Sashe 2
Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Matashin ya saki baki da Ido ya na Kallon Abdul, shi kuwa ya karkaɗe kwalar rigarsa da aka riƙe ya yi gefe ya na muzurai. "Me kake nufi ne?? ka yi min laifin kuma sai ka sa a Ɗaure ni?" Abdulkareem ya ce "Ɗan Halak ka fasa, ai kasan yadda doka take, ka riga ka ɗau doka a hanunka ka ga ba ka da dalilin ƙorafi akaina tinda ka rama, Ka ja saɓa ko mu saɓeka da kanmu." Cike da taurin kai Matashin ya ƙara cewa "Wai kai da me kake taƙama ne haka?, gani ka ke kamar ƙarfinka ɗaya da ni ko??" "Ka zo a gwada Gwani mana, na gaya maka dalilin da ya sa na bari ka dokeni amma banda haka da ba za ka bar layin nan lafiya ba daga kai har Motar taka." ya na gama faɗe ya bar wajen ya nufi inda ya wurga Takalminsa, Matashin kuwa ganin an fi ƙarfinsa ya sa shi jan Motarsa su ka bar wajen. Sai a lokacin Aaminat ta samu ƙwarin guiwar matsowa kusa da shi, cike da ɓacin rai ta ce "Ka na Shaye-shaye ne Abdool?? ko kuma dama Mahaukaci ne kai ba mu sani ba??" Rikitattun idanunsa ya zuba mata kafin ya ƙyalƙyale da dariya sannan ya ce "YaYa Aameenath!! Ba za ki Fahimce ni ba yanzu, don Allan ki shige gida ki dena tsayawa kan hanya kar a sabauta Mana Rayuwarki." idan Abdulkareem ya yi mata wani abin komai na jikinta dena aiki ya ke sai iya Zuciyarta, yau ma kamar kullum sai ta zama kamar bishiya ta saki baki ta na kallonsa, aranta kuwa irin Manyancensa ta ke tunani. Siyama takama hannunta gami da cewa "Tawo mu tafi ki bar wannan Tantirin Yaron, idan ma Nasiha ki ka yi masa ba zai fasa halinsa ba, ace rigimar da ba da kai ake ba dole sai ka shiga?" muryarsa ce ta dakatar da ita "Ke!! me kike da suna ne?? Siyama ko? to Anti Siyama dai Sabi da darajar masu daraja, ki fita idona in rufe tsakanina da ke daban tsakanina da Yarana daban tsakanina da sauran Ƴan Adam daban hallau tsakanina da YaYa Aaminat ya fi kowane tsakani da na ambata muhimmanci, Tsarin rayuwata ne a haka, ki kula da kanki." zuwa yanzu Siyama itama ta rasa bakinta hakan ya sa ta ja hannun Aaminat ƙiiiiii su ka shige ciki.
Abdulkareem ya ja tsaki kafin ya wuce gida ya na famar mita.
"Aaminat! Aaminat"!! ko kin fiso a kiraki da sunan da ki ka fi dacewa? Bazawara iye Mama ta faÉ—a tana bankaÉ—a labulan É—akin a kwan ce take tana aikin nata na kuka dariya Mama tayi tace "eh lalle ne zawaru
samun guri kina gani dai Fati basa nan ki tashi kiyi girki kuma in kika gama ba ace ki iba ba" da kai ta amsa mata ganin bata da niyar magana yasa Mama ta juya da lukutayen kafafuwanta.
ciwo kanta yake yi kamar ze faɗi gashi babu me bata magani gas ɗin ta kunna ta ɗora girkin, ta zauna a Kicin ɗin tana tunane tunane ya rayuwar ta zata kasan ce?? shin cikin zawarci zata mutu ko kuwa za ta yi Aure? waze Aureta mutane suna gudun bazawara?, kuka ne ya kufce mata dede lokacin da Umma ta danno kai kicin ɗin sosai Umma take jin kukan har cikin ranta kamar bazata kula ta ba se kuma ta kauda kai gefe tace Aaminatu lafiya ki ke kuka haka??" ba ta kula ta ba taci gaba da gursheƙen kukan ta Umma ce ta kama hannun ta da cewa ba ki da lafiya ne?" kai ta gyaɗa mata alamar eh shuru Umma tayi tana kallon Aaminat da duk ta rame
cike da nuna damuwarta akan ta tace "kije Umar ya kai ki asibiti kinji, ke ce bakya jin magana Aamina kin kashe Auren kuma kin ƙi yin wani, darajar Ƴa mace fa Aure ne" to kawai tace mata daka haka bata ƙara cewa komai ba har Umma ta fita.
A haka ta gama girkin ta zuba a kula ta ajiye batare da taci ba ko ta É—iba ta nufi É—akinsu,
gado ta faɗa taja ƙaton bargo ta rufa tana rawar sanyi jitake tamkar kan ta ze faɗi sabi da tsabar ciwon da ya ke yi mata.
