← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 38

Sashe 25

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zaune yake ya buga tagumi yana tunane-tunane Nana Kadija ta shigo da sallama zama tayi kusa da shi, gami da cewa "ya Audu komai fa ƙara zafi yake, ya kamata ka janye maganar Auren nan" wani dummmm!!!! yaji a ƙwaƙwalwar sa tayi, yayi saurin dafe kai, cikin sanyi da damuwa Nana ta ce "yanzu haka Ummi kuka take domin kuwa Dadda ya dora mata laifi ya ce duk ita ce ta ɓata mai yara" a kiɗime ya dube ta ya ce "Ummin ce take kuka???!!!" "eh" "yasalam bari naje wajen ta" da sauri Nana ta riƙeshi ta ce "ko kaje bazata kula kaba nima har nagaji da magana batace komai ba" komawa yayi ya zauna Kadija ya ce "yanzu mafita zamu nemo" ya ce "Dole hakan za'ayi don ba zai yuwu na bar Aaminat cikin wannan halin ba, kuma zan iya yin abinda ba zai yiwa kowa daɗi ba" a gigice Nana ta kalle shi ta ce "nashiga uku ya Abdul a hayyacin ka kake kuwa? me za ka yi kuma haka? don Allah ni dai karka jawo mana abin da ya fi ƙarfinmu ka yi haƙuri" cikin ɓacin rai ya ce "wai ba kince mafita zamu nemo ba??? to mu nemo mana" a jiyar zuciya ta sauke kana ta ce "lokaci yanaja kuma Dadda da Ummi kara sama suke a ganina kaje ka sanarwa da Uncle Rabi'u", da sauri ya ce "Alhamdulillah Allah na gode maka shikenan matsalata kau" Nana tayi dariya kana ta ce "duk kabi ka zauce a kan Bazawara" dan da nan ya ɗaure fuska ya ce "kinga ke fa matsalarki ba a abu da ke sai kin ɓatawa mutum rai" dariya tayi gami cewa "kwana biyu baka da lokacin da zamu ɗanyi faɗa ko yanzu da nace maka Audu babu abinda kace shi yasa na ce haka amma kayi haƙuri" murmushi ya ɗanyi kana ya ce "to yanzu dai zanje nasami Uncle Rabi'u kuma kinga shine sama da Dadda dole Dadda ya risina" amma fa matsalar ɗaya ce kai ma kasan Dadda kaifi ɗaya ne" cije gefen laɓɓan sa yayi kana ya ce "Allah ya dafa ma lamarin kawai shi ne"
daga haka suka cigaba da tattauna wa
*Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta*
*Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.*

*HALY-JASHERU venture's*
*munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.*
*prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA*

"ya Aaminat kinsan kuwa Mama ce ta ziga Abba wai yace a wata zai Aurar dake" sakin baki tayi tana kallon Umaima, cikin mamaki ta ce "wai sai yaushe Mama zata bari nasha ruwa??! ta kurar tata tayi yawa kinga yanzu ta ƙara jefani a masifa" tsaki Umaima tayi gami da cewa "ai wallahi ko samun mata kamar Umma da wahala a gabanta fa ta faɗa amma ta kasa cewa komai saida ta dawo ɗaki naji tana kuka dana tambaye ta sai tace babu komai, saida na matsa mata sannan ta faɗa mini kuma tace karna faɗa miki ni kuma yau na faɗami" wani numfashi Aaminat taja ta sauke tare da gargiza kai" ta ce Ummm Mama kenan haryau bazata karaya ba ai gashina ƴata da tafi fifi-tata yanzu ita ce take mata fitsara iri-iri amma taƙi ganewa" Umaima ta ɗan gyara zama gami da cewa "nifa wallahi ina ganin Auren ki da Abdul kamar ba zaiyuwu ba" Aaminat tayi wani murmushi mai kama da yanzu aka fara kana ta ce "nima ina wannan tunanin amma innna tuna waye Abdulkareem sai na kauda tunanin hakan" murmushi Umaima tayi kana ta ce "nimafa na faɗa komar so yanzu in na kira Abdurrahim baya ɗauka kuma baya kirana" rausayar da kai Aaminat tayi kana ta ce "kinga ai dama haka komai yake, keda Fati baku da aiki sai yaudarar samari gashi kema anyi miki saikiji da daɗi ko babu" ƙasa tayi da kai cike da nadama Aaminat ta ce "amma kita addu'a Allah zai cire miki sonshi" "to" tace suka cigaba da hirar duniya,

tuni Abdulkareem ya shirya tsaff ya ziyarci gidan Uncle Rabi'u ya zayyane masa duk a binda kefaruwa, Uncle Rabi'u ya É—an gyara zama gami da cewa "to duk naji bayanin da kayi mini in sha Allah
yau da yammaci zanje Abuja amma nan da kwana uku zanje nasame shi" Abdul ya murmusa, Uncle ya dafa kan Abdul gami da cewa "karka damu kaji in sha Allah ko mai zai dai-dai ta Allah yayi muku albarka" "Amin" Abdulkareem ya ce tashi yayi gami da cewa "Baba ni zan koma a gaida su ya Abbas" har zaka tafi???" "eh Baba zanje in zagaya masana'antar mu" Baba ya ce "to Allah ya tsare ka gaida Æ´an uwan ka" "Amin" ya ce ya fita inda ya ajiye motar sa,

