Sashe 12
Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kai tsaye Babban Falo ya nufa ya tarar da ƴan uwansa su na hira ba abin da ya yi tsalle ya tsinka musu mari, ɗan ƙaramin tsaki yayi ya nemi guri ya zauna kusa da Ummi batare da yace musu komai ba, "Ya Audu ko sallama babu??" Nana Kadija ta faɗa cikin sigar tsokana, sai a lokacin ya tuna da be yi sallama ba, ya sunkuyar da kai yana wasa da zobukan yatsunshi "Ya Audu magana fa nake"
harara ya watsa mata sannan yace "Dije kar ki takura min" "ni kake cewa Dije?" "an faɗa Dijen gala Ƴar Gona" turje turje ta fara yi tana cewa "Ummi ki na ji de yana cemin Dije kin ƙi ki hana shi" murmusawa Ummi tayi kafin tace "ke kuma ki ka ce masa Audu banyi miki magana ba se shi sabi da kece Zinariya ko??" Abdulmajid ya ce " Yaran nan in ki ka bi ta tasu Ummi sai bakinki ya yi ciwo, Ko Nana Fareeda da Nana Hauwa'u da suke ƙananu ba sa faɗan nan da su ke yi, kuma na lura rashin duka ne ya ke damunsu, yauwa kai tin ɗazu mu ke jiran shigowarka mu ci Abinci kazo ka tsaya cecekuce da wannan me ƙaton kan" murmushin baƙin ciki da ta kaici yayi sannan yace "wa ya ce ku tsaya jirana?? ni na ƙoshi" sakin baki sukayi suna kallonsa kafin Abdussalam ya ce "Ƙalubale Gareka Ɗan Uwa, Nana Kadija ta ce ruwa kawai kake ta kurɓa sai Juice a duk tsawon yau Yaro in za ka zauna ka ci Abinci ka zauna don in ka dawo ƙashi ba ruwan wani." ya ɗan ɗangale kafaɗa alamar ko a jikinsa.
Ummi ta ɗan muskuta gami da cewa "haba Autana ba'a horon yunwa ka ci Abinci ka ji Babban Mutum!" tingira kai ya yi a shagwaɓe yace "nifa bana son cin Abincin sabi da Aam" ɗiffff yayi yana muzurai, a ran shi yace taɓ yau na kusa zunguro sama da kara. Abdussalam ne ya katse masa tunani da cewa "sabi da me ka ce??"
Abdurrahim ya ce "Tabbas nima na ji zai faɗi wani abu ya fasa, ni dai nasan da abin da ya ke ɓoyewa, wallahi ku tashi mu yiwa Yaron nan Cali-cali yau ya faɗa mana menene a ransa ya ke sa shi rama ta wuya." Ummi tace "kun samin ɗa gaba ku ƙyale shi ni zanji me yasa ya ƙin cin Abincin" rarrashinsa suka shiga yi da ƙyar ya ce zai ci Nana Kadija tace "nasan yadda zamuyi maka se kayi lauma uku se muyi ɗaya" tafawa Nana Hauwa'u sukayi da Abdurrahim Nana Farida tace "kanki yana kawo wuta kamar fulogi" haka suka sashi gaba in yayi Cokali uku se suyi ɗaya tun yana ƙoƙarin ci har ya gaji ya ɓare baki ya fara kuka wai so suke su kashe shi cin yayi yawa. Ummi ta galla masa harara taɗan hade fuska tace zauna se Abincin ya ƙare zaka tashi" komawa yayi ya zauna ya ci gaba da kuka Abdulmajid ya ɗan yi dariya yace "taɓ Jariririnmu babu lafiya gidan ya koma kamar gidan mutuwa an dena dariya" Abdussalam ya ce "Ni fa duk ba wannan ba." su ka haɗa baki wajen cewa "To me????"
© INDO tare da AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin HaÉ—aka ne💪ðŸ¾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S
Shafi 10
Bismillahirrahmanirrahim
"Maganar gaskiya ba zuba masa ido za mu yi ba don ba shi da lafiya, ga yadda ya ke yiwa mutane kuka kamar an tsoma shi a wuta, kun manta tsabar kwainane da Manyance irin nashi ne? gaskiya ya kamata mu kai shi wajen likita ko da likitan Mahaukata ne" Abdussalam ya yi magana cike da son nuna gaskiyarsa, Nana Fareeda ta ce "Kuma wallahi haka ne YaYa Abdussalam." Abdulmajid ya ce "Ni gardama ce ba na so shi ya sa na zaÉ“i na zuba masa ido tinda haka ya ce, ko ka manta ya ce mu zuba masa ido kawai?" Abdurrahim ya ce "To ai amfanin hankali kenan don ya faÉ—a tinda mu da hankalinmu ai ba biye masa za mu yi ba." Ummi ta ce "Gaskiya nima abin ya dame ni sosai, kuma ya na yawan zazzaÉ“i yanzu, amma sabi da kafiya Magani ko Æalli ya Æ™i sha." Goge hawayen ya fara yi ya na cewa "Na dena zazzaÉ“in kuma dama lafiyata Æ™alau, da fa hankalina ta ya zan zauna da cuta." Abdussalam ya ce "Da sauÆ™i dai hankalin naka don in da da shi da yanzu ba wannan maganar ake yi ba, kukan nan da kake yi ma ba dalili ya na É—aya daga cikin Ƙarancin hankalin." ya ja numfashi ya busar kafin ya ce "Ka na nufin Mahaukaci ne ni??" "Ahh ba wai ina nufin Mahaukacin gaske ba, hauka irin na Ƙuruciya nake nufi don ya na da yawa a tare da kai. Abdulmajid ya haÉ—e fuska ba alamun wasa ya ce "Abdulkareem ba na son shirme ka tashi mu je ka ga Likita, idan kuma ba haka ba ranka zai É“aci ka san ba na son Hau." "To ai dama ba cewa na yi ba zan je ba" Abdulmajid ya miÆ™e tare da cewa "Abdussalam ÆŠakko Mukullin Mota kai kuma Abdurrahim ka tawo min da Abdulkareem." Abdulkareem ya miÆ™e ya na cewa "Ni ba sai an tafi da ni ba zan biyoka." Abdulmajid ya murmusa ya na tunanin wai a hakan ya ce ba Ƙuruciya a tare da shi ya na magana ya na kuka kamar wani É—an shekara Uku.