Zaune suke a Falon Ummi suna fira Abdulkareem ya É—an daki kafaÉ—ar Abdurrahim yace "kana sha" "amma kaÉ—an" cewar Abdulmajid dariya suka sa Abdulmajid ya hantsulo daga kan kujerar da ya kashingiÉ—a, yace "kai anayi muna dariya jiya naga wata Cika ta ci wanka za ta je gaiyar soÉ—i ta ji fenti an sa mata wannan hodar tasu fuskarta jajir amma wuyan kamar an babbaka kan rago"
wani ihu suka sa suna dariya Abdulkareem ya dafe kai yace "Jar uba jiya kuwa naga anyi yasar wata rijiya a wata unguwa da nasani na É—ebowa su Nana Fareeda su bursuna" ta zabga masa harara ta murguÉ—a baki
tace " A haka ake gani a ƙyasa ehhe" dariya suka yi "haka zakaga wata ƙafa karsan karsan fuska kuwa taci kwailin" Nana Fareeda ta ɗago tana kallon su tace "nide ai ba bilitin nake ba balle ku ce" Abdulmajid ya ce "waya sani ko kina ɗanawa" Abdurrahim ya ɗan dafa kai yace "gaskiya an ciki wasa"
Abdukareem kuwa kallon ta yayi ya ɗan yamutse fuska yace "wani goshinki kamar jirgi" zaro ido tayi ta shafa goshin nata taji hakan yake ko kuwa kuka tasa tana kwashe littattafan ta da gudu tayi sashin Ummi tana kuka kan Ummi tafa ɗa tana cewa Ummi kinga su Auta ko se tsokana ta suke murmusa wa ta yi tace "kamar baki san halin su ba kike musu kuka kuka?" "To ai ni tsokana ce ba na so, kuma na ce su bari sun ƙi. Ummi ta murmusa gami da rausayar da kai.
Abdulkareem ne ya miƙe gami da cewa "Ni fa Abokaina su na jirana bari in yi waje." Abdulmajid ya ce "To Abokin Abokai, sai ka shigo." bai ce komai ba ya yi hanyar fita.
A Garden ya tarar da Dadda ya na zaune shi kaɗai ya na ƴan aikace aikacensa, har ya wuce Dadda ya ce "Babban Mutum" shafa kai ya yi gami da cewa "Wai Baba sai da ka ganni??" Murmushi Dadda ya yi ba tare da ya ce komai ba, Abdulkareem ya ƙaraso ya nemi kujera ya zauna gami da cewa "Barka da Dare Dad ba ka kwanta ba??" "Lafiya lau! kwanciyar me zanyi bayan na aje ku kuma ku ba ku kwanta ba??, An sanar min wani ya mareka waye shi??" zaro ido ya yi ya na cewa "Waye ya gaya maka??" gyaran murya Dadda ya yi hakan ya sa Abdul ya yi saurin gyara zamansa domin kuwa a tsarin Daddy ba a Maido masa Tambaya ba tare da an bashi amsa ba "Wallahi Dad Glass ɗin Mota na fasa masa" a ɗan mamakance Dadda ya ce "Babban Mutum!!?? Me yasa to??" "Wata Yarinya ya ɓare ne shine nima na ɓare mar Glass ɗin ka ga mun yi ragas" "Wace yarinya ce??" "To dai ga ta nan dai Baba Ƙanwar Abokina ce, to kuma kasan ba na ɗaukar Hau. Daddy ya ce "Tooo!! Ina fatan an kaita Asibiti ita Yarinya" "Ahh!! Dadhh!! ba ina nan ba wai? kasan za a yi komai akan tsari ai" ya yi maganar cikin sigar shagwaɓa, Dadda ya ce "Tashi ka je inda za ka tafi, amma ka dinga kulawa fa" miƙewa ya yi gami da cewa "To"
Ya na fita su ka sake sabuwar hira don jiran zuwansa dama su ke yi.
Aaminat
washegari ta tashi da sauƙi dama yawan kuka ne ya haddasa mata ciwon kan, bayan ta yi bacci kuma ya lafa. Ta na zaune ta na wanke-wanke Umma Sa'a ta yi sallama, amsawa ta yi ta na murmushi ta ce "Umma Sa'a Sannu da zuwa" a yatsine ta ce "Yauwa Aaminat, wanke-wanken ne don lalacewa sai kusan Azhar ake yinsa? akwai girɗeɗiyat mace kamarki a gida amma don baƙar ƙazanta sai yanzu ake yin wanke-wanke?? ba dole ma Aure ya mutu ba" A sanyaye Aaminat ta ce "Wallahi Umma Sa'a ba hakan ake yi ba, yau ne don ba ni da lafiya ban yi da wuri ba" "Ke dalla rufen baki, ai ke yanzu rufin asirinki ki yi Aure kuma ki gyara ƙazantarki don ba mijin da zai yarda da wanke-wanken Azhar, kin ga yanzu ma IV na Auren Ƙanwarki na kawo amma ke sabi da kin sa ido a Duniya ba za ki yi Auren ba" "Ni fa Umma ba ku fahimce ni bane, wallahi gabaki ɗaya mummunar fahimta ku ka yi min, ni ban taɓa ƙin Aure ba, me zai sa ma na ƙi Auren??"
Â©ï¸ INDO & AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin HaÉ—aka ne💪ðŸ¾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S
Shafi 2
Bismillahirrahmanirrahim
Wato ya lura Duniya idan ba ka tsaya mata ba ita kwanta maka za ta yi, mutum ne mara gaskiya amma ba za ka yi magana ba sai ka zama tsinanne.
Da wannan tunanin ya kwana, washegari tin safe ya shirya Ya nufi Kasuwa.