← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 38

Sashe 21

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abdulkareem ya ce "Ba haka nake so ba ke ce ba kya iya hana kanki kuka, amma ni kullu yaumin burina naga farin cikinki, sani ne ba ki yi ba amma na fi kowa jin zafin kukan nan naki."
Kasa magana ta yi ta cigaba da rera kukanta, Abdulkareem ya ce "Ki tafi gida, kuma ki kula da gargaÉ—ina."
Dama jiran ƙiris take ya na faɗa zaizai ta wuce hanyar gidansu, Siyama kuwa ya na jiyowa kanta ta yi saurin juyawa za ta koma cikin gida, ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta, juyowa ta yi kanta a ƙasa ta na wasa da ƴan yatsunta jikinta sai tsuma yake.
Ya ɗan matsa gaf da ita ya na binta da zara-zaran idanunsa murya ƙasa-ƙasa ya ce "Siyama ki yi haƙuri ba a son raina na yi hakan ba, ina da zafin rai ne wani lokacin, kuma kin zo min da maganar da hankalina ba zai iya ɗauka ba, ba na jin akwai wanda zai iya sa ta farin ciki bayan ni, ni ne na dace da rayuwarta." ba tare da ta ɗago kai ba ta ce "Haka ne, ni na haƙura, amma ya kamata a ce yanzu Aaminat ta san gaskiya." Abdul ya ce "Na cika da fargabar abin da zai biyo baya shi yasa nake tsoron sanin nata, amma zan yi shawara." gyaɗa kai ta yi alamar eh, bai ƙara cewa komai ba ya juya itama ta shige gida.
Tagumi ta buga ta na tunanin irin shirmen da su ka tafka, Allah i sa komai ya zo da sauƙi shi ne addu'arta a halin yanzu.

Yarima
Cikin shirinsa ya fito Falo ya na tafiya ya na gyara zaman agogon hannunsa, muryar Yayarsa Raheena ce ta sa ya fara slow ya na zazzare ido, idanunsa su ka sauka akanta suna tsaye ita da Ammee su na tattaunawa Khausar Ƴarta ta na gefe ta coge ta na danna waya.
Ƙarasawa ya yi gurin cikin sanyin jiki Zuciyarsa fal mamakin haɗewar da Ammee da Raheena su ka yi lokaci ɗaya saɓanin Da da Raheena ta fita daga sabgar kowa na gidan a cewarta Duk sun fi son shi akanta don haka ta yi fushi ta fitar da kanta daga cikinsu, amma yau sai gasu sun haɗe kai, Addu'a yake Allah i sa ba Kishiyar Ammeen su ke son cutarwa ba.
Lura da zuwansa ne ya sa su ka yi shiru da zancen da suke yi, Ammee ta kalle shi a fizge ta ce "Menene?" ya ce "Zan fita ne, Aunty Raheena yaushe ki ka zo?." a yatsine ta ce "Meye naka a ciki? ai gidan ubana ne ina da ƴancin zuwa a duk lokacin da naga dama." ya ce "Ba ina nufin wani abu bane, Allah i baki haƙuri, kuma dama ba ni na hanaki zuwa ba ke kika sa kanki." Ta buga tsaki kafin ta ce "Allah wadaran ɗan da yake zigawa a yiwa uwarsa Kishiya ni ban taɓa ganin irinka ba; ai ga irinta nan Ammee kun fifita shi a kaina yanzu ga abin da ya jawo miki nan."
Ammee ta rausayar da kai ta taɓe baki gami da cewa "Umm!! kin ga ranar Duniya, amma dai kinsan ni ina sonki ai Mahaifinku ne dama me nuna bambanci wai shi ya fi son Namiji." Yarima ya ce "A'a ba ruwansa fa Ammee wallahi itace kawai ta ɗorawa Zuciyarta haka amma shi dukkanmu ya na sonmu." a hantare Ammi ta ce "Kai dallah gafara shashashan da bai san ina ke masa ciwo ba, kai ai anyi Mahaukaci tinda har ka fifita wata akan Uwarka , ka je ka rungumeta nima ina da tawa ƴar."
Yarima ya kasa cewa komai ya yi gaba zungui-zungui Ammee da Raheena su ka rufa masa baya da harara, Khausar ma ta bi bayansa da kallo kafin ta zabga tsaki.
Raheena ta ce "Ni fa in fayyace miki gaskiyata Ammee na tsani Abubakar tin da ya zo Duniya na dena jin daɗin rayuwa, sai ma da na fita daga cikinku ne na samu nutsuwa, gashi duk wani abu da za ka yi masa don ya ƙuntata ba ya tasiri akansa." Ammee ta rausayar da kai gami da cewa "Uhm!! Allah i kyauta dai, Nima ai yanzu kinga ya yi min sabi da Namiji ɗan kunama ne, shi yasa ake cewa in ka haifi Namiji wata ka haifawa, yanzun haka kwalliyar nan da ya yi ya cokara hula in ba sa'a ba wajen wata zai tafi." Raheena ta yi tsaki gami da keɓe baki, har cikin ranta neman makasar Yarima ta ke yi don a cewarta shine duk wata damuwa ta-ta, ci gaba su ka yi da tattaunawa, sun daɗe a wajen kafin Ammee ta raka Raheena wajen Mota dama fitowa ta yi za ta tafi shine aka tsaya ana ƙara tattaunawa.