Da su ka dawo bai saurari kowa ba ya wuce Bedroom don kuwa duk haushinsu ya ke ji kamar ya bubbugesu.
Dadda ya dubesu a tsanake sannan ya ce "Na shigo gida na tarar duk bakwa nan ance Babban Mutum ba lafiya." Abdulmajid ya ce "Eh Dadda yanzu mu ka dawo ai." "Me Likita ya ce game da shi?" Abdulmajid ya zauna sannan ya ce "Wallahi Dadda abin akwai ɗaure kai wai damuwa ce ta fara yi masa yawa har Ƙunci ya harba masa zazzaɓe-zazzaɓe.'" Dadda ya zare Glass ɗin idonsa cike da mamaki ya ce "To fa? ikon Allah kenan, Babban Mutum da wace irin damuwa haka?" Abdussalam ya ce "Kullum sai mun tambaye shi me ya ke damunsa amma ba amsa sai dai ya ce ba komai, kuma ni banga abin da akai masa ba." Abdurrahim ya ce "Ko dai a cikin Yaran da ya ke Abota da su matsalar take??" sai a lokacin Ummi ta ce "Kai a'a gaskiya Yaran nan duk ba wanda zai sa Abdul damuwa haka sai dai wani abin, zurfin ciki gareshi ne shi yasa, mu taya shi da Addu'a kawai." Dadda ya Jinjina kai ba tare da ya ce komai ba.
Yau Aaminat ta tashi da zazzaɓi me zafi da ciwon kai, yau ko aikace-aikacen tsakar gida ta kasa yi sai dai ta kwanta in ta gaji ta tashi, fatan ta ɗaya Allah i jefo wanda zai temaka mata ko da ƙwayar Magani ne.
Tana cikin wannan halin Siyama ta yi sallama bayan ta gaida Umma ta shige ɗakinsu Aaminat, da sauri ta ƙarasa kanta ta na cewa "Aaminat me ya faru ne? ba dai zazzaɓin ki ke ba naga jikinki na kakkarwa." A wahalce ta ce "Siyama ba ni da lafiya ki temaka ki karɓo min maganin zazzaɓi in Anti ta na da shi." Siyama ta ce "Ai wannan Rashin lafiya taki ta fi ƙarfin zama, a tsaitsaye ta ke ƙarar dake gashi yanzu har ta kaiki ƙasa, ba zan iya jura ba ki tashi mu je Asibiti." "Ba zan je ko ina ba Siyama, ba na son fita sabi da ina tsoron na yi gamo da wannan mummunan Yaron. "O'o Allah Me Baiwa, ke kuma ki na wannan zazzaɓin amma tunaninki ma kar ki fita ki ga Abdulkareem to in kin ganshi zai ɗauki ranki ne??, wannan fa banzan tunani ne, me yasa ki ke da gardama ne? gaskiya ki tashi mu je yanzu za mu dawo, nan fa ƙaramin Asibitin nan na tsallake za mu je ba wai nesa ba. "To zazzaɓi fa nake ta ya zan iya tafiya? ni dai ki ƙyale ni in ba za ki ban maganin ba. Siyama ta miƙe ta kwance ɗankwalinta ta fita ta jiƙo shi sharaf sannan ta dawo, Aaminat ta miƙawa gami da cewa "Karɓi ki shashshafawa jikinki zazzaɓin zai ragu in sha Allahu sai mu je Asibitin." ba ta yi musu ba ta karɓa ta yi yadda Siyama ta ce duk da ba daɗi.
Cikin kayanta ta duba ta ɗakko mata Hijab ta zura mata sannan ta ɗakko mata takalma, ba ta zauna ba ta ce "Ai jikin ya yi sanyi tashi mu tafi." "Ni wallahi da ƙyale ni ki ka yi Siyama, ki ka sani ko Ajalina ne ya yi in mutu in huta?" cike da takaici Siyama ta ce "To inaga Ajalin naki ne, kuma zuwa Asibiti ya zama dole ko ki tashi ko in sa Abdulkareem ɗin ya ɗakko Motar gidansu ya zo ya kai ki da kansa, kinsan ba kan gado gareshi ba har cikin gidannan zai shigo ya taitayeki, Allah i sa ma ya na nan." ta ƙarasa maganar ta na ƙoƙarin fita daga ɗakin, da sauri Aaminat ta ce "Wallahi Siyama ba na son irin wannan, haba don Allah ba tashi zan yi ba shine za ki fara ambato min sunan Shaiɗanin Yaron nan?." Siyama ta ce "Da ki zauna ma". riƙe hannunta ta yi sannan su ka fito, Umma ta ce "Ina za ku je ne??" Aaminat za ta yi magana Siyama ta yi saurin cewa "Ba ku san ba fa da lafiya ba Umma? Asibitin tsallake zan rakata ai, don abin ya ci tira." Umma ta rausayar da kai gami da cewa "To Allah i yaye."
Ko kulata Siyama ba ta yi ba su ka ci gaba da tafiya.