← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 38

Sashe 17

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*HALY-JASHERU venture's*
*munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.*
*prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA*

A Falon Farko ya tarar da E,iya ta na zaune kan kafet ta na Azkhar, ta sha Hijab wanda ya karɓi fusukarta ta yi kyau sosai, zama ya yi kan kujera ya saka guiwar hannunsa na dama akan cinyarsa sannan ya buga tagumi ya zuba mata ido cike da shakiyanci.
Da farko banza ta yi masa sai da ta ga ya na neman sawa ta ƙware sabi da kallo ta yi sauron kammala Azkhar ɗin ta yi Addu'a sannan ta kalle shi cike da sababi ta ce "Kai in ba a san asalinka ba sai a ce Mayene Wallah!" ya tintsire da dariya gami da cewa "Hajiya E'iya Matata ta kaina, gani na yi kin yi kyau sosai shi ya sa nake kallonki." "Aff!! Ƙarya ka ke yi, da dai bansan halinka ba sai ka shogama ni." dariya ya yi sannan ya ce "To Ina wuni" ta ce "Da ban wuni ba ai da ba ka ganni ba." ya ce "Daɗina da ke Sababi wallahi, Ina ƴan ƙannen nawa?" ta taɓe baki sannan ta ce "Ƙannenka sun tafi Yawon Ta Zubar" cikin sauri ya ɗora hannunsa akansa gami da cewa "A'uzubillah!!" ya furta ya na dariya, ci gaba ya yi da cewa "Wai ba na ce ki dena cewa Yawon ta zubar ɗin nan ba? kin fa san me ake nufi da hakan" "Na sani sarai kuma ba zan dena faɗe ba, yawo ba dalili ina ya ga amfani? gaskiyar ce ba kwa so kuma sai na faɗa, tsabar iskanci fa Huzaif Baby ya ke kiran kansa." Dr Yarima ya ƙara Kecewa da dariya ya na cewa "Wallahi ba ki da dama Matar nan, shi ya sa fa da tunani ya yi min yawa na gudo wajenku don nasan anan ne zan samu farin ciki, in banda rikicin tsufa don ya cewa kansa Baby ai ba wani abu bane, kema ai Babyn ce." ya ƙarasa maganar cikin sigar zolaya, ta riƙe haɓa da sauri gami da cewa "Ni!!!!? rufa ni ba da ni ake wannan Tumɓelen ba, ba na so, in haifi ubanka ka ce min Baby banda ka raina ni?" Miƙewa ya yi ya na cewa "Ina Budurwata? na lura yau a fusace ki ke ma." ta ce "A'a zauna mana, ko ruwa ban baka ba fa, ka ce ka na neman Budurwa bayan ga mata? zauna maza za ta zo ta sameka ta na Sama ƙila ma kwalliya take maka." ya koma ya zauna tare da cewa "Ai daɗin budurwa kenan in ciki ta ƙi sai a fita waje." ta taɓe baki murya ƙasa-ƙasa ta ce "Ka ji da shi dai." Ɗakko masa ruwan ta yi a gora tare da kofi ta dire masa sannan ta koma ta zauna. shiru ne ya biyu baya kafin ya buɗe baki zaiyi magana Inni ce ta katse shi da cewa "Ah marhaba da zuwanka Saurayina." ya saki murmushi gami da cewa "Yauwa dama ke nake nema, tin da na shigo kin ganta nan banda faɗa ba abin da mu ka yi, kai amma gaskiya kin yi kyau Budurwar Mijin Wata." ya faɗa ya na kallon E'iya taɓe baki ta yi ta kauda kai. shi da Inni su ka sa dariya, Inni ta ƙaraso kusa da shi ta zauna, bayan sun gaisa su ka ci gaba da hira.

Sai misalin ƙarfe 9:53pm ya shiga gida, Mamy ta na zaune a Falo ta na kallo, ya na ganinta ya yi ƙasa da kai ya na shirin zillewa sashinsa, "Yarima!!" ta kira shi ba tare da ta kalle shi ba. tin daga yanayinta ya fahimci a cike take fam, shafar ƙeyarsa ya yi a ransa ya ce "Shi kenan rigima ta tashi." ƙarasawa ya yi, ya gaisheta ta amsa kadaran kadahan sannan ta ci gaba da cewa "Tin Yamma ka ce min za ka ɗan je can kuma ga shi har goma, ina ka je? me ka zauna yi?" "Gidan su E'iya na je." mewtcss!!! Mamy ta ja tsaki kafin ta ce "Wai me ya sa ni ba za ka ji maganata ba sai dai ta ubanka??? ban haneka da zuwa wajensu ba wai??" a rayuwa Yarima ya na bala'in takaicin ƙiyayyar da Mahaifiyarsa ke nunawa Kakarsa ta wajen Uba, ya rasa me ta yi wa Mamyin da ta tsangwameta haka har ta kai ga hana shi zuwa wajensu, "Mamy su ɗin fa Kakannina ne ai ba komai bane don na je na gansu, don Allah ki dena irin haka kema fa uwa ce, yanzu idan Ƴaƴana su ka yi miki haka ai ba za ki ji daɗi ba." Mamy ta saki baki gami da cewa "Auu?? lallai ma, ni ka ke faɗawa haka??" ya ce "Ki yi haƙuri kawai ina takaicin hakan ne." Ta jinjina kai gami da cewa "Danƙari Maƙari" bai bari ta ci gaba da wata maganar ba ya miƙe tare da yi mata sallama ya sanar da ita ba zai ƙara sakkowa ba.
Ko amsawa ba ta yi ba ta bi shi da ido har ya ɓacewa ganinta.

