← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 38

Sashe 26

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tunda Uncle Rabi'u yazo suke ƙarda da Dadda akan yabar Abdul ya Auri wadda yake so, saidai Dadda ya kafe ya tsaya tsayin daka a kan ra'ayin sa, Uncle Rabi'u ya gyara zama gami da cewa "bai kamata ka hana yaro abinda yake so ba, tunda yace Aure yake so to ka rabu da shi mana yayi kuma ai ba haramun bane dan ya Auri bazawara", Dadda ya rausayar da kai, cikin girmama yayan nasa ya ce "bawai na hana shi Auren bazawara bane, No, Ina buƙatar ya ƙara hankali ya san inda ke masa ciwo, ga Abdulmajid ga Abdurrahim ga Abdussalam duk ba wanda ya taɓa zuwa min da zancen Aure sai ƙaraminsu wai Abdulkareem, maganar Gaskiya Yaya ina girmamaka ne shi yasa nake bi a hankali amma ba zan iya bari ɗana ya yi aure ya na da shekara ashirin da ɗaya ba, don bance ya kai da biyu ba ma, ka yi haƙuri in sha Allahu indai ya ƙara hankali to wannan ba ni da matsala ko wa zai aura indai ba mara tarbiya bace" cike da gamsuwa Uncle Rabi'u ya ce "Eh na fuskanceka sosai kuma in sha Allahu zan ƙara yiwa Yaron nasiha, zan nuna masa cewa haƙurin ma ya na da amfani, amma ku tayashi addu'a kawai Allah i zaɓa masa alkairi idan yanzun ne idan sai nan gaban ne." murmusawa Dadda yayi gami da cewa "In sha Allah za mu ƙoƙarta, na ji daɗi da ka fahimce ni." murmushi Alhaji Rabi'u yayi ya ce "to Allah yayi mana mai kyau, kuma dan Allah ku daina fushi da ɗana shifa yaro ne," ƴar dariya Dadda yayi gami da cewa "ai ɗan na ka yana da kafiya sam ya koma tamkar bashi ne wanda nake kira da Babban mutum ba!" Alhaji Rabi'u ya ce "toni zan koma sai akira min Abdulkareem ɗin" Dadda ya ce "to" sallama sukayi da Alhaji Rabi'u cikin fara'a da sakin fuska Dadda yanufi ƙofar da zata sada sa da labun gidan,

ba a ɓata lokaci ba Abdulkareem ya shigo Falon kai a ƙasa, zama yayi a ƙasan kafet, ya ce "Uncle gani" murmushi Uncle Rabi'u yayi sannan ya ce "Abdul kayi haƙuri kasa Allah a ranka kaji ka maida komai ba komai ba, mahaifinka yaƙi Amincewa da maganar Auren ka, nayi iya ƙoƙari na amma ban sami nasarar shawo kanshi ba amma ina ganin kayi biyayya wa iyayen ka," wasu hawaye ne masu zafin gaske suka fara tsere a kumatun Abdul, "kayi haƙuri ka daina kuka kowa da tashi ƙaddar idan Allah baiyi matar ka bace to babu makawa sai kun rabu,...." ya ɗan tsagaita kafin ya ce "ka sanar da yarinyar cewa mahaifinka bai amince ba idan tana da wani tace ya fito" zuwa yanzu Abdul ya fara fita haiyacin sa, kuka yake razgawa tamkar ƙaramin yaro Uncle Rabi'u kuwa sai faman rarrashin sa yake, "Abdul kaifa musulmi ne ka ɗauki ƙaddara a yadda ta zo ma, ka gode wa Allah da ya wadata ka, ta ko ina ka kana da damar da zaka taimaka mata, ita rayuwa dama haka take wani lokaci farin ciki,.. wani lokaci baƙin ciki, kuma a rayuwa Ɗana ko a da ma ba yanzu da zamani ya juya ba, Ba komai ake so kuma a samu ba ɗana, ka tuna waɗanda su shuɗe kafin mu, ko ba ka sauraren tarihi ne? gashi za ka ga su na son abu to kuma ba shi Allah yake basu ba, wasu lafiya suke nema sun rasata, wasu ƴan uwa suke so gashi ba su da su, wasu ƴaƴa suke buƙata kuma me kyautar bai basu ba, wasu kuɗi ne abin son su amma Allah bai yi da rabonsu ba, za ka ga wasu ido ne ma basu da shi, wasu ba su da damar jin magana duk da suna da kunnuwa, amma duk a haka muke raye kuma muke farin ciki da abinda Allah ya bamu, to ita rayuwa a haka take, ta yuwu ita ba matarka bace shi yasa hakan take faruwa" cikin kuka ya ce "Uncle nagode da nuna damuwar ka akaina Allah ya saka da alkairi kuma in sha Allah zanyi ƙoƙarin ganin nayi wa iyayena biyayya koda hakan zaiyi silar rayuwa ta" yana gama maganar ya ƙara fashewa da wani matsanancin kuka mai tsuma zuciya, cike da tausaya wa Uncle ya ce "Abdul kasa a ranka haka Allah ya rubuta Aaminat ba matar ka bace kaji kataya ta da addu'a Allah ya bata miji nagari wanda zai riƙeta da gaskiya da Amana!" daker ya iya ɗaga harshen sa ya ce "na..na..na..nagode!!!!" jiki a matuƙar sanyaye Uncle Rabi'u ya tashi sannan ya dafa kan Abdul ya ce "Allah ya baku ikon haƙuri da juriya da kai da ita Allah ya haɗa kowa da rabon sa na alkairi, katashi ka koma sashin ka ka daina kuka domin kuwa kukan ka yana karyar min da zuciya"
bai ce ko mai ba sai aikin kuka da yake babu ƙaƙƙautawa jiki a mace Uncle ya nufi ƙofa,
*Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta*
*Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.*

