← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 38

Sashe 19

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tana shiga gida ta faÉ—a kan gado tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya.
Siyama ce ta shigo ɗakin tare da sallama, Aaminat ta amsa tare da cewa "dama so nake naje gidanku yanzu se gaki," Siyama ta ce "Yariman ya tafi??" wani kallon sheƙe-ƙe Aaminat tayi mata gami da cewa "to in be tafi ba a ɗakin nan kikeso ki ganshi? ba daga ƙofar gida kike ba?" Murmusawa Siyama tayi ba ta ce komai ba ganin haka yasa Aaminat cewa "Siyama Yarima yana sona nace zanyi shawara ki bani shawara" rausayar da kai tayi sannan ta ce "ni a ganina Yarima bashida wani aibu mutum ne me dattaku da kuma sanin ya kamata sabida haka ki amince masa kawai" shiru ta ɗanyi kafin ta ce "Siyama kiyi tunani ya Abdul zeji idan har naso wani ba shi ba kuma shi ya fara cewa yana sona sannan Yarima" tsaki Siyama tayi kafin ta ce "kinga kema kinsan kina son Yarima kuma me zesa kidinga tunanin Abdul shifa ba sonki yake ba kawai tausayin ki ya keji kuma shi Abdul inde har Yarima ze saki farinciki to ze iya haƙura ya barwa Yarima" shiru ne ya ɗan ratsa na wani lokaci kafin Siyama ta ce "ni zantafi" "ince mai ina sonshi??!" "ruwa ya rage naki" "Siyama wai meyasa kike wani fushi-fushi ne??" murmushi ta ɗanyi ta ce "ba fushi nake ba kede kawai in Yarima ya kiraki to kice mai kin amin ce dan Allah ba don nu ba, nima kaina ina so in ga kin fita daga wannan halin, ace mutum ba shi da aiki sai tunanin bara anci wake" "in sha Allah zan faɗa mai ki de tayani da addu'a Allah yasa Alkairine" "Ameen" Siyama ta ce sannan ta fita.

Misalin ƙarfe tara na dare kira ya shigo wayar Aaminat ta ɗauka zuciyar ta na wani bugu-bugu sallama yayi mata, ko ba a faɗa ba tasan Yarima ne "Assalamu alaiki sarauniyata fatan kina lafiya" ta amsa da cewa "Wa'alaikumussalam lafiya lau" shiru ne ya biyo baya kafin Yarima ya katse shirun da cewa "kina farin cikin shiga rayuwarki da nayi kuwa??!!" murmushi me sauti ta ba tare da ta ce komai ba, hakan ya bashi damar ci gaba da magana "amincin Allah ya tabbata gareki a duk tsawon rayuwarki masoyiyata, ina so ki faɗa min ko da hankalina zai kwanta numfashina ya dena sassarfa, shin kin aminta da soyayyata???!!" rasss!!!!!! taji gabanta ya faɗi ta yi shiru ta na zazzare ido, jin ya ƙara maimaita tambayar yasa ta tattaro nutsuwar ta fara magana cikin in ina "na...na.amince" "Alhamdulillah Allah kai ne abun godiya Allah na gode maka da ka mallaka min zuciyar da nadaɗe ina muradin samunta".. bayan ya gama godiya ga sarki Allah ya ci gaba da cewa "Ina Sonki Aaminat !! Ina fatan kema ki so ni da dukkan Zuciyarki" wani murmushi me sauti ne ya kufce mata shima murmushin yayi, ta ce "ina jin bacci se da safe" sukayi sallama cike da farin ciki da jindaɗi.

haka rayuwa taci gaba da tafiya na wani lokaci kullum Yarima da Aaminat ƙara shaƙuwa suke....

*Ku Dakata Mana✋🏽🤸🏾‍♀️Saurin Me Kuke🤔 sai ka ce Za'a ci da Rabonku🤔😍* Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.*

*HALY-JASHERU venture's*
*munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.*
*prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA*