Bayan kwana uku Yarima ya shrya tsaf yayi kyau sosai babban Falo ya nufa yana tafe yana tunane-tunane harya ƙarasa falon zama yayi akan kujera sannan ya dubi Ammi ya ce "Ammi ina kwana" "lafiya ƙalau" ta faɗa fuska babu yabo babu fallasa, tashi yayi ya ce "Ammi natafi" "ina zaka???!!!" ko ɗarrr baiji ba ya ce "gidan su E'iye" wata muguwar harara tabuga mai tare da ya mutse fuska, juyawa yayi zai tafi ta ce "waɗannan kakan nin naka mayune sun kama kurwar ka yaro tun kana ƙarami nake nesanta ka da su amma sun liƙema" ran Yarima in yayi dubu ya ɓaci, dan haka yaci gaba da tafiya ko waiwayon ta baiyi ba yanaji tana surfa masifa amma yayi ficewarsa,

Bai ɓata lokaci ba ya ƙarasa gidan su E'iye kai tsaye Falon Inni ya nufa yana tafe yana kiran sunan ta cike da tsokana, fitowa tayi daga ɗakin dake cikin Falon tana cewa "sannu da zuwa saurayi na" murmushi yayi gami da zama ya ce "budurwa ta nayi kewarki kwana biyu" murmushi tayi kana ta ce "Allah sarki rabin raina ai kana zuciya ta" dariya ya ɗanyi gami da cewa "ina E'iye" Inni tace "inaga dai tana ɗakin ta ai yanzu rana tayi" shiru ne ya ɗan ratsa na wani lokaci kafin Inni ta ce jikalle na baka da lafiya ne???? naga ka rame" murmusawa yayi gami da cewa "A'a lafiya ta lau kawai dai jiki da jini" "to saika faɗa mana mara jini ajika"! E'iye ta faɗa gamida ƴar dariya juyawa yayi ya kalle ta ya ce "ko sallama bakiyi ba amma kunnan ki yaji abinda nace" murmusawa tayi kana ta ce "ai kunacan kuna soyewa kaida budurwar ka nayi sallamar baku amsa ba" dariya yayi ya ce "to mata ta irin wannan kishi haka" "Allah ya kyauta nayi kishin ka ni yanzu ma ba Auren ka nake ba nasake ka" "subhanallahi dama mata ce take sakin mijin ta" dariya tayi ta ce "ni dai bana Auren" shima dariyar yayi cikin jin daɗin barkwancin da suke shida kakan nin na sa, Inni ta ce "Habu zaka kaini nayi siye'siye??!" "kai Inni banason tsokana ki daina cemin Habu" dariya ta ɗanyi ta ce "to ai sunan ka ne" "to kishirya kuma bazamu da E'iye ba karta samana ido" dariya sukayi sudika,
Inni ta shirya tsff tashe hijab É—inta suka kama hanyar shopping,

INDO CE &&& Salma Auta
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)

Littafin Haɗaka ne💪🏾

Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S Association

Tare da

Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S

Shafi *21*

Basu ɓata lokaci ba suka kammala siyayyar da zasuyi suka koma gida,

kashingiɗe yake a kan kujera yana waya cikin nishaɗi da farinciki sai faman fara'a yake sam ya manta a inda yake ya ce "Aaminat Ina sonki, so na har a bada, in dai inaraye bazan bari kisake kukan baƙin ciki ba" wani ni'imtaccen murmushi ta saki, kamar tana ganin sa, ya ƙara da cewa "Aaminat kece ƴa mace ta farko da nakejin bazan iya rabuwa da ke ba"! "yazama dole karabu da ita kuwa" rassss!! rassss!!! gaban sa ya buga yayi saurin katse kiran yana muzurai, Abdussalam ya ɗan yi murmushi mai cike da ma'anoni ya ce "yaro man kaza" ƙasa yayi da kai, Abdussalam ya zauna gami da cewa "Auta mai yasa ka koma haka???, naga Uncle Rabi'u yazo duk da ban san dalilin zuwansa ba amma na alaƙanta zuwan da kai kaika ce ya zo ko" cikin sanyi ya ce "eh ni nace yazo ya sami Dadda", kallon sa ya ɗanyi cike da tausayawa ya ce "Abdul kayi haƙuri ka taushi zuciyar ka, kabi Umarnin iyayenka" har ga Allah Abdussalam baya jin daɗin yadda suke yiwa Abdul saidai acewar su hakan shine zaisa ya janye maganar sa ta Auren Aaminat, a raunane ya ce "Ya Abdullah ina sonta wallahi ku tausaya mini ku dubi halin da ɗan uwanku yake ciki, ita ɗin abar tausayi ce ina tausaya mata, kutayani ƙoƙarin shawo kan su Dadda," wani lafiyayyan mari ya zuba masa, sai da yaga taurari sun gifta, cikin ɓacin rai ya ce "ni zaka dinga faɗawa kana sonta dan baka da hankali, cikin kwanaki kaɗan ka canza mana gida komai namu ya canza kuma duk ta silar wata matsiyaciyar yarinya," ƙasa yayi da kai dan kuwa ko kashe sa Abdussalam zaiyi baya jin zai iya ɗaga mai murya, rai a ɓace Abdussalam ya bar wajen,
Chapter 25 · 0% Book details