← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 38

Sashe 35

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Walid kam duniyar tayi masa zafi saiyayi kamar ya daina kuka, sai ya ƙara fashewa da sabo, Bilal ya dubi Abdul ya ce "dan Allah Guda ka taimaka, ka fito da Mama," sai a lokacin Abdulkareem ya kalle su, ganin sun zira masa ido yasa shi cewa "yakira yayarsa ya sanar mata mana," Walid ya kalle shi ya ce "indai Fati ce tayi hannun riga damu ta juyawa kowa baya kusan sati ɗaya kenan Mama tana kiranta, wani lokaci da ta ɗauki kiran tace kar atakura mata, wani lokaci, ma bata ɗaukar kiran," ya ƙarasa maganar kamar zai ƙara rushewa da kuka, kowa yayi zumu-zumu yana kallon Abdulkareem, shi kuwa ranshi fess, saidai bai bari Walid ya gana hakan ba, Jabir ya numfasa gami da cewa "to yanzu ya za'ayi??" Abdulkareem ya murmusa kana ya ce "yakira ɗayar yayar tasu mana," da sauri Walid ya ce "wai yaya Aaminat,??" "eh ita" sauke ajiyar zuciya yayi sannan ya ce "banajin yaya zata iya taimakawa Mama, domin kuwa alhakin ta ne yake bibiyar Mama" Abdul yaja tsaki gami da cewa "dalla ka kirata an faɗa maka ba'a yafiya, zata yafe mata kuma zata fito da ita ka kira ka sanar mata," yana gama faɗin haka ya tashi, ya nufi gida, yana cikin tafiya yaji garam sunyi karo, ahan kali ya ɗago kansa ya zuba mata wani masifefen kallo, jiki na rawa ta ce "dan Allah kayi haƙuri, wallahi ban kula ba," tsaki yayi gami da cewa "ina idanunki suke, ko aka suke, kina tafiya amma hankalin ki na wani wajen, ƙasa Siyama tayi da kai, ƙirjinta yana wani bugu, Abdul ya kauce ya fara takawa, cikin ƙasaita,,

Walid yana kiran Aaminat ya zaiyana mata komai, numfasawa tayi, sannan ta ce "Walid ka kwantar da hankalin ka, kaji zanzo in biya duk bashikan da Mama taci yanzu," cikin farinciki ya ce "ya Aaminat samun kamarki da wahala, kin manta duk wani sharri irin na Mama kan manta munanan ƙazafin da tayi maki," murmushi tayi mai ciwo ta ce "hannun ka baya ruɓewa ka yanke ka jefar, Mama uwa ce gareni, kuma tana cikin wani hali, kaga dole zanyi ƙoƙari naga na fitar da uwa ta" "haka ne yaya Allah ya saka miki da alkairi," "amin" daga haka sukayi sallama,

Yarima ta kira ta sanar masa, yaso ya hana ta amma da ya tuna ko wace Mama a wajen Aaminat sai ya amince, bata ɓata lokaci ba ta shirya tsaf cikin Atamfa riga da zani, ta zindima hijab ɗinta har ƙasa, sannan ta fito ta umarci Direba ya kaita, inda zataje.

basu ɓata lokaci ba suka isa, ofishin ƴan sandan, tana shiga ta hangi Mama a cikin ɗan wani ɗaki, tayi muzu-muzu kana gani kasan ta wahala, gaisawa sukayi, cikin mutuntawa, sannan Aaminat tayi musu bayanin duk Abinda ya kawo ta, Mama kuwa tana ganin Aaminat ta ƙara rushewa da kuka mai cike da nadama da danasani, saida suka ɗauki lokaci suna magana da ƴansandan sannan Aaminat ta biya su Mara da Lantana kuɗin su, tayi ƴan cike-cike aka fito da Mama, Aaminat ta juya zata tafi taji, an rungumota, cikin muryar kuka, Mama ta ce "Aaminat ki yafe mini na zalumce ki, ni kuma ga tawa ƙaddarar, ta sanadin Fati na shigo wajen nan amma Fati bata damu dani ba," ta ƙarasa maganar tana kuka, Aaminat ta kama hannun Mama ta jata suka fita, murfin mota ta buɗe ta ce "Mama ki shiga muje ki rakani duk inda ake binki bashi abiya su," Mama tana kuka ta shiga motar.

haka suka dinga bi gida gida ta biya su kuɗin su, sannan suka wuce gidan Aaminat, saida Mama tayi wanka taci Abinci, ta ƙara nemar yafiya, Aaminat ta ce ta yafe, tasa Direba ya maida Mama gida,

Washe gari da safe Abba ya shirya tsaf zai fita, Mama ta fito daga ɗaki, simi-simi "dan Allah kayi haƙuri Alhaji, ko kallon ta baiyi ba yayi gaba abin sa, Mama ta rushe da kukan nadama da da na sani, Umma ce ta fito daga ɗakin Abba ta fara rarrashin Mama,

