← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 38

Sashe 30

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ummi dan Allah ku dauwo mana da ɗan uwanmu yau kusan kwana ashirin da wani abu, ba muga Abdul ba" "kuyi haƙuri muna bamu san inda yake ba gashi yanzu hankalina kullum ƙara tashi yake nayi da nasani, yanzu bansan awana hali ɗana yake ba" Nana Farida ta share ƙwalla gami da cewa "laifinku ne keda Dad baku tsaya kun fahimtar da shiba nasan da kunjashi ajiki kun nuna masa bakuso ta sigar salama da duk haka bata faru ba" Ummi ta muskuta tare da rausaiyar da kai, Nana Hauwa, ta miƙe gami da cewa "Allah sarki rayuwa gashi ai kuna da nasani" Abdurrahim ne ya shigo Falon hakan yasa Hauwa komawa ta zauna" "sannu da hutawa Ummi" ya faɗa yana zama, Ummi ta ce "yawwa" "haryanzu dai babu labarin Abdul nifa nafi tunanin yabar india dan kuwa nayi neman na rasa shi" "shikenan su Dadda sun rabamu da ɗan uwan mu" Farida ta faɗa tana fashewa da kuka, Ummi kuwa ta kasa koda magana, Nana Hauwa ta ce "Allah ya baiyana shi aduk inda yake" suka amsa da "amin"

Kadija zaune take a É—an matsakaicin É—akin su na gidan Uncle Rabi'u,
waya ta ɗauka tare da danna kira bugu ɗaya ya ɗauka cikin jin daɗi da farinciki ya ce "Dijan gala yakike" dariya tayi gami da cewa "lafiya ƙalau wallahi" "za kizo ɗin" "eh ya Abdul in sha Allah da yammacin yau zan sauka a Abuja" "Allah ya kawoki lafiya amma idan kikazo kije gidan Anti Maryam zanzo nan ɗin" "kana ganin babu matsala idan Anti Maryam kazo, kuma zata iya faɗawa su Dadda" murmushi yayi kana ya ce "a tasani kuma bazata faɗa ba ɗazu ma naje gidan" "yaushe zaka koma" "Jibi kinsan dan naga ya kike nazo kuma da mun gaisa zan ɗaware" "to sai nazo ɗin yanzu ma na faɗawa Mami nace zani wajen Anti Maryam kuma kwana zanyi nace amma karta faɗawa su Ummi" "Allah ya kawoki lafiya" daga haka sukayi sallama cikin farinciki da annashuwa,

"Abubakari kwandon sikari" Anti Zainab ta faɗa tana dariya "kai Anti dan Allah kidaina tsokana ta," zama ta yi akan ɗayar jujerarda ke kallon sa, ta na dariya ta ce "idan uwa bata tsokani ɗanta ba waye zai tsokane shi" dariya yayi gami da cewa "yaya ta tafi ne" Anti ta ce"A'a" Rahina ce ta shigo falon ta zauna Yarima ya ce "yanzu nake tambaya kin tafi" "A'a yanzu nakira Abban Kausar nace masa sai bayan Biki zamu dawo kuma ya amince" murmusawa yayi kana ya ce "Allah ya kaimu amma kun ɗiba da yawa kobaya ƙasar" "eh bayanan amma zai dawo ɗaurin Aure" murmushi yayi ya ce dakince ya barshi basai ya dawo ba" kallon sa tayi cikin jindaɗin yau gata ga ɗan uwanta suna magana, ta ce "ai dole ma yazo bikin fa ƙanina ake" sukayi dariya kana suka ci gaba da hira jefi-jefi don kuwa ba wani sabawa su ka yi ba"

