← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 38

Sashe 38

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Abdulkareem yana zaune akan kujerar Falo, ya lumshe ido, yayi nisa a duniyar tunane-tunane, Husna kuma tana daga gefen sa sai sharar hawaye take, kuka take mai cin rai amma bakowa ne zai san tana kukan ba, dan kuwa kuka ne mara sauti, shikan shi Abdulkareem É—in baisan tanayi ba,

Washe gari da safe kowa ya tashi shida Amaryar sa cikin farin ciki da annashuwa, kowa na kula da masoyinsa,

"Husna" ya kira sunan ta cikin sarƙaƙƙiyar murya, cike da ladabi ta juyo tare da risinawa, ta ce "na'am" murmusawa yayi gami da cewa "Siyama kina sona ko dole akayi miki,??" ya watso mata tambayar gami da tsira mata idanu, ƙasa tayi da kai kana ta ce "ina sonka na daɗe da sonka acikin zuciya ta kawai ina kauda kai ne, ko alokacin da kake son Aaminat lokaci lokaci nakanji ina kishin hakan, ko da yaushe addu'a nake Allah ya nuna min ranar da zan zamo mata agare ka, sai dai kash baka sona" ta ƙarasa maganar tana sharar ƙwalla, da sauri yasa hannu yana share mata hawayen cikin nutsuwa ya fara magana da cewa "ba wai bana sonki bane, nayi tunanin mahaifina ne yasa iyayen ki sukayi miki dole shiyasa, ko jiya da naji kina kuka nayi tunanin bakya sona ne" ya numfasa, kana ya ce "ina sonki Siyama ba tun yauba sai daga baya na gane ina sonki," wani murmishin farin ciki ne ya kufce mata, ta sa tafukan hannayen ta ta rufe furkar ta, wani ni'imtaccen murmushi ya sakar mata, yana kallon, kyawawan hannayen ta da sukaji lalle, ƙoƙarin tashi take taji ya ɗauke ta calak, ya nufi uwar ɗaki.

(😳kutt!!! Abdul!! Indo ta tsorata😳)

Bayan sati biyu da biki duk wani wanda ya halacci taron ya koma gida.

Ɓangaren Yarima da Aminat ma soyayya ba kama hannunn yaro,

Haka ɓangaren Abdulkareem da Siyama ko da yaushe suna manne da juna,

tsakanin Abdulkareem da Aaminat kuwa sun manta da sun taɓa wani abu wai shi soyayya, zumunci suke sosai dama Abdilkareem da Yarima Aminan juna ne Siyama da Aaminat ma tamkar ya da ƙanwa,

Ɓangaren Fati ma da Ahmad sun watsar da duk wani abu, sun kama ga Allah rayuwa suke cike da son juna, suna da ƴa guda ɗaya wadda taci sunan Aaminat ana kiranta da Meenal,

Ɓangaren Kamal ma Alhamdulillah rayuwa tayi kyau,

Umma da Mama ma sun haɗe kansu tamkar wani abu bai taɓa faruwa ba,

Alhaji Aminu mai kasuwa da Alhaji Sadiƙ, Amintar su kullum ƙara gaba take duk inda kaga ɗaya to ɗayan ma yana nan,

Ammi da Anti Zainab ma rayuwa suke tsaftatacciya.
Anti Rahina ma da su Yarima harda su Abdul kai ahaÉ—e yake ita ce Babba ita da Anti Maryam,
ko wane ɓangare kagan su gwanin ban sha'awa, in ba faɗa maka aikai ba bazaka ce ba dangi ɗaya bane.

Bayan shekaru bakwai,

Allah ya azurta Abubakar (Yarima) da Aaminat da ƴaƴa kyawa wa guda biyu, mace da namiji, na farkon yaci sunan Abdulkareem ƙanwar shi kuma taci sunan E'iye Rukayya ana kiran ta Nihal, Ma sha Allah, saidai muce Allah ya ƙaro zuri'a mai Albarka da kwanciyar hankali na har a bada,

Ɓan garen Abdurrahim da Umaima ma sun Haifi ɗa ɗaya Samid.

Abdulkareem da Husna (Siyama) Allah ya basu kyautar Æ´aÆ´a biyu, ta farkon mai sunnan Ummi Kareematu tana amsa suna, Najwa,
Nabiyun kuma yaci sunan Mahaifin Siyama, Habibu, ana kiran sa, Abba,

Alhamdulillah su Ya Omar da Kahdija Allah ya basu Æ´a, É—aya taci sunan Umma Fa'izatu ana kiran ta, Neehla,

Abdussalam da Iman ma Allah ya basu kyautar Æ´aÆ´a Biyu, É—aya yaci sunan Dadda yana amsa, Hanif, Sai Hanifa,

Abdulmajid da Salma ma suna da É—a É—aya, wanda yaci sunan Uncle Rabi'u.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya ko wane ɓangare sai Farinciki da ƙaunar Juna, Ziyara kam ba kama ƙafar yaro, lokaci lokaci sukan haɗa kwarya-kwaryan taro, ƴaƴan suma sunyi shaƙuwa sosai da ƴan uwan su,

SAIDAI MUCE ALLAH YA ƘARA ZUMINCI DA HAƊIN KAI BAKI ƊAYA.

Alhamdulillah Alahamdulillah

(Mun taƙaita labarin nan sabida wasu ƴan dalilai da abubuwa da su ka yi mana yawa, mu na fatan kun yi farin ciki da karantawa wannan Littafi, Allah i bamu ladan Alkairan cikinsa, kusakuren cikinsa kuma Allah i yafe mana baki ɗayanmu)

INDO&AUTA
Chapter 38 · 0% Book details