɗaki, Fati kuwa ɗakin Mama ta gudu su ka dasa Labarin Aaminat, Fati ta na bawa Maman labarin yadda ta so ayi ba ta so faɗan ya ƙare iya haka ba.
Aaminat kuwa banda kuka ba abin da take yi bayan ta shiga É—akin.

Haka aka ci gaba da rayuwa a gidan salin alin kowa ya dena shiga harkar kowa tsakanin Ƴaƴan Umma da na Mama, Musamman Umar da Hamza, Fati kuwa tsakaninta da Aaminat sai dai baƙar magana da habaice-habaice, Aaminat kuwa duk hakan ba ya damunta burinta ɗaya ne ta ga ta bar gidan don haka ta zage da Addu'a tuƙuru.
Umaima kuwa duk jikinta ya yi sanyi, daga ita har Umman, sai yanzu su ka gane shigo-shigo ba zurfi Mama take yi musu ta cusa ƙiyayyar Aaminat a Zukatansu har ta sa su ke tsangwamarta.
A ɓangaren Mama kuwa ƙiris take jira ta samu abin yi ko ta samu abin da za ta laƙƙabawa Aaminat sharri, kullum cikin masifa da kumbure-kumbure take ba dan komai ba sai don ganin Umma da Umaima har ma da Umar duk sun koma jikin Ƴar uwarsu sun dena nuna mata ƙyama kamar yadda su ke yi Da.

Yau ta kasance Ranar Laraba, an tashi da Sanyi gami da Hazo sosai kasancewar Yamma ce ya sa sanyi ya ƙara yawaita.
DR Yarima
Sanye yake cikin Riga da wando Ƙananu dukkansu Farare sai Baƙar Jacket da baƙin Takalmi ya rufe idanunsa da baƙin Glass, hannunsa sanye da agogo golden.
cikin nutsuwa ya ke takawa har ya isa wajen Motarsa ya buɗe ya shiga mazaunin Direba, ya na so ya tayar da ita domin tafiya amma ya kasa sabi da dogon tunanin da Zuciyarsa ta tafi yi. ba kowa yake tunani ba face Aaminat wadda komai nata yake matuƙar burge shi. "So ka ke ka ce ka kamu da Sonta?" ya tambayi kansa, da sauri ya zaro ido gabansa ya yanke ya faɗi, ko shakka ba ya yi kuma hakan ne, bai taɓa kawo cewa abin da ya ke ji zai iya zama so ba sai a yanzu wannan tunanin ya faɗo masa, girgiza kai ya yi gami da cewa "Ba zai yuwu ba, ba zan zama maci Amana ba, Kar ka yi gangancin haka." a sarari ya yi maganar duk da cewar shi kaɗai ne a gurin.

Cikin sanyin jiki ya shiga tuƙa Motar, ba ya son zuwa Gida Ammi ta tsare shi da tambayoyi don haka ya nufi gidan Kakanninsa a cewarsa sai ta yi tambayar da dalili.
*Ku Dakata Mana✋🏽🤸🏾‍♀️Saurin Me Kuke🤔 sai ka ce Za'a ci da Rabonku🤔😍* Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.*
Chapter 16 · 0% Book details