Abba yana fita yaci karo da wani bawan Allah, baki sake Abba ya tsaya yana binsa da kallon mamaki, da al'ajabi, mutumin yaja ƙafa ya ƙarasa inda Abba ya tsaya, ya ce "Abba Kamalu ne, nazo ne na nemi yafiyar ka da Aaminat dan Allah kuyafe min, cikin mamaki Abba ya ce "Kamalu kaine ka koma haka,???!!!" "nine duniya ta ladabtar da ni, haƙika na cutar da baiwar Allah wadda batasan komai ba sai gaskiya da Amana, Abba duk wasu munanan magan ganu da na faɗa akan Aaminat wallahi ƙarya nake sharrin zuciyane," ya ƙarasa maganar yana kuka, Abba kam ya kasa koda motsa ɗan yatsa ɗayane sai ido, Kamal ya kara cewa "maganar tana bin maza agida na itama sharri ne ƙazafi ne, nayi hakan ne dan na tozarta ta na rabu da ita, na Auri wata, sai gashi wadda na Aura ɗin neman yar uwata take, ina azabtuwa awajen ta ta rabani da duk wani abu da na mallaka, hatta iyayena ta rabani dasu," ran Abba in yayi dubu ya ɓaci ji yake kamar ya shaƙe Kamal ya huta, cikin ɓacin rai "Abba ya ce haƙika ka cuce ni kasa na juyawa ƴar ciki na baya, ƴar da tafi kowa ladabi da biyayya, tafi duk sauran ƴaƴana tausayamin, amma kasa na juya mata baya nake azabtar da ita, amma kaje kaida Allah ni nayafe maka," cikin kuka Kamal ya ce "haƙiƙa nine silar rushewar farin cikin ƴar ka, ko bakomai duniya ta hukunta ni yanzu na rasa duk wani abu na farin ciki, ina fuskantar tsanani," ya ƙarasa magnar yana shash-sheƙar kuka,

Abba ya juya zai tafi, zuciyar sa cike fal da baƙin ciki da takaici, tabbas yayi gangancin yarda da abinda Kamal ya faɗa masa lokacin da ya saki Aaminat, cikin sauri Kamal yaja ramammun ƙafafuwan sa, ya tari Abba cikin muryar kuka ya ce "don Allah kayi min hanyar da zan nemi yafiyar Aaminat," cak Abba ya tsaya zuciyar sa tana wani irin tuƙuƙi, Kamal ya haɗa hannayen sa waje ɗaya ya ce "don girmin Allah na roƙeka ka taimaka min na nemi yafiyar ta wallahi in ban nemi yafiyar ta ba ruhina ba zai samu salama ba," Abba ya kalle shi sannan ya ce "yanzu Aaminat tana ƙarƙashin ikon mijin ta ni bazan iya yi maka hanyar da zaka gana da ita ba saida izinin Mijin ta," "na yarda kanema min alfarma awajen mijin ta in nemi yafiyar ta," Abba ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Omar dake tsaye, yana jinsu, ya ce "Omar ka kira Abubakar ka sanar masa, in ya Amince ka rakashi, amma karka kuskura ya shigar masu gida," cike da girmamawa Omar ya ce "to Abba amma ni bazan iya ɗaukar wannan ƙazamin mutumin ya mashin ɗina ba," "kayi haƙuri ka raka shi, dole ce tasa" badan yaso ba ya ce "to" Abba ya wuce yashiga motar sa, Omar kuwa sai jan tsaki yake yana zabgawa Kamal harara, Dr Yarima ya kira yayi masa bayanin komai, Yarima bai musa ba jin ance Abba ne yasa akirashi asanar masa, hakan yasa ya amince amma bawai dan yaso ba, Omar kuwa takokin yadda zai ɗauki Kamal yake amashin ɗinsa acewar zai ɓata masa mashin, ganin bashida zaɓi ne yasa ya ce Kamal ya hau sutafi, yana hawa Omar ya figi mashin ɗin,

Basu daɗe ba suka isa, aharabar gidan Kamal ya tsaya, Omar yashiga ya ce da Aaminat ta fito, amma bai faɗa mata kowaye ba, batare da tunanin komai ba ta zira hijabi ta bi bayan ya Omar, suna ƙarasawa harabar gidan tayi turusss ganin Kamal, rai a ɓacen-ɓace ta juya da niyar komawa, Omar ya ce "kiyi haƙuri ki tsaya ki saurare sa,"

"Babu abinda zanji daga gare sa sabi da haka kace ya tattara mummunar fuskar sa ya barmin gida ko nasa ayi masa korar kare" tana gama faɗin haka taci gaba da tafiya, Omar ya sha gaban ta ya ce "karki manta da cewa muma munayi wa Allah laifi kuma munemi yafiya ya yafe mana" tsayawa tayi tana huci, Kamal kuwa kuka yake yana cewa "dan Allah ki gafarce ni ki yafe min duk abinda na aikata miki dan Allah, "kaje na yafe maka duniya da lahira, Allah ya shirye ka," tana gama faɗin haka ta juya tayi ciki, "Ahamdulillah Allah na gode maka, da kanuna min wannan rana, Aaminat da mahaifinta sun yafe min," Kamal ya faɗa yana jan siraren ƙafafuwan sa, Omar ya kalleshi ya ce "inna ta gaida Ashsha," Kamal ya juyo ya kalli Omar yana goge hawaye, Omar kuwa yana gama faɗin haka ya zuge ƙofar gilashin ya shige cikin tafkeken Falon,

INDO &💗 SALMA[8/12, 6:24 AM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)

Littafin Haɗaka ne💪🏾

Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

Tare da

Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION

Shafi 30

Zama yayi ya kalli Aaminat dake razgar kuka ya ce "ke kuma kukan me kike!!" share hawayen tayi ta ce "nifa ba kuka nake ba" "kice dariya kike," sakin baki tayi tana kallon ya Omar, tsaki yaja gami da cewa "nifa wallahi haushin mutumin can nakeji kuma kika zauna kina yi masa kuka" "wai kai ana maganar mutane kana sako zaburarru," dariya yayi batareda yace komai ba, shiru ne ya ɗan ratsa na wani lokaci, Aaminat ta katse shirun da cewa, "Bari in kawo maka abinci" "ke nifa da tafiya zanyi amma tinda kin matsa ba komai" miƙewa tayi tana cewa " Ya Omar nawa niko ta Allah" harara ya maka mata, ƴar dariya tayi, ta nufi kicin,
Chapter 35 · 0% Book details