kiran sallar magrib Kadija ta sauka a tafkeken gidan babban yayansu Abdurrahman kai tsaye ta kutsa kai falo, tare da sallama, da gudu ƙaramar ƴarsu Islam ta taso ta rungume ta tana cewa "Oyoyo-Oyoyo" jin haka yasa Anti Maryam fitowa daga kicin ɗin dake falon, cikin murna da dariyar farinciki ta ce "sannu da zuwa ya hanya" "Alhamdulillah" Kadija ta faɗa tana zama kan ɗaya daka cikin kujerun Falon, waya ta ɗakko ta dannawa Abdul kira, yana ganin kiran ya ɗauka, cikin farinciki ya ce "ina harabar gidan yanzu zan shigo," "ok" maida kallon ta kan Anti Maryam tayi ta ce "ina wuni" dariya Anti Maryam tayi sosai ta ce "saida kika gama wayar" "Au wallahi na sha'afa burina naga ya ɗan uwa yake" sallama yayi yana cewa "yau gani ga tsigai dariya sukayi,
ya kalli Khadija ya ce " Khadi ya hanya" "lafiya lau sai godiyar Allah"
"nayi kewarku wallahi kewarku" kaidai bari harfa rashin lafiya nayi" "Allah kice ruwa ya daki babban zakara" "sosaima dan kuwa naji jiki" dariya suka sa Anti Meri kam sai faman kaiwa da komowa take ta cika gabansu da kayan alatu iri-iri, Abdul ya kurɓi shayi sannan ya kalli Anti ya ce "Anti kushirya fa kunkusa Aurar da Dije" "Ah haba dagaske waye sirikin namu" dariya yayi Kadija ta maka masa harara, ya
ce "ai gaskiya ce tun ina gida nagane kuna soyewa da Omar" "kace sunan sa Omar" "eh mana kuma na bashi" tsaki Kadija taja ta ce "kowa yafaɗa maka ma oh'ho" "nina sani da kaina sau da yawa ina lura da lokacin da kike dawowa daga makaranta" "to kaji daɗi ai ka faɗa" "sosaima gashi har ƙiba nayi" dariya suka sa cike da farinciki,,

har wajen shaÉ—aya suna aikin abu É—aya, daga baya kowa ya nufi makwancin sa Abdul ma a gidan ya kwana kasancewar gidan babba ne.

washe gari tunda safe Kadija ta kama hanyarta ta komawa gida, Abdul ma ya shrya yayi wa Anti Maryam sallama, da niya shima gobe zai tafi Qatar,

Yau biki ya rage saura kwana uku ko wane ɓan gare shrye-shiye babu kama hannun yaro

inda Anti wato maman su Siyama da Æ´ar Autar su Umma suka zage dantse wajen shirya Aaminat,

Mama da ƙawar ta sun zage wajen ganin Bikin Fati yafi na Aaminat (Bazawara) inda suke shige da fice na ara aren bashika dan kuwa kashe kuɗi suke sosai,

