← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 38

Sashe 13

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sun yi sa'a su na zuwa Wata Malamar Asibitin da ta ga jikin nata ba daÉ—i ta ce su shiga wajen Likita don samun temakon gaggawa.
Bayan sun shiga Ɗakin Likitar ta yi mata nuni da kujera gami da cewa "Zauna." zaman ta yi ta na maida numfashi duk ya bi ta gaji ga tafiya ga rana. Likata ta ce "Meke damunki??" "Zazzaɓi da Ciwon Kai sai kuma wani ciwo a ƙirjin...." sallamar wani matashin Saurayi ce ta katse mata magana, Likitar ta fara fara'a gami da miƙewa tsaye ta na cewa "A'ah marhabin da Manya, Yallaɓai yau ku ne a Asibitin namu?" Fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Hajiya Maimuna mu ne da tsakar ranar nan." Hajiya Maimuna ta ce "Sannu da zuwa; ke patient Allah ya temake ki ga Babban Likita sai ya duba ki don na ga larurarki babba ce, kin zo a sa'a." ya ɗan shafi sumarsa ya na dariya gami da cewa "Kai Hajiya Maimuna, ba daɗewa zanyi ba fa, wani Patient zan duba shi yasa ma ki ka ganni." Hajiya Maimuna ta yi dariya gami da cewa ''To ai Dr aikinku ne temakon Al'uma kar mu yi haka yau, temaka mata." ya ce "Idan na fito sai a turo ta." Hajiya Maimuna ta ce "To Mu na godiya." bai ce komai ba ya ɗauki abin da zo ɗauka sannan ya fice, Hajiya Maimuna ta zauna kafin ta ce "Na fa yi miki murnar ganin DR Yarima Ƴar nan." a marairace Aaminat ta ce "Ni fa ban damu da ganin Babban Likita ba, Allah shi ke yayewa don Allah ki saurare ni ba na son jira, ko a zaunen nan ma wahala na ke sha" Hajiya Maimuna ta ce "Minti nawa ne zai gama ya dawo kanki?, ke ba za ki gane komai bane; ki ga yadda ki ka wani ɗauke gabaki ɗaya, ki na fa da babbar matsala Yarinya, koma Kujerar nan ta gefe ki bawa Al'umma guri, don ma kin samu zai ganki shine za ki yiwa mutane iyayi." cike da takaici Aaminat ta miƙe ta koma gefe ta zauna, ta na jin Hajiya Maimuna ta na cewa "Zazzaɓin naki ya samo asali gwara ki zauna a ɗora ki akan layin magani daidai da larurarki." ba ta ce mata komai ba don kuwa itama ta shiga sahun waɗanda ta ke jin haushinsu.

Ta daɗe ta na jira sannan wata Ƴar Budurwa ta shigo da sallama, bayan Hajiya Maimuna ta amsa ta ce "Dr Yarima ya ce a tura masa wadda ki ka ce." Hajiya Maimuna ta ce "Ga ta nan, rakata " a yatsine budurwar ta ce "Ki taso" Aaminat ta tashi ta mara mata baya.

ya na zaune ya harɗe ƙafa akan kujera sai danne-dannen waya ya ke, ko ɗago kai ya kallesu bai yi ba, Budurwar ta bata gurin zama sannan ta fice.
Aaminat ta ce "Zazzaɓi da ciwon kai nake sallame ni sauri nake." ɗan murmushi ya yi ba tare da ya kalleta ba ya ce "Ba shi kenan ba, faɗi gaskiya." Sai a lokacin ta tuna zafin da ta ke jin Zuciyarta na yi ta zaro ido tare da tambayar kanta ba dai Ciwon Zuciya bane?, Sai a lokacin ya ɗago ya zuba mata idanu gami da cewa "Zuciyar ta na ciwo ne??" tsuke bakinta ta yi ta kauda kai, sai a lokacin ma ta tuna ashe a zahiri ta yi magana; banza ya yi mata ya ci gaba da danna waya ganin haka ya sa ta ce "Zafi nake jin ta na yi haka kamar Ciwo ko da yaushe sai na dinga jin Ƙunci." ya ce "To Hawan Jini gareki ko Ciwon Zuciya??." da sauri ta ce "Kai Malam ba na son neman bala'i cewa nayi zazzaɓi nake." ya yi dariya kafin ya ce "A alamunki ba ki da faɗa amma zafin ciwo ya sa kin fara; kan ki ya na juyawa ne ko kuma jiri?" ta gyaɗa kai alamar eh, ya ce ''Ina Mijinki ??" duk da ba lafiya gareta ba sai da ta harare shi sannan ta ce "Meye haɗinka da shi???" "Kamata ya yi na yi magana dashi akan lafiyarki mana." "To ba ni da Miji yanzu a gaban iyayena nake, kar ka ɗakko min abin da ba zan iya ba kawai ka rubuta min maganin zazzaɓi." tuntsirewa ya yi da dariya kafin ya ce "Wallahi zafin nan naki ya na bani armashi Aaminat!; Dole fa sai kin yi gwaje-gwaje, gobe ki dawo." ganin ta zaro masa ido ya sa shi cewa "Ya dai?" ta ce "Wa ya faɗa maka sunana??" idanunsa ne su ka ƙara girma, lallai ya kusa ya yi ɓaramɓatama da sauri ya ce "To kin taɓa ganin anga Likita a Asibiti ba tare da an bada suna ba?" ta yarda da hakan don haka ta ce "Yanzu sai me? gida nake son tafiya." Rubutu ya yi a Farar Paper sannan ya miƙe gami da cewa "Mu je Pharmacy ki karɓi magani." ba ta yi musu ba ta bi bayansa, da kansa ya harhaɗa maganin sannan ya ce ta biyo shi kuma ya ƙi bata maganin, ba dan ranta ya so ba take binsa zaizai duk inda ya yi ta na biye da shi, Siyama ta na kallonsu cike da mamakin ta yadda akai lokaci ɗaya Ƙawarta da Dr Yarima su ka zama kamar da can sun saba, ganin za su fice daga Asibitin ya sa ta miƙe ta bi bayansu cikin sauri.
Wajen Motarsa ya nufa ya buɗe mata baya gami da cewa "Shiga na raka ki gida." banza ta yi masa kamar ba ta ji shi ba, Siyama ta yi zuruf ta shige ta na cewa "Mun Gode Dr Dama da kyar ta iya zuwa wallahi ka temaka." "Ke kuma daga ina?" "To ai ni ce na kawota Asibitin ni ƙawarta ce; ke Aaminat idan ba za ki shigo ba sai ki daɓa a ƙasa, ai kinsan Dr Yarima dai kuma kowa ya san shi ba sace ki zaiyi ba kuma bai yi kama da mutanen banza ba bare ko ki ce." Dr dai ya na jinsu nashi aikin dariya kawai don kuwa yanayin Tirjiyar Aaminat ya mugun sa shi a kwalba.
Sun daÉ—e a tsaye ita da shi sannan ta ji wahala ta shiga Motar, ga rana ga rashin lafiya.
Su na tafiya DR da Siyama su na hira yawanci tambayoyi ya ke mata akan abin da ya shafi Aaminat da rashin lafiyarta,
Ita kuwa sai bashi amsa take yi daki-daki.

