Sashe 23
Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abdulmajeed ya ce "ƙwarai kuwa, yanzu na ji suna zanzen shi da DR Abubakar ba su san ina gurin ba, ga shi nan sai ya yi muku bayanin wadda zai aura kuma ku shirya don kuwa uban ƴar ya ce wata ɗaya ya bashi, fitinannen yaro kai! ko ina shi ina aure?" Dadda ya ce "Sake shi to" sakin nasa ya yi Abdulkareem ya gyara rigarsa Zuciyarsa na tsalle, ba tare da tangarɗa ba ya ce "Aaminat nake so ta layin nan Ƴar gidan Alhaji Shu'aibu." Ummi da su Farida su ka sanya salati da sallallami, Abdussalam da Abdurrahim kuwa sai sakin baki su ka yi suna kallonsa.
Dadda ya ce "Na san Baban nata amma ban santa ba." cikin ɓacin rai Ummi ta ce "Wata Yarinya ce ba budurwa ba ma bazawara, yanzu sabi da Allah Abdulkareem aikin da za ka janyo mana kenan? ka na nufin ka watsar da duk tarbiyar da muka baka ne ko me?" cike da takaici ya ce "Ki yi haƙuri Ummi amma sam wannan ba rashin tarbiya bane, Ita ma fa macece kuma wadda take lokacinta, don ita bazawara ce ba ya na nufin shikenan ba ta da galihu ba, Daddy don Allah kar ka hanani abin da nake so wallahi ni ita nake so kuma ina son aurenta a cikin wata ɗayan da babanta ya ce." Dadda ya ninke Jaridar hannunsa ya zare Tabarau ɗinsa ya zubawa Abdul ido har na ɗan lokaci sannan ya jinjina kai gami da cewa "Danƙari, Babban Mutum ni ba zan zauna ina jayayya ko sa'insa da kai ba, kawai ban amince ka yi aure yanzu ba ko Bazawara ko Yarinya Ƴar goye ma duk ban amince ba, kai da Aure sai nan da shekaru Goma lokacin ka gama kafa kanka kasan inda ke maka ciwo, idan kuma za ta jiraka hazawasalam ni dai na gama maganata."
Cikin fitar haiyaci Abdul ya yi saurin durƙusawa kan guiwarsa hankalinsa a matuƙar tashe ya fara magana ba tare da tunanin cewa Mahaifinsa ne a gabansa ba "Dadda ni fa Namiji ne kuma namiji ba ya kaɗan, me zan buƙata a rayuwa bayan wanda Allah ya bani?, ya bani hankali da nutsuwa kai da kanka babban Mutum kake kirana, sannan ina kasuwanci ina da shaguna a kasuwa bayan Asibitin da Ka Mallaka min, ina da ilimi kuma ko da na aureta ban girmin ƙarin ilimi ba, Dadda ka temaka ka canja min wani Punishment wannan ya yi min tsauri hankalina ba zai iya ɗauka ba." sai a lokacin Abdurrahim ya ce "Abdulkareem anya kuwa ba ka fara shan wani abu ba? Daddan ya na faɗa ka na maida martani sabi da ka rasa hankalinka?" ya girgiza kai kafin ya ce "Ka kirani Mahaukacin dai amma Please kar ka kuma ce min ina shaye-shaye, Dadda komai ka ce in yi zan yi amma don Allah karka hanani Aurenta, itama Aaminat abar a tausaya mata ce ku temaka ku bani dama na inganta rayuwarta." Dadda ya miƙe rai ɓace ya ce "Tabbas hankalinka ya gushe ɗin ne shi yasa kake tunanin ma zan canja maganata, ka fi kowa sanin ni kaifi ɗaya ne mutum me tsatstsauram ra'ayi da kuma magana ɗaya, abin da zai yuwu shi nake amincewa da shi ba wanda ba zai yuwu ba, kar ka ƙara tinkara ta da wannan maganar idan kuma ka yi hakan fushina ya tabbata gareka; don muna nuna maka so ba shi yake nufin za mu barka ka dinga katoɓara iya son ranka ba." ya na kaiwa nan ya gangara sashinsa cike da fushi da takaicin haukan Abdulkareem, don a cewarsa hauka ne kawai.
Ummi kuwa da abin duniya ya isheta sai ta fashe da kuka itama ta tashi ta yi nata ɓangaren.
Su Abdurrahim su ka tasa Abdul gaba su na yi masa faɗa da nasihohi, sai dai a nashi ɓangarem in ta shiga ta kunnen hagu ne sai ta fito ta dama.
©INDO tare da SALMA AUTA
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin HaÉ—aka ne💪ðŸ¾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION
Shafi 19
Sai da suka gaji da yi sannan kowanne ya saɓe ya bar Abdul a gurin.
Bedroom ɗinsa ya nufa zuciyarsa cike da baƙin ciki da takaici, gabaki ɗaya haushin kowa yake ji musamman su Abdulmajeed masu bakin yiwa mutum faɗa.
Haka ya kwana cikin takaici ko baccin kirki ya kasa yi sai juye-juye yake yi.
a ɓangaren Abubakar (Yarima) ma haka ya kwana ba kwanciyar hankali, baccin sai ɓarawo.