sanye take cikin riga Abaya marun tayi rolin ɗin mayafin tayi bala'in kyu sosai duk da bawata kwalliya me hayaniya tayi ba amma tsan-tsar kyawun ta ya ƙara baiya na dama Aaminat fara ce ƙal dan Umma ta biyo a fari.
mudubi ta kalla fuska ɗauke da murmushi ta ɗauki turare ta feshe jikinta sannan ta zira takalmin ta, Umaima da bata iya shiru ta ce "yaya ina zuwa haka kinyi kyu wallhi" murmusawa tayi ta ce "gidan su Siyama zani" Umaima ta ce "bari nazo muje" kafin kace meye wannan ta yafa mayafin ta, Aaminat ta ce "kai kin fiya son yawo wallhi" "nide muje" fita sukayi ƙofar gida kamar daga sama taga Abdulkareem sanye cikin shigar ƙananun kaya riga fara da wando baƙi yayi bala'in haɗuwa yajingina da tamfatsetsiyar motar sa me tsadar gaske ya harɗe kafa tare da kauda kai gefe, Aaminat kuwa zuwa yanzu ta gama tsinkewa da Abdul ido ta tsira masa babu ƙiftawa, jikinta se rawa yake tabbas ta sani yau haƙurin Abdul ya ƙara kuma seta ɗanɗa na kuɗar ta, a hankali ya fara takun shi me cike da ƙasaita da jin kai da kuma zarra, seda ya zo gaf da ita sannan ya tsaya da hannu yayiwa Umaima Alamar ta bar wajan, jikin na ɓari ta saki hannun Aaminat ta fece, wani tattausan murmushi yayi me cike da baƙin ciki da takaici, sannan ya fara motsa kyakkyawan bakinshi ya ce "Aamaint ina sonki amma ba kiyi la'akari da haka ba kike soyayya da wani wanda baki san kowaye a wajena ba,.. ya ɗan numfasa kafin ya ce ko be faɗa miki muna da alaƙa da shi ba?? Aaminat kinci Amana ta kuma ina so kisani har yanzu ina so ki kuma muddin ina raye bazaki Auri yarima ba,.."
"nikam naga rayuwa" ta faɗa cikin ranta wani tsallle zuciyar Abdul take kamar zata fito waje dafe ƙirjin shi yayi tare da cewa "Aaminat ina sonki soyayyar ki tana azabtar dani tabbas zan iya rasa rayuwa ta daga ranar da akace kin Auri wani wanda bani ba".. ya zuba guiwoyin shi biyu a kasa ya karyar da murya cikin sanyi da kuma raunin zuciya ya ce Aaminat ina sonki ina ƙaunar ki kece duk wani farin ciki nawa ido na ya rufe bana ganin kowa seke kunne na ya toshe bana jin komai idan bake ba duk wani mafarki na kece ina sonki soyyayar da ni kaina bansan iya adadin ta ba, son da nake miki ya shafi rayuwar gidan mu dan kuwa yanzu ta sanadiyyar soyayyar ki gidanmu ya canza, Aaminat bata san lokacin da zuciyar ta ta karye ta fara kuka tana cewa, "Dan Allah Abdul karage wannan makauniyar soyayyar da kake min inna ce bana son ka nayi ƙarya amma Abdul shifa Aure ba wasa bane, kaifa yanzu baka isa mizanin da zaka Auri mace kamar ni ba in kuwa ka aure ni to ka tar watsa rayuwar ka karka manta ni BAZAWARA ce" ta ƙarasa maganar tana wani irin kuka me tsuma zuciya, Abdul kuwa ya kasa koda motsa ɗan yatsan shi ne, har yanzu guyawun sa na ƙasa ya sunkuyar da kai, hawaye masu azaba da kuma zafi suna sauka daga idon sa zuwa ƙasa, sun ɗauki tsahon lokaci a haka kafin Abdulkareem ya ta shi ya juya, seda ya taka sau uku sannan ya ɗan tsaya ya ce Aaminat kisa aranki duk tsanani duk wuya sena Aure ki!!!!!!!!!" yana gama faɗin haka ya juya ya shige motarsa ya bata wuta,
da gudu ta shiga gida tana kuka ta wuce É—akinsu...

*Ayeesha Abdulkareem INDO* Ta na me farin cikin Sanar da ku cewa An Fara Karanta Littafinta WATA HANYA a Gidan Radio Garanti Mita 94.7 Ku Kasance da Abdullahi Muhammad SALBAS Domin Jiye Kunnuwanku irin Faɗakarwa Da Nishaɗi da ke cikin Wannan Littafi. Kar kuma Manta Sunan Marubuciyar Ayeesha Abdulkareem INDO, Garanti Radio 94.7 Ƙarfe 5:30pm Daidai

Share Fisabilillah

*©INDO Tare da SALMA AUTA*
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)

Littafin Haɗaka ne💪🏾

Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

Tare da

Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION

Shafi 16

Mama da Fati Suna zaune a tsakar gida suna Taɗi, ganin Aaminat ta shigo tana kuka yasa su jindaɗi Mama ta sheƙe da dariya gami da cewa "Allah sarki bazawara yau ma saurayi ya gudu" Fati ta ce "dama waze Auri bazawara se tsoho ko talaka" Mama ta ce "kekuwa ƴata daga me jirgi se me mota" suka sa dariya kafin su ci gaba da hirar Aaminat.

Aaminat kuwa ta daɗe ta na kuka ganin ba zai kaita ko ina ba ya sa ta share ƙwallarta.
Chapter 19 · 0% Book details