Bayan ya watsa ruwa ya yi shirin Bacci sai kuma tunane-tunane su ka sake yi masa sallama, bai iya rintsawa ba har sai da ya yanke hukunci zai gayawa Aaminat ya na sonta kuma ya tsara zuwa gidansu gobe.

Sai mu ce Asbha ta gari.

(To masu Karatu ya yi Bacci kuma ku kwanta kafin gobe mu garzaya Gidan Alhaji Aminu Mai Kasuwa don jin Halin da Abdulkareem yake ciki😍)

*Ayeesha Abdulkareem INDO* Ta na me farin cikin Sanar da ku cewa An Fara Karanta Littafinta WATA HANYA a Gidan Radio Garanti Mita 94.7 Ku Kasance da Abdullahi Muhammad SALBAS Domin Jiye Kunnuwanku irin Faɗakarwa Da Nishaɗi da ke cikin Wannan Littafi. Kar kuma Manta Sunan Marubuciyar Ayeesha Abdulkareem INDO, Garanti Radio 94.7 Ƙarfe 5:30pm Daidai

Share Fisabilillah

©️©️
INDO tare da SALMA AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)

Littafin Haɗaka ne💪🏾

Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA ONLINE WRITER'S

Tare da

Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S

Shafi 14

Washegari.
Abdulkareem ne kwance kan Gadonsa ya lulluɓe gangar jikinsa da bargo fuskarsa ce kawai a buɗe sai muzurai yake ba alamar walwala a tare da shi.
Tunanin irin Yankan ƙaunar da Aaminat ta ke yi masa yake yi gashi duk yadda ya nemi hanyar da zai dakatar da hakan ya kasa samu, ya rasa ta inda zai bi ya shawo kan matsalar.
Nana Khadija ce ta yi sallama ba tare da ta jira ya amsa ba ta shigo ta zauna a gefen gadon, fuskarta a ɗaure ba alamun wasa, ko kallonsa ba ta yi ba ta ce "Sai wani ɓoye-ɓoye ka ke yiwa mutane, idan ba ka gayawa wani ba a cikinmu ai ka gayawa wani, ko an gaya maka ana iya samun maganin cutar da ba'a santa ba? ni na san akwai wani abu a Zuciyarka amma sai raina mana hankali ka ke yi." "Ke har wani hankalin da za a raina gareki?" ta ce "Ka ga ni fa ba wai na zo mu yi faɗa bane; na zo ne da batun sirri tsakaninmu, banda abinka in ka gaya min ai ka samu abokiyar jaje ko da ba za mu iya yin maganin abin ba. Nazari ya ɗan yi kafin ya ce ''Ba na son gaya muku ne duk ku tayar min da hankali." "Faɗi indai ni ce ba ni da matsala. "Kinsan Aaminat? ta gidan su Waleed.
ta zaro ido gami da cewa "Me ta yi maka?" "Ni ne na yi mata laifin domin kuwa na kamu da sonta, a da kawai tausayinta nake ji amma yanzu abin ya wuce nan, ina son ganin farin cikinta ko ta wane hali, amma ita ta ƙi ƙaunata ƙarshe ma nema take ta ba wani damata ya yi amfani da ita. jikin Nana Khadija ya yi mugun sanyi murya a sanyaye ta ce "Amma Ya Abdulkareem kai ma ka san hakan da kamar wuya ya akai ka bari hakan ta faru?" ya ce "Ni ma ban sani ba, amma kema kin sani ba a yiwa so shamaki, ki bar zancen nan kawai tin da kin ji, ki tayani da Addu'a kawai, tashi ki ban guri yanzu nima zan fito." miƙewa ta yi jiki a sanyaye ta yi hanyar fita, duk hankalinta ya tafi a tunanin ta yaya Abdulkareem zai iya Auren Sa'ar Yayan yayansa? ta yaya ma Iyayensu za su yarda?, da wannan tunanin ta koma Falo ta nemi guri ta zauna sannan ta ci gaba da tufkawa da warwarewa.
Chapter 17 · 0% Book details