Ɓagaren su Anti Rahina ma shiri ake sosai wajen ganin sun tsara biki,

Ya Omar ne zaune a ɗakin Umma ya zabga tagumi hannu bibiyu, sallamar Aaminat yaji hakan yasa ya ɗan saki fuska, ya amsa ƙarasowa tayi kusa dashi ta zauna, cikin nutsuwa da girmamawa ta ce "ya Omar anya kuwa ƙalau kake naga ka zabga tagumi ko bakajin daɗi" murmusawa yayi gami da cewa "karki damu ƙalau nake kawai banason hayaniya ne" "haka ne bakason hayaniya amma naga kamar yau kana cikin damuwa" "eh hakane ina cikin damuwa amma ki bar zancen kawai" "sabida me zakace nabar zancen" rintsa ido yayi kana ya ce "Aaminat banajin daɗin yadda Abba yake yiwa Umma" "nima abin yana damu na wallhi" Ya Omar ya ɗan ja numfashi tare da sauke ajiyar zuciya ya ce "karkiso kiji irin cin zarafin da Abba yayi wa Umma yau har zagin ta yayi kuma duk ta sanadin Mama ne" ya ƙarasa maganar kamar zai fashe da kuka, cikin rawar murya Aaminat ta ce "Allah Sarki, ai Allah yana kallo kuma zai saka mana" ta share hawaye sannan ta cigaba da cewa "ita rayuwa haka take kowa da tasa irin ƙaddarar," "Aaminat ina zamu saka kanmu Mama ta sako mu gaba, yanzu naji tana cewa Abba wai nima bin mata nake, haka kema tayi miki sharri tasa muka tsaneki" cikin kuka Aaminat ta ce "taje dan kanta Allah zai saka mana, kuma in Allah ya yarda kamar yadda tasamu a ƙunci itama saita shiga ƙunci da azaba ta duniya"
Ya Omar ya ce "yanzu haka Abba yace bazai ƙara yi miki kayan ɗaki ba" Aaminat tayi murmushin takaici ta ce "wannan kuma dama bana buƙata suje suriƙe kayansu, ai muma Allah ya azirtamu dan kuwa Umma tana da masu yi mata ko babu komai nasan Baba Usman zaiyi mini" shurune ya ɗan ratsa kowa ya faɗa daniyar tunani, Umma ta shigo ɗakin da sallama, murya a dashe dagaji tasha kuka, Aaminat ce ta amsa, Umma ta zauna kan gadon ta sannan ta kalli su Omar ta ce "kutashi yaya Usman yazo zamu bishi" "zamu bishi kuma??" Omar ya maimaita cikin sigar tambaya Umma ta ɗaga masa kai alamar eh "maiyafaru Umma" Aaminat ta faɗa, Umma tayi gyaran murya ta fara magana da cewa "ƴan uwana sun yanke shawarar baza'ayi taron biki anan ba sabida gudun rigima, kunga dangin Mama zasuzo Bikin Fati kuma sai sun tada fitina, ƙarshe kuma tazo ta ƙare akanmu shiyasa su yaya, suka ce muje gidan yaya Usman ayi taron kuma duk wani abu da ake buƙata ya ɗauke mana ya ce shizaiyi komai shima ai ƴarsa ce"

cikin farinciki da jindaÉ—i Omar ya ce Alhamdulillah wallahi naji daÉ—i Allah ya saka masu da akairi Aaminat kuwa taji daÉ—in hakan amma bata nunaba saima sunkuyar da kai datayi

Indo &&&& Salma
[8/1, 1:28 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)

Littafin Haɗaka ne💪🏾

Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

Tare da

Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION

Shafi 26

Umma ta murmusa ta ce "Aaminat ko kinfiso ayi Bikin anan" "Aa Umma canÉ—in sai yafi kwanciyar hankali" Umma ta tashi tana cewa "Aamiant kije ki kira Siyama da ita zamu tafi" "to" tace Umma ta fita, Aaminat ma tashi tayi ta zira hijabi ta nufi waje,

Basu ɓata lokaci ba suka kwashi duk wani abunda zasuyi amfani da shi suka kama hanyar Gidan Baba Usman.

É—aurin aure saura kwana É—aya kenan
kowawane ɓangare ya kacame, sai ai'kace-ai'kace ake ko wane gida ya cika da dangi ko ta ina gidan su Yarima ma yayi taff da mutane sai hada hada ake,

haka gidan Baba Usman ma dangi sun taru ba ƙarya manya da yara kowa ya nata shagalinda.

Gidan su Fati ma biki yayi biki, inda su Fati suke ta
sherye-shiryen fita Dinner
Nafisa ƙawar Fati ce ta shigo ɗakin su Fati ko sallama babu sai uwar shewa da ta saki, tana cewa "Amarsu ta ango yau saura kwana ɗaya mu kaiki" Fati ta tashi tsaye gami da cewa "dama ke nake jira kizo ki tayani zaɓar kaya dan wallhi so nake nayi shiga ta kece raini" "haba ai karki ɗaga hankalinki zaki fita da fitarki dan akwai ban-banci tsakanin Bazawara da Budurwa" Walid dake zaune aɗakin ya dubi Fati ya ce "wai Fati maiyasa ba ki da tunani ne,??? ita Aaminat ba sa'ar gasarki bace don kuwa zaran bakalar yadin bane" "dakata munafiki ina ruwanka damu ko kafiso mu zauna muna gani Bikin Bazawara yafi nawa??, to wallahi karka sake wannan tunanin nafi ƙarfin Aaminat ko ta ina" tashi yayi ya ficewarsa, ya barsu suna zage-zage da masifa.
Chapter 30 · 0% Book details