Yarima.....
a ƙofar gidansu Aaminat ya tsayar da motarsa, zazzafar iska ya furzar hankalinsa duk ya rarrabu kashi-kashi wani kan Aameenat wani kan Ammee da Raheena har ma da Abi da Matarsa wadda yake kira da Aunty Zainab ko Aunty. waya ya cira ya turawa Aaminat kira kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta ɗauka gami da sallama, ya sauke ƴar ajiyar Zuciya sannan ya ce amsa sallama ya ci gaba da cewa "Na zo fa." da sauri ta ce "Ka zo??" ta yi tambayar ƙirjinta na bugun shalugude...
Ya ce "Kin manta na ce miki zan zo ne?" da sauri ta ce "A'a ban manta ba na zata dai ka fasa,, gani nan zuwa." ta na faɗen haka ta yi ƙitt ta kashe wayar, Yarima ya bi wayar da kallo ya na mamakin abin da ke damunta.
Cikin sauri-sauri ta ɗakko gogaggen Hijab ɗinta a sif ta saka ta fesa turare, ba ta saurari inda kayan kwalliya su ke ba bare ma ta yi tunanin za ta yi, cikin sauri ta fita ta na alla alla ta je ta bashi haƙuri tare da uzurin rashin lafiya don kar Abdulkareem ya ƙyalla ido ya gan shi.
A hanyar soro ta yi katari da Abba ya na ƙoƙarin shigowa, ta raɓe gefe cike da ladabi ta ce "Sannu da shigowa Abba." bai amsa ba sai ma cewa da ya yi "Na samu labarin wani ya na zuwa gurinki, to ki gaya masa wata ɗaya ya rage masa idan Aurenki zai yi ya fito a wata ɗayan nake so in aurar da ke." Zuciyar Aaminat ta bada Durummmmm!!!! Abdulkareem ne ya fata faɗo mata, ba shakka idan Abba ya ce dole a wata ɗaya zai aurar da ita ya jefata a masifa, Abba ne ya katse mata tunanin nata da cewa "Ko ba ki ji ba??" ta ce "To Abba in sha Allah zan faɗa." ya jinjina kai sannan ya wuce ciki, Aaminat ta yi waje cikinta ya na ƙugi da rugugi na tsoro.
Yau ma kamar kullum ya na tsaye a jikin mota ya na jiran fitowarta, kanta a ƙasa ta ƙarasa inda yake tare da yi masa sallama ya amsa ya na murmushin ƙarfin hali. shiru ne ya ɗan biyo baya na wani lokaci kafin ya ce "Mun gaisa da Abba ai." ta yi murmushi gami da cewa "Na ji daɗin hakan." Ya ɗan gyara tsayuwarsa kafin ya ce "Na zo kuma na yi shiru, hankalina ne duk ba a kwance ba, ni ba na son fitina wallahi ko yaya take." da ɗan mamaki ta ce "Fitina kuma?" ya ce "Aff! yi haƙuri don Allah wallahi abin da ya shafi cikin gidanmu ne kinsan mata da kishi kuma Abi ya yi sabon Aure." Aaminat ta rausayar da kai cike da tausayawa ta ce "Allah sarki, am..um... dama ni kam zan ce maka ka yi haƙuri yau ba ni da lafiya ne so na ke na yi sauri naje na kwanta." "Subhanallah! me ke damunki? ai ba kwanciya ya kamata ki yi ba magani ya kamata ki sha. ido ta zaro a ɗan razane, har ga Allah ta manta cewa shi ɗin likita ne take neman jibga masa ƙaryar rashin lafiya, Yarima kuwa ya kafeta da idanunsa da su ka fara kawo ruwa, cikin inda-inda ta ce "Au..ai..am. dama fa ba wata rashin lafiya ce me girma ba da zarar na yi bacci shi kenan, don Allah ka yi min uzuri, amma kafin haka dole ne in isar maka da saƙon Abba, ya ce in gaya maka indai Aurena za ka yi to ka turo manyanka su yi magana." ta ƙarasa maganar kanta a ƙasa cikin ɗan jin kunya.
Yarima ya ja numfashi kafin ya ce "Aaminat! nima ya gaya min haka kuma ya ce nan da wata ɗaya yake so komai ya faru, Aaminat ki yi haƙuri da jin abin da zan gaya miki, ki ɗauka hakan ƙaddararmu ce baki ɗaya." Ɗan numfasawa ya yi sannan ya ci gaba da cewa "Ba ni ne asalin Masoyin naki ba Abdulkareem ne!" rasss gabanta ya faɗi ta yi zaram ta ɗago kai ta zuba masa idanu cike da rashin fahimta, ya gyaɗa mata kai cike da son tabbatar da gaskiyarsa, "Abin da kunnenki ya ji shi na faɗa, Abdulkareem Aminu Mai Kasuwa, yaron da ki ke rainawa ba ki ɗauka a matsayin Namiji na shine ya turo ni gareki, na yanke hukuncin faɗa miki ba tare da ya sani ba domin dole-dole wata rana gaskiyar za ta fito kuma ko ba haka ba ma a yanzu ake buƙatar hakan domin shi Abba mijinki yake nema ba ɗan Aike ba." tasssss!! Aaminat ta wanke shi da mari cikin kuka ta fara magana "Ashe kai mayaudari ne macuci maci amana?! me na yi wa maza ne da suke son tarwatsa rayuwata? shin menene laifina a Duniyar nan da ƙaddarata ta fi ta kowace mace muni? ashe kai ma ba so na kake ba ashe kai ma yaudara ce ta kawo ka gareni!! Kaicona, ni dai ban yi sa'ar zuwa Duniya ba.
Chapter 21 · 0% Book details