©️ INDO Tare da AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)

Littafin Haɗaka ne💪🏾

Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S

Tare da

Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S

Shafi 11

Bismillahirrahmanirrahim

Hirar tasu ta na bala'in Ƙona Zuciyar Aaminat don ita gani take duk sun dameta.
abin da ya bata mamaki har ƙofar gidansu ta ga ya je tsaf ba tare da wani ya yi masa kwantance ba, ta tambayi kanta ta yadda hakan ta faru amma sai ta basar don kuwa ba wannan ne a gabanta ba.
Siyama ta buɗe murfin Motar ta fita ta na cewa "Ni fa ban san da yaren da zan yi Godiya ba Yallaɓai." Ya yi murmushin gefen baki, daidai lokacin da Aaminat ta ke shirin fita daga Motar ya ce "Ƙawarki ta na da Mutunci sosai, ba ruwanta da faɗa ga sauƙin kai, a taƙaice dai ta haɗu ta ko'ina." Tsam ta tsaya kamar wadda ya ɗaure har sai da ya gama maganar sannan ta ja sangalalen ƙafafunta ta yi gaba. Cikin Hanzari ya fito har tuntuɓen harshe ya ke garin kiran Sunanta, ta tsaya sauraren abin da zai ce ba tare da ta waigo ba, "Aaminat ki kwana a shirye kuma cikin zaɓi biyu, ko in zo ƙofar gidanku in ɗauke ki ko ki zo Asibiti ki sameni." sai a lokacin ta juyo hawaye sun cika kwarmin idonta, cikin rawar murya ta ce "To duk na meye? ba dai Magani ne ba to ai ka bani." ya girgiza kai gami da gyara tsayuwarsa, cikin muryarsa me cike da nutsuwa ya ce "Aaminat ki na buƙatar test ai na faɗa miki tin ɗazu, ba zan iya zuba Ido ina kallo ki cutu ba don ni likitan Al'uma ne ko kuma in ce na waɗanda ba za su iya ba, temaka miki a wannan Ƙadamin kamar Alhakin da ta rataya a wuyana ne, Allah i ƙara lafiya." ya na kaiwa nan ya saka Baƙin Galashinsa wanda ya rufe kyawawan idanunsa sannan ya juya cikin takunsa irin na Cikakken Namiji wanda ya amss sunansa, Ƙasaita nutsuwa ɗagwarmashi ƙwarewa, kaɗan daga cikin salonsa.
Haka kawai Aaminat ta tsinci kanta da tsayawa kallonsa ta kasa gaba ta kasa baya kamar tsohuwar Bishiyar da ta daɗe da kafuwa a guri, sai da ta dena ganin biɗi-biɗin motarsa sannan ta samu ƙwarin guiwar shigewa ciki, ta na jefa ƙafarta ta tsorata sabi da jin dariyar Siyama, ta saki baki ta na kallonta cikin sirkakken yanayi, takaici da kuma mamaki.
Siyama ba tare da ta dena dariyar ba ta ce "Iskancin Loko; ka ga Dr da patient ɗinsa?" ta ƙarasa maganar tare da riƙe haɓa alamun mamaki.
Aaminat ta ja dogon tsaki sannan ta wuce ciki ba tare da ta cewa Siyama ko Ƙwal ba.
Chapter 13 · 0% Book details