*HALY-JASHERU venture's*
*munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.*
*prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA*

Abdul kuwa yana wajen ya kasa koda motsa ɗan yatsan sa ɗaya ne da nufin tashi" baya jin zai iya rayuwa gani yake tamkar numfashin sa a duniya ya zo ƙarshe,
ya daɗe a haka kafin ya tashi jiri ne ya fara ibarsa, yayi saurin dafa kujera yana wani numfashi sama-sama cikin hanzari da tashin hankali Ummi ta nufo wajen da gudu tana ƙarasowa ya ɗaga mata hannun sa dake rawa, Alamar da katar wa, tsayawa tayi cakkk kamar wadda a ka riƙe, Nana Kadija ce ta nufo wajen tana kuka, hannu ta miƙa mai ya kama, ta jashi suka bar wajen da ido Ummi ta bisu cikin tashin hankali, ta rasa abinyi hakan yasa ta juya gudu-dugu sauri-sauri tanufi inda Dadda yaka

Aaminat kuwa wannan furicin ne yake mata yawo aka yazama dole karabu da ita, ta kasa zaune ta kasa tsaye sai zarya take haka kawai zuciyar ta, ke raya mata Abdul yana cikin tashin hankali hakan yasa hankalin ta ya ƙara tashi ko tsakar gida ta kasa fita tana ɗaki kuka kam tayi ta gaji kanta har ya fara ciwo "maiyasa duk wanda ya shiga rayuwa ta saiya haɗu da ƙalubale dama gidan su Abdul basa ƙauna ta" wannan tambayar take yiwa kanta saidai bata da amsoshin su hakan yasa ta koma ta kwanta tayi lamo tana jiran Siyama ko Umaima su leƙota,

Yarima yana zaune a office wayar sa ta fara ringin da sauri ya É—auka don gani mai kira sunan Abdulkareem ne ta fito a kan wayar jiki a sanyaye ya kara a kunnan sa tare da sallama "salamu'alaika" "kana ina??!! muyar Kadija ta daki dodon kunnan sa, ya ce "lafiya??? ina Abdul É—in??!" murya a cunkushe ta ce "tambayar ka nayi kana ina??!!" "ina Asibiti" "to ka hanzarta zuwa gidan mu" tana gama faÉ—in haka ta katse kiran, sororo Yarima yayi ya kasa gaba ya kasa baya "mai yake faruwa" ya furta a fili zimbur ya tashi cikin hanzari ya fice daga office É—in ya nufi ma'ajiyar motar sa yana zuwa bai jira komaiba ya faÉ—a motar ya jata a guje, ya bar Asibitin,

Ummi ta sanar da Ddda abinda ke faruwa murmusawa yayi gami da cewa "ki ƙele sa zaiyi zai gama" sakin baki tayi tana kallon Dadda, shi kuwa ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya yana karatun jaridar sa, juyawa tayi zata tafi yayi saurin cewa "zoki zauna" babu musu ta koma ta zauna, hankalin ta yana kan Abdul saidai babu yadda zatayi ya zama dole su hane sa da abinda yake shirinyi,

Yarima yana zuwa yayi
parking kai tsaye ya nufi ƙofar da zata sada sa da sashin Abdul, yana tafe yana tunane-tunane ya saƙa wancan ya warware wannan har ya ƙarasa ɗan ta ƙaitacan Falon, rasss rasss gaban sa yayi wata mummunar faɗuwa ganin Abdul a dur ƙushe a wajen, cikin hanzari ya ƙarasa wajen ya ɗaga Abdul yana cewa "Abdul mai yake faruwa" cikin sarƙaƙƙiyar muyar sa ya ce "Abubakar taimoko zakayi mini a karo nabiyu" "taimako??" ya maimai ta cikin sigar tambaya, baki na rawa Abdul ya ce "ka taimaka mini ka Auri Aaminat" zindummmmm!!!!!!! gaban Abubakar ya yanke ya faɗi tare da zazzaro ido ya kalli Abdul,
Abdulkareem ya É—aga masa kai a lamar eh

©️INDO &&& Salma Autar Jarumai
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)

Littafin Haɗaka ne💪🏾

Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S Association

Tare da

Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S Association

Shafi 22
Chapter 26 · 0% Book details