Aaminat
ita ma haka ta kwana sai kici-kici take ta kasa baccin daga ta kwanta sai ta tashi, sai ma ta ga daren ya yi mata tsayi da yawa sabi da ta ƙagara garin ya waye.
Washe gari kuwa tin safe Abba ya na fita itama ta fita zuwa gidan su Siyama.
Bayan ta gaida Aunty ta wuce É—akin Siyama
Ta na zaune bakin katifarta ta zuba tagumi da hannayenta duka biyu.
Aaminat ta ƙarasa ta zauna jiki a sanyaye ta ce "Siyama kin ji abin da ya faru dani? ashe wai Abdulkareem ne ya turo min Yarima."
Siyama ta ja numfashi kafin ta ce "Hakan ba baƙo bane a gurina domin kuwa nima da sa hannuna a ciki, Abdul ne ya roƙe ni na yi masa wannan Alfarmar, a lokacin da na ce dole sai na kai ki Asibitin nan ai shi ne ya sa ni, ina ganin fa kar ki tsaya tunanin wani abu daban Aaminat, Abdulkareem ya na sonki tsakaninsa ga Allah ba don wani abu ba."
jikinta ya ƙara yin sanyi salam ta yi shiru ta ja tunani, sun daɗe a zaune curko-curko ba me cewa ƙala sannan Aaminat ta ce "Gaskiya in haka ne ban kyauta masa ba, duk abin da yake yi don ya fitar da ni daga cikin damuwa ne, yadda nake ɗauka duk ba haka yake a zahiri ba."
Siyama ta sauke nannauyar ajiyar Zuciya sannan ta ce "Na godewa Allah da ya baki ikon fahimta, yanzu abin da za ki yi kawai ki ba shi haƙuri kuma ki amince da soyayyarsa idan ba ki yi haka ba kuwa ni ba ruwana, ba gori ba ko me zai faru dake nan gaba ba zan ƙara damun kaina ba."
Aaminat ta ce "To ni ta ya zan ba shi haƙuri??"
Siyama ta ce "Ba ni wayarki in sa miki lambarsa ki kira shi, yanzu ba tare da ɓata lokaci ba."
Ba musu ta miƙa mata wayar ta karɓa ta jera mata lambobin
sannan ta bata wayar ta.
Karɓa ta yi ta tashi jiki ba ƙwari ta koma gida, tin da ta zauna take tunanin kiran nashi sai dai in ta kira ba ta san ta ina za ta fara ba.
Abdulkareem
Sai 10:00am ya fito lokacin duk yayyensa su Abdussalam sun bar gida su Khadija ma su na makaranta sai Ummi ita kaÉ—ai a Falo ta na zaune kamar korarriya, ita ba magana ba ita ba aiki ba ta na dai zaune kurum sai aikin tunani take.
Kusa da ita ya zauna ya gaisheta ta amsa masa ƙasa-ƙasa, ganin ta na ci masa magani ya sa shi tambayarta abin da ya faru.
Cikin takaici ta ce "Abin da za ka ce kenan? har ka manta tayar mana da hankalin da ka yi jiya?"
Ya rausayar da kai kafin ya ce "Meye abin tashin hankali Ummi? daga na yi zancen Aure ba fa ƙaramin yaro ba ne ni, i'm twenty something years old fa kuma ina da komai da zan iya riƙe mace."
Wata harara Ummi ta zabga masa wadda ta sa shi raina kansa, cikin matuƙar takaici ta ce "Abdulkareem shiga taitayinka, mu ba sa'o'in wasanka bane, mu za ka zo wa da rashin hankali cikin gida? da ƙuruciyarka ka ɓata ta ta hanyar Auren Bazawara?, to bari ka ji ni ko 15 years indai budurwa za ka aura daidai kai ba zan damu ba, amma ina raye ba ka isa ka auri budurwar da ta girmeka ba ma bare wata Bazawara da Allah ne kaɗai ya san tsiyar da ta tufka wancan mijin nata ya rabu da ita, ni dai ba a zuriya ta ba in za ka yayewa kanka ka yaye tin kafin dare ya yi maka."
Ya buɗe baki zaiyi magana ta dakatar da shi da cewa "Na gama maganata, ba na son jin komai, na riga na faɗa ban amince ba kuma idan ka yi ko bayan raina ban yafe ba, tinda na lura kai zuma ne sai da wuta, kar ka ji irin baƙin cikin da na kwana da shi jiya na furtawa da ka yi cewar za ka auri bazawara, wannan ai zubda kima da mutuci ne, to ni ba na son jin komai a bakinka indai ba cewa za ka yi ka janye ba, kuma ni me iya fita shirginka ce indai ka ce za ka bujire mana."
Sakkototo ya saki baki ya na kallon Ummin ta shi, a ransa ya na tsaka da mamakinta bai taɓa zaton za ta iya yin abin da ta aikata ba, kenan itama ta na ɗaya daga cikin waɗanda suke ƙyamar Bazawara? to wai me yasa hakan?
Tambayoyi ne suke masa yawo a tunaninsa sai dai ba shi da amsarsu ba shi da mai bashi don haka ya tashi ya zabari mota ya bar gidan.
*Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